Masana ilimin kimiyya a Birtaniya sun kirkiro wata manhajar wayar komai da ruwanka, da za ta kawo gagarumin sauyi a bangaren kula da idanu a kasashe masu tasowa.
Manhajar za ta baiwa ma’aikatan lafiya damar duba wa ko akwai cuta a ido, kuma su yi gwaji da na’ura ‘yar karama mafi araha.
Mutane fiye da miliyan 285 ne a fadin duniya, ke fama da matsalar gani ko kuma makanta.
Ana tunanin cewa za a iya rigakafi ko magance hudu zuwa biyar na matsalolin ido, ta hanyar yin tiyatar yanar ido mai sauki, ko kuma ma amfani da tabarau.
A yanzu haka ana kan gwajin wannan manhaja a kan mutane 5000 a wasu kauyuka na kasar Kenya.
Daga BBC HAUSA