28.4 C
Nigeria
Monday, April 28, 2025

Fasahar AI: Kafin Musulmi yayi amfani da ita dole yasan wadannan abubuwa guda 7

Rubutawa: Salisu Hassan Webmaster

Gabatarwa
A zamanin da na’urori ke iyan koyon abu da kansu, su yanke shawara ba tare da sa hannun dan adam ba, har ma ya iya kirkirar abu da kansa, Musulmai na fuskantar abubuwa guda biyu: ko dai su rungumi damar da AI ke bayarwa wajen inganta al’umma, ko kuma suna jin tsoro dangane da illolin da wannan fasahar ka iya ruguje ingantattun dabi’u na addini musulunci. Duk da tun fil Azal koyarwar Musulunci tana karfafa neman ilimi (العلم) a kowane fanni muddin wannan ilimin ya dace da manufar shari’ar musulunci. Kamar yadda malaman musulmi na farko suka shiga cikin ilimin Girkawa suka fitar da abinda da ya kai da a wancan lokacin Musulunci da Musulmai suka samar da cigaban da Duniya bata taba riska sai lokacin. Haka ma a yau, al’ummar musulmi za su iya amfani da AI wajen ilimi, lafiya, noma da da’awah – muddin an bi umarnin Ubangiji na tabbatar da adalci, kare mutunci da dogara da Allah. Wannan tafiya tana bukatar cikakken sanayya game da wannan fasahar da kuma dubi zuwa ga abinda ya dace da shari’ar Musulunci cikin Maqasidish Shari’ar (مقاصد الشريعة), domin tabbatar da cewa AI ya kasance hayar da zaya taimaki al’umma ba wai hanyar da zata maye gurbin mahaliccin mu ba.

1. Halal da Haram: Tabbatar da Halaccin AI

Dole musulmai su tabbatar cewa amfani da AI be kaucewa iyakokin da Shari’a ta amince da su ba na halacci (الحلال) ko haramci (الحرام). Mu sani AI yana zama halal idan abinda yake yi ya tsare gaskiya, ya nisanci yaudara ko ha’inci, kuma ana amfani da shi ne a harkar ilimi, kiwon lafiya, da walwalar jama’a – ba tare da taimakawa wajen aikata miyagun ayyuka ba. Idan kuma AI ya taimaka wajen batsa, damfara ko zalunci, to haramun ne.

Misali kamar siyan wuka ne domin aikin yau da kullum, kamar kare kai, amfani a cikin gida don yanke-yanke, kaga musulmi ya halatta ya mallaki wuka kuma ya ajiye ta tare da shi. Amma a lokacin da wuka ta koma don ayi fashi, kisa da barazar rayuwa, to kaga mallakar wukar ta zama haramun. Shi yasa dole duk wani sabon abu da ya shigo dole se an kalli makasudin shi da amfanin shi a shari’ar Musulunci.

Ayyukan hada-hadar kudi ta AI dole ne su nisanci gharar (الغرر) (rashin tabbas mai yawa) da riba (hana karbar kudin ruwa) domin su dace da dokokin Shari’a. — journal.maqasid.org

Malamai na shari’a suna jaddada cewa amfani da AI a fannin sa ido ko kuma bincike kan mutane bai kamata ya keta ka’idojin kare mutane daga cin zarafi ba. — Muslim Ad Network

2. Adalci da Gaskiya: Yiwa kowa da kowa Adalci

Adalci (‘adlالعدل) ginshiki ne a addinin Musulunci. Dole ne a tabbatar da cewar ba a horar da AI akan fasahar nuna wariyar launin fata ba, domin yin hakan zai fada cikin aiki da dokar Allah ta tabbatar da cewar duk bayanan da zai bayar ba zai ci zarafin wani ba ko taba masa mutuncin.

Tsarin (المقاصد) Maqāṣid na Shari’ar Musulunci yana tababbatar da an kare hankalin mutane (ḥifẓ al-‘aql – في العقل ) da kuma kare nasabarsa (ḥifẓ al-nasl في النسل), wanda za a iya lalata wannan nasabar ta hanyar amfani da AI. — SpringerLink

Wani nazarin shari’a ya nuna cewa son rai wajen daukar ma’aikata ko bayar da bashi yana haddasa rashin adalci a al’umma, wanda ke sabawa akidar Musulunci. — SpringerLink

3. Kare Sirri da Mutunci: Karewa kowa Mutuncinsa

Musulunci yana da tsanani wurin karewa mutane mutuncinsu (satr al-‘awraستر العورة) da mutuncinsa (‘العرض). Tara bayanai ba tare da izini ba ko bincike cikin sirrin mutane yana keta wadannan hakkoki masu daraja. Saboda haka, duk wani AI da aka gina fasahar shi, ta hanyar satan bayanai ko ta keta mutuncin da alfarmar bayanan mutane to wannan ya zama kamar fasaha ce mai taba al’aurar mutane.

