38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

An saki wani Operating System mai suna Anonymous, mai cike da kayan hacking tare da shi.

Abubuwan mamaki ba za su kare ba, matukar mutum yana raye a duniya, a daidai lokacin da kasar Amurka da sauran kasashe suke ta kokarin kafa dokokin da zai hana saka haramtattun abubuwa a kan internet sai ga wani sabon OS wanda shi kanshi ba a san wadanda suka yi shi ba, wanda yake cike da kayan fasakwaurin internet.

Ko da yake kungiyar nan ta () it ace take da alhakin wannan Operating System din, amma da yawa daga cikin su sun ce su basu da hannu wurin sakin wannan OS wanda yake cike da abubuwan da zasu iya kawo hatsari ga tsaron internet.

OS din wanda ya zo a cikin sa programs da dama wadanda suke bayar da damar a iya fasawa ko kuma lalata tsaron internet ya hada da wanda yake hana ka iya aikawa da sako fiye da daya a lokacin (denial-of-service attacks), wanda shi wannan tsari da aka fito da shi shine wanda kake gani idan kana son ka cike wani form a internet sai ka rubuta wasu surkullen kalmomi kafin ya baka damar ka aika da wannan form naka. To, idan ka yi amfani da wannan OS din to zai ratse wannan tsaro kuma zai iya aikawa da sako iya yawan da ake so.

Ba denial-of-service attacks kadai bane ke cikin wannan mugun OS din ba, yana tare da wadansu mugayen program kamar su, simulator Ddosim, da scanner Sql Poison da Password cracker wanda ake kira da John the Ripper.

A wani dandali na Tumblr ya ce an kirkiri wannan OS din domin “ilimantarwa ne kawai” sannan kuma domin “duba tsaro dake cikin web pages”.  Sannan kuma a cikin wannan dandalin sun gargadi masu son yin amfani da wannan anonymous da cewar basu yi wannan OS din domin a kai hari ga wata kafa ba ko kuma wani website, “duk wanda ya yi fasakwaurin wani website, zai kare a kurkuku”.

Ko da yake akwai wani website wanda shi kuma dandalin Hackers ne da kuma a nan ne ake samu labarai da dumi-duminsu akan abinda ya shafi fasakwaurin internet sun gargadi  mutane da su guji amfani da wannan program domin sun ja kunne wajen amfani da wannan OS din suka ce suna ganin wannan OS tarko ne domin suna ganin shi kanshi program din wata hanya ce da zata iya kaika ga kwaso virus da Trojans.

Ko da yake wannan kungiya da ta saki wannan OS din sun ce basu da shugaba lokacin da hukumar nan ta FBI a satin da ya gabata tuhumi wannan kungiya ta LulzSec. Sun ce wannan ba kungiya ba ce, wurin karawa juna sani ne kawai.

 Kadan daga cikin Programs da wannan OS ya zo da shi

ParolaPass Password Generator
– Find Host IP
– Anonymous HOIC
– Ddosim
– Pyloris
– Slowloris
– TorsHammer
– Sqlmap
– Havij
– Sql Poison
– Admin Finder
– John the Ripper
– Hash Identifier
– Tor
– XChat IRC
– Pidgin
– Vidalia
– Polipo
– JonDo
– i2p
– Wireshark
– Zenmap
…and more

3 COMMENTS

  1. Godiya mai yawa da wannan article duk da wasu suna ganin amfani da wannan OS ganganci ne to ni dai zan gwada amma don qarin ilmi kawai. . . Amma inaso ka taimaka ka gaya mana website din da zamu samu wannan OS din ko da trial version ne

    • Shi wannan OS din babu trial version nashi, kuma ba na sayarwa bane kyauta ake bayar da shi, kuma ma ai a cikin article din mun fadi komai da komai game da shi, matakin farko da ya kamata ka sani shi wannan OS din ba kamar windows OS bane LINUX ne, sabo da haka idan ka iya amfani da LINUX ka kuma iya Installing din shi ka shiga google ka searchig Anonymous OS zaka ga website din da fatar ka gamsu.

  2. tamba yana shine akan modem don’t Allah inason karin bayani idan anshiga internet se sikirim din computer yarika nuna damaged rubutun baya fita sosai inason karin bayani admn

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img