A wani sabon yunƙuri da kamfanin google na ƙasar Amurka suka yi na sake fito da wata sabuwar hanyar magance satar wayar-komai-da-ruwanka (smartphone) me ɗauke da manhajar Android shi ne na kara wani sabon kalmar bincike a shafin su na google mai suna Find My Android.
Wannan kalmar ita ce mutum zai yi amfani da ita a lokacin da yake neman wayar sa, ko ta wurin tunanin wani ya da ɗauke ta, ko kuma ta hanyar neman ta domin rashin sanin inda ya saka ta.
Kamfanin wanda suka haɗa wannan tsari da tsarin da suke da shi na Android Device Manager ya na baka damar gano wurin da wannan wayar take, kuma har ya baka damar kiran wayar domin jin ƙarar ta idan mutum yana tunanin cewar wayar tana kusa da shi.
Wani ƙarin abin jin daɗi shi ne, shi wannan tsari zai buɗe maka taswirar wurin da wayar take (Map) ta amfani da google Map, ya nuna maka daidai inda wayar take a yanzu, ko kuma lokaci na ƙarshe da google ya sami labarin inda wayar take.
Abubuwan da mutum yake bukata a wannan tsari shi ne mallakar gmail account, kamar yadda muka yi bayani a cikin muƙalar mu me taken Android – Tambayoyi 7 Da Mai Amfani Da Wayar Android Ya Kamata Ya San Amsarsu a wannan muƙalar mun yi cikakken bayani akan muhimmancin mallakar gmail account ga duk wanda yake riƙe da waya ƙirar Android. Idan kana buƙatar sanin yadda ake buɗe gmail accout za ka iya kallon bidiyon gmail ta wannan hanya Yadda ake bude Imel na Gmail.
YA Find My Android YAKE?
Find My Android ba manhaja ba ce, kamar yadda aka saba a baya cewar manhajojin da suke iya gano waya idan ta ɓace za ka ga manhaja ce. Find My Android tsarin bincike ne da kamfanin google ɗin suka ƙara a cikin surkullen binciken su. Misali idan mutum yana neman abu a intanet zai shiga browser kawai ya buɓe shafin google ya rubuta abin da yake nema, idan sakamako ya fito sai mutum ya zaɓi wanda ya fi dacewa da kai ka buɗe shi.
To shima wannan tsarin neman wayar kusan haka yake, idan kana neman wayarka abin da za ka yi sai ka nemi kwamfuta ko waya mai intanet ka buɗe browser sai ka rubuta www.google.com idan shafin ya buɗe sai ka yi sign in da imel ɗinka na gmail.

[blockquote]Wannan imel da za ka yi amfani da shi ka tabbatar da cewar shi ne wanda kake amfani da shi lokacin da wayar take tare da kai. Da shi kake saukar da manhajoji da suke Google Play Store. Kasancewar duk abin da kake yi da wannan wayar gidan google suna lura da shi.[/blockquote]
Idan shafin ya karɓi abubuwan da ka saka na username da password sai ka dawo ramin da aka ajiye domin yin bincike abubuwa a google sai kawai ka rubuta Find My Android. Wannan shi ne kawai abin da za ka rubuta, da zarar ka gama rubutawa sai ka latsa maɓallin google search daga nan google zai fara bincikar inda ya ga wayar ɗazo ko kuma yanzu.
YA GOOGLE YAKE IYA GANO TA?
Kamfanin google suna amfani da abubuwa guda biyu wanda duk wayar-tafi-da-gidanka tana tare da su, Intanet da GPS. Duk wayar da aka ce Smartphone (wayar-tafi-da-gidanka ) ce to za ka samu tana yin browsing wanda shi ne ma dalilin da ya sa mutane suke son amfani da wayar. Global Positioning System (GPS) wata na’ura ce da ake amfani da ita wurin gano wurin da abu yake ta hanyar amfani da ilimin sanin wuri na Longitute da Latitude. Wannan na’ura ma’aikatu da dama suna amfani da shi, musamman masu fitar da filaye, ko taswirar garuruwa, ko masu neman faɗin wuri kamar masu aiki Ƙasa da Sifiyo da dai makamanta su. To kusan dukkan wayoyin-tafi-da-gidanka suna da wannan na’ura ta GPS a cikinsu, wanda shi ne, mutane ke amfani da shi a Google Map wurin yin tafiya don gano wurin da mutum bai sani ba, ko kuma domin fahimtar adireshin da wani wuri yake.
