Tare da fatan alkhairi don Allah ina son ku yi mini karin bayani a kan facebook a inda ake sa address din email da password da neman abokai wai shin wani password ne za a sa na email ne ko na facebook?
To Malam Isa Abba Askira idan na fahimci tambayarka shi ne a wani lokaci idan mutum yana searching na Friends yana haduwa da irin wannan amma hakan ba komai ba ne sai domin tantancewa a kan ko mai amfani da wannan facebook shi ke da account din, ko kuma ba shi ba ne, amma dangane da password da kake gani a lokacin da kake searching friends sai ya ce ka saka email account yana nufi email dinka sannan kuma password na shi wancan email din yake nufi, domin idan ka ba facebook daman shiga email dinka za su duba contact dinka suka ga wasu abokanai kake hulda da su, idan suka same su sai su aika masu da sakon cewar kana da accout na facebook su yi hulda dakai ta facebook. ILLA IYAKA MUNA GODIYA da fatar ka gamsu.