Al-kur’ani yana kamanta leƙen asiri da babban zunubi; don haka dole ne tsarin AI ya mutunta hakkin samun izini kafin tattara bayanai. — ResearchGate

Bincike daga Saudiyya ya tabbatar da cewa dokar Musulunci tana kallon keta sirrin bayanan mutane a matsayin babban laifi, kuma tana bin tsauraran matakan kare wadannan bayanan da amfani dasu a boye.

4. Amfani wurin yin alheri: Taimakawa maslahah (Alheri Ga Jama’a)

Daga cikin ka’idata ta (مقاصد الشريعة) Maqāṣid al-Shari‘ah tana kawo amfani ne ga jama’a (maslahah مصلحة – ), wanda ke karfafa cewa idan za ayi amfani da AI wajen ragewa mutane wahala da inganta rayuwarsu to wannan bai sabawa shari’a ba.

Misali kamar amfani da AI wajen kiwon lafiya domin samun ingantaccen sakamako, ko fanni noma domin a samu yalwa da gano cututtukan da kuma inganta aiki domin hakan yana nuna kare rayuka ne (ḥifẓ al-nafs حفظ النفس ) da kuma kare dukiya (ḥifẓ al-māl حفظ المال ). — iqra.study

Chatbots masu koyar da karatun Alkur’ani da gyaran Tajwidi suna saukakawa wurin samun ilimin addini ga kowa, wanda hakan kare addini (ḥifẓ al-dīn حفظ الدين ). — ResearchGate

5. Dogaro akan Fasaha: Daidaita Dogaro

Duk da cewa fasahar AI na bayar da manyan damammaki, amma dogaro na hakika (tawakkul التوكل) yana ga Allah shi kadai. Musulmi ya kamata su yi amfani da fasahar AI cikin lura da taka tsantsan, ba tare da watsi da abubuwan da addini suka gindaya ba.

Masu sukar AI suna gargadi ne a kan cewa a nuisance shi, saboda mutane suna dogaro akan fasahar ne (algorithms)  su maye gurbin ikon Allah. Sai dai koda zaka yi amfani da AI to ka dogora ga Allah da kuma fatan ikhlasi.

6. AI Don Da’awah da Koyarwa: Fadada Isar Da Sako

AI na iya karfafa aikin da’awah ta hanyar bayar da fassarar Qur’ani cikin harsuna da yawa, ba tare da wata wahala ko kuma fannonin ilimi na Shari’a. Sai dai yana da kyau a tabbatar da ingancin ilimin da AI zai kawo da kuma cewar kowace Aya ko Hadisi ko maganar magabata daidai ne. Kamar chatbots na neman hadisi yayi maka bayani da fassara da kuma yin ta’aliki akai. Haka ana amfani da wannan fasahar domin koyarwa na musamman.

Manhajojin IQRA suna baiwa wadanda ba larabawa damar fahimtar Alku’ani a cikin yarensu kuma cikin sauki. — iqra.study

Chatbots da aka horar su bisa litattafan hadisi sahihai kamar Ṣaḥīḥ al-Bukhārī da Ṣaḥīḥ Muslim suna bayar da amsoshin tambayoyi kan fiqhunsu cikin aminci. — Umrah International

7. Nauyi  akan masu Kirkira: Shigar da Maqāṣid Cikin Surkullen AI

Masu kirkirar AI suna da alhakin tabbatar da cewa sun hada kai da kwararrun masu kirkira da kuma kwararru a bangaran ilimin Addinin musulunci mai zurfi domin inganta ayyukansu. Hada manufar Maqāṣid a cikin surkullen algorithms na AI na tabbatar da kare addini, rai, hankali, zuriyya da dukiya.

Tsarin fasahar Musulunci na bukatar a ci gaba da yin amfani da tasirin AI tare da shigar da ra’ayoyin masana da jama’a don kauce wa cutarwa (الضرر). — Academia

Hadin gwiwa tsakanin malamai da injiniyoyi yana da matukar muhimmanci wajen tsara ka’idojin AI da suka dace da sharuddan Shari’a. — WIRED

Kammalawa: Ginin AI Mai Cike da Imani da Kyautata Al’umma

Ta hanyar saka ka’idodi da dokokin Musulunci a cikin dukkan matakai na fasahar AI — daga tsarawa zuwa amfani — musulmi za su iya tabbatar da cewa fasaha tana taimakawa ci gaban al’umma da dan Adam. Wannan daidaitaccen tsari yana girmama Maqāṣid al-Shari‘ah, yana bunkasa walwalar jama’a, kuma yana tabbatar dogaro ga Allah. Yayin da AI ke sauya fasalin rayuwarmu, ya kamata mu bar Musulunci ta jagoranci shi: mu tabbatar yana yin adalci, da kare mutunci, da amfanar jama’a domin cin nasara a duniya da lahira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img