Mafi yawan lokuta idan na zauna ana maganar KASU (Kaduna State University) dangane da yadda ake samun sauƙi wurin shiga wannan jami’ar sunan mutum na farko da yake faɗowa bakin al’umma shi ne Farfesa Ibrahim Malumfashi.
Wannan bawan Allah bai taɓa karɓar takardar ɗalibi da sunan cewar zai nemar mashi admission ya buɗe durowa ya ajiye ba, sannan da yaro zai sami admission sannan a sami matsala ko wurin sakamakon jarabawa ya kasance wurin da aka tura shi babu halin a ɗauke shi, zai iya ƙoƙari wurin ya ga an canza wa wannan ɗalibi inda zai dace da shi. Haka da ta Allah za ta kasance yaron bai sami shiga ba, to zai yi wa yaron alƙawarin cewar idan Allah Ya kai mu shekara mai zuwa, muna nan muna da rai da lafiya ka sake sayen form, kuma ka je ka yi ƙoƙarin sake jarabawa.
Wannan bawan Allah da sauran irinsa waɗanda suke taimaka wa yara wurin samun sauƙin admission da taimaka wa yara wurin ganin sun sami ingantacce ilimi mai kyau, Allah Ya saka musu da alkairi, ya biya musu buƙatunsu, Ya tsare musu iyalansu, ya karesu daga sharrin waɗanda basa son taimakawa.
Ba mu bayar da wannan shaida a gare shi ba, sai dai da abin da ya riske mu na alkairanshi, sannan ba mu da masaniya da abin da yake ɓoye.
Ba mun yi wannan rubutu domin al’umma su je su matsa mishi da maganar admission ba ne, mun yi wannan rubutu domin mu faɗa muku alkairinsa, domin jama’a ku taya shi da addu’ar fatan alkairi.