29.5 C
Nigeria
Sunday, May 4, 2025

Yadda ake amfani da Google Drive

Google Drive wata ma’ajiya ce da kamfanin Google dake kasar Amurka ya kirkira, kuma yake baka ita kyauta domin ajiyar bayanan ka a kwamfutar su wacce take babban dakin adana bayanai nasu da ake kira da Datacenter matukar mutum yana da internet kuma ya mallaki wannan dama da suka bada. Sun baka damar ajiyar abubuwa kamar su takardun documents ko spreadsheet, presentation da hotuna da bidiyo da dai duk wani abu da ake iya amfani da shi a na’ura mai kwakwalwa.

Me yasa ake amfani da Google Drive?

Google Drive a yanzu shine mafi shaharar ma’ajiyar bayanai a sama ko muce girgije wato (CLOUD). Idan baka cikin masu amfani da ma’ajiyar Google Drive, to ina mai shawartar ka da ka kasance daya daga cikin masu ajiyar kayansa online dan samun sauki. Domin kuwa cikin sauki za ka iya sarrafa kayanka daga kowace computer tare da taimakawar internet. Kuma banan ya tsaya ba, yana baka damar rarraba kayanka ga wanda kaso (SHARE) cikin sauki daga kowacce computer da ka tsinci kan ka tare da taimakawar internet.

Kirkiran takardu (file) a ma’ajiyar Google Drive.

Google Drive ba iya ajiyan bayanai ya tsaya ba, yana baka damