Mene ne Animation?
Animation dai hotunane daukakku, tsararru, ko zanannu masu motsi. Wandanda motsin da suke yi ya samo asaline ta hanyar jera su da aka yi daki daki. Bayyanarsu hotunan da kuma motsin da ake gani yana faruwane a sabili da saurin da ake ginin wucewar hotunan ne, wanda yake kayyadajje ta hanyar amfani da computer ko akasin haka.
Karkasuwar Animtion
Animation ya kasu kashi daban daban, wadanda aka dunkule su aka kuma raba su zuwa gida uku kamar haka :
1. Traditional Animation
2. Stop motion Animation
3. Computer Animation
Traditional Animation
Traditional animation , animation ne wanda ake yin shi ba tare da amfani da computer ba, shi ne irin animation na farko da aka fara a duniya.
Traditional animation ana yin shi ne ta hanyar zana hotunan (frames) da ake son motsa su da hannu ba tare da wata na’ura ba, sannan sai a kwafe su ko kuma ayi tracing(sake bin zanen da abun zanen)din su akan wata fellen roba mara kauri mara launi(wato transparent) mai sunaCels sannan a daura su a zanannen hoton bango(background image) mai launi, bayan haka sai a dauko wani irin abun daukan hoto mai suna Rostrum Camera a dauki zanannun hotunnan a rika jera su akan hoton bangonsu mai launi(background image) daya bayan daya. To bayan an wanke hotunan daga abun daukan hoton, sai a jera su akan majigi (projector) a bayyanar da su da sauri, to a nan ne hotunan za su zama masu motsi (Animated movie), fina-finan zane masu motsin (Animated movies) da aka yi amfani da irin wannan tsari sune; The Lion King, Spirited Away, Les Triplettes de Belleville, Snow White da dai sauransu
A karkashin Traditional Animation za a iya karkasashi shima kamar haka:
Full Animation:
A irin wannan salon, ana yin zanen da kuma sa shi motsin yayi kamanni da dabi’un na dan adam na gaskiya, yawancin Animations din Disney ( kamfanin animations ne) suna amfani da irin wannan salon, The Secret of NIMH, The Iron Giant da dai sauransu.anyi anfani da tsane.
Limited Animation:
wannan kashin yafi sauki, domin wajen zanen da kuma hanyar zana shi ba a cika lura da na kwaikwayon don misalan irin wannan kashi sune kamar The Flintstones, Yellow Submarine da dai sauransu.
Rubber Hose:
A irin wannan tsari, akasarin zanen mutumin ko abin da ake a sawa motsi, ana zana su gwai-gwai (cartoony) wato ba kamar mutanen gaskiya ba, a wannan salon mai zane na da ‘yancin yin zanen kowane iri ba tare da la’akari ko yayi kama da abinda yake kwaikwayar zanawa ba, haka ma kuma a wajen sa shi motsi(animating), misalan irin wannan animations din da aka yi amfani da sune sun hada da Mickey Mouse din da aka fara a farko, Ren and Stimpy, Popeye da dai sauransu.
Stop Motion Animation
Stop Animination, Animination ne da ake anfani da abin daukan hoto a rinka daukan shi hotunan daya bayan daya, wanda ta yadda ba za’aiya anfani da hannu ba wajen motsa shi Daga karshe a zo a jerasu a rinka motsa su a jere su zama animation movie , ga kadan kamar haka:
Cutout Animation:
A irin wannan tsarin animator(mai yin animation) ya kan yayyanka zanen da yayi ya dinga motsa su yana daukan hoton su, sannan ya sa musu motsi ta hanyar bayyana su da sauri, misalan animationsdin da aka yi da irin wannan salon sune; Monty Python’s Flying Circus, Tale of Tales da dai sauransu.
Puppet Animation:
A irin wannan animation din animator ya kan yi amfani da abu kamar bebin roba(puppets) wato wanda aka yi mai hannuwa da kai da kafafuwa, da dai sauransu, amma wanda zai iya tsayuwa da kanshi(armature), wato mai waige, ya na motsa shi yana daukan hotonsa, kowane motsi hoto daya, wanda idan aka bayyana shi da Sauri sai ya zama hoto mai motsi(animated movie). Misalan animations din da aka yi da wannan salon sune: The Nightmare Before Christmas, Robot Chicken, The Tale of the Fox, da dai sauransu.
Clay Animation:
A irin wannan salon animator na amfani da yumbu ko wani abu mai kama da yumbun ya gina abinda yake so ya sa wa motsi, ta hanyar yi masa waigi(armature)yana motsa su yana daukan hotonansu kamar yadda animator mai bin salon Puppet Animation yake yi, abinda ya bambanta Clay Animation da Puppet Animation shi ne amfani da yumbu, animations din da aka yi da wannan salon sune; Creature Comforts, Dimensions of Dialogue Na Jan Švankmajer, The Amazing Mr. Bickford, Chicken Run, Wallace & Gromit, da dai sauransu
Computer Animation
Computer Animation, animation ne wanda ake yin shi ta hanyar amfani da computer, a irin wannan Animation din ana zana hotunan da ake so a sawa motsi da tsara su da sanya musu motsi duk ta hanyar amfani da computer, irin wannan animation din da shi aka fi amfani a wannan zamanin da muke ciki yanzu . Computer Animation ya kasu kashi biyu kamar haka:
1. 2D Animation
2. 3D Animation
2D Animation:
A irin wannan animationdin ana amfani da hotuna wadanda suke da kusurwa biyu 2D wajen yin animation, Traditional animation shi ma a wannan yanayin yake, amma shi ba da computer ake yinshi ba, a yau akwai software da dama da ake amfani da su wajen yin 2D animation kamar su; Flash, Corel Rave, Anime Studio, SwishMax da dai sauransu. Misalan fina finan da aka yi da 2D animation sune kamar: SpongeBob SquarePants, Ben10, Naruto da dai sauransu.
3D Animation:
A irin wannan animation din animator yakan yi amfani da hotuna wadanda suke a kusurwa uku 3D wajen hada animation, irin wannan animation din ne idan aka hada sai kaga tamkar ba zane bane, zaka dauka komai gaske ne, shima 3D Animation yana software da yawa da ake amfani wajen yin 3D Animation kamar haka; Maya, 3D max, Anim8or, Poser, iClone, Light Wave, Blender, da dai sauransu. Shima 3D Animation an yi amfani da shi wajen hada fina finan hotuna masu motsi masu yawa ga kadan daga ciki; Shrek, Toy Story, The Incredibles, ice age,Rio da dai sauransu.
Dan Allah munaso idan an koyar da abu wanda yake da bukatar amfani da software to a bamu link din da zamubi muyi Downloading din software din. Kamar dai wannan muna bukatar ta sosai. Mungode
Wannan haka yake ammma kuma yana daga cikin alkawuran da mukayi na cewar ba zamu rika baiwa mutane link na gurbatattun gidajeba domin su rika samun software na bogi, amma idan ba na bogi ake so ba to zamu rika sakawa mun gode.
Gaskiya kuna kokari Allah saka muku da alheri don Allah kuyimin bayani yadda ake afani da photo shop karmar yadda ake chanza fuska dadai sauran su nagode
Allah ya saka
Jazakallahu bi khayr..
Kuna sitar da softwares ne? Kuma aina zamu same ku? Muna godia