38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Computer Software Gamsasshen bayani a kansu

Computer Software, Software ko kuma ka ce Compter Program na nufin abu guda daya, amma abin da suke nufi shi ne, wadansu tarin rubuce-rubuce ne da ake dunkulesu wuri guda da ake son su sarrafa Hardware ko kuma su fadawa computer ga abin da za ta yi.
Kamar misali irin wadannan umarni na computer su ne suke baka damar idan ka danna maBallin da ke jikin keyboard ita na’urar ta fahimce irin maBallin da aka danna, ba domin Software da aka tsara zai rika fassara abin da keyboard ke yi ba da ya zama bashi da amfani. Haka kuma ta fannin program har ila yau, idan ka yi amfani da keyboard ka yi rubutu su wadannan umarni su ne suke da alhakin su ajiye shi cikin memory na computer wani software ya sarrafa shi.
Shi kuma wani software zai dauko wannan data da aka ajiye a cikin memory domin ya mayar da ita ta koma information. Wani umarnin shi kuma yana baka damar yin lissafi ne ka hada wancan data da wancan ya baka amsa. Haka wani umarnin yana baka damar ka fitar da sakamakon aikin ka zuwa takarda ko kuma ka gan shi a jikin monitor. Kusan kamar yadda muka fada babu yadda za’a yi Hardware ya yi aiki ba tare da software da yake sarrafa shi ba. Kafin computer ta yi wani aiki ko kuma ta gabatar da wani umarni shi umarnin dole a ajiye shi a cikin memorin nata. Ko da yake a zahiri wadannan ajiyayyun umarnin suna fitowa ne daga babbar kwakwalwar computer zuwa memori duk sa’adda aka kunna ita wannan na’ura.
Idan ka siya Program na Computer yana iya zuwa ne a cikin CD ko DVD, sai ka saka shi a cikin na’urar ka ajiye shi, domin idan har kana bukatar wannan Software da ka siya ya yi aiki sai ka ajiye shi a cikin na’urar wato (Installation). Shi ya sa wani lokaci ana yin Installing proram kai tsaye a cikin memory daga jikin Floppy ko CD ko DVD ko Flash Drive wanda yin haka ba sai ka sake ajiye shi a cikin Hard Drive ba. Saboda haka software shi ne ginshikin aikin computer, idan kana da ingantaccciyar software, to na’urarka za ta zamar maka babban kayan aiki wanda za ka sami dimbin amfanin ta, kuma ka samu sauki wajen saukaka aikin ka. Saboda haka software ta kasu kashi biyu System Software da Application Software.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img