Tunda wayoyin wannan lokaci suna amfani da Intanet da GPS sai kamfanin google suke yin amfani da wannan dama su gano wurin da wayar take.
ME ZAN IYA YI IDAN NA GA WAYAR TAWA?
Idan aka yi sa’a wanda ya tsinci wayar ya kunna intanet, to da zarar ka neme ta zai nuna maka wurin da take, idan kuwa a daidai lokacin da kake neman ta bata kan intanet to google zai nuna maka wuri na ƙarshe da lokacin da aka shiga intanet da ita.
Abubuwa guda uku zaka iya yi da wayar
- Kiranta: Da farko za ka iya sa google su kira wayar (ringing) wanda idan kana tunanin ba dauke maka ita aka yi ba, ka rasa inda ta shiga ne, kuma baka da wayar da za ka kira amma kuma ga kwamfuta mai intanet a wurin.
- Kulle Ta: za ka iya rufe wayar yadda ba wanda zai iya amfani da ita. A lokacin da kake ƙoƙarin shirya yadda kake son wayar ta rufe, za ka cike wani ɗan ƙaramin fom da google za su baka wanda za ka rubuta kalaman sirri da kake son ayi amfani da su wurin buɓe wayar (password), domin idan an kulle ta kuma aka ganta ba sai kayi amfani da intanet ba wurin buɗe ta ba. Sannan zaka rubuta saƙon da kake son wanda ya buɗe ita wayar ya gani misalin kamar ka rubuta “Wannan wayar an sace ta ne”. Daga ƙarshe sai ka sa lambar wayar wanda kake son a kira idan an tsinci wayar.
Wannan shine abu na biyu da mutum zai yi, yin haka zai kulle wayar duk lokacin da aka buɗe intanet ɗinta. Kuma ko da mutum yayi factory reset, wato ya goge wayar ta dawo kamar ranar da aka siyeta, da zarar ta ji ƙanshin intanet zata sake kulle kanta.
- Goge ta: abu mafi muni da mutum zai yi shi ne ya goge wayar gaba ɗayan ta, ta hanyar lalata dukkan abin abin da ke cikinta. Ba ana maganar contact da saƙonni ba ne, wannan tsarin zai baka damar goge wayarce baki ɗayanta, ta hanyar goge manhajar wayar gaba daya yadda wayar har abada ba zata yi amfani ba.
Wannan shine tsarin da kamfanin google suka bullo da shi domin magance masu satar wayar Android.
Muna godiya duniyar computer, da iron wannan kokari, amman nabi duk tsarin man nayi sing in Google na Sanya find my andrio , so said taba no wani option daban , bazata Nina min map ba . so ya yakamata nayi kenan?
Nagode
ka sake bin ka’idojin da muka lissafa, ya kasance wayar tana amfanida account na gmail da kayi searching da shi.
Allah yabiya dan uwah
dan allah inaso na kulla abuta dakai
09035339932
Ba matsala zan kira In Sha Allah
Allah yasaka nima gatawa lambar dan abota 08066539887
Allah yasaka da alheri gaskia muna matukar karuwa .Wanan shine may Kawnarka daga Ghana Sulley
Madalla Malam Suley da fatan kuna lafiya
Allah ya biyaka da gidan Aljannan firdausi. Kuma in ba takuri g lambata dan samun karuwa dakai kokuma samun sakonni irin wannan ta whasapp, na gode. 07031200424
Enter your comment here…Na godewa Allah! Nidai na gwada yayi, muna godiya DC.
Allah ya saka da alheri Webmaster muna fatan yanzu kun dawo da cigaba da ilmantar damu Allah yayi jagora
Slm mlm salisu wlh muna matukar , alfahari daku Allah yakara basira yadda kuke bamu wannan ilimi kyau ta kuma Allah yabiyamaku bukatunku cikin sauki Ameen mungode ? saikuma alfarma kozan iya tuntubarka dawanne address zanshiga
Wannan tsari yayi kyau sosai, Sai godiya.
Alhamdulilllah Allah yasaka da alkahairil
Mal Salis Allah Ya qara basira, don Allah ga number ta nima a sani a tsari abotan 08062703330
Allah ya biya Web master, da irin wannan kokarin.
Enter your comment here…gaskiya muna godiya muna kuma addu’ar Allah y qara kaifin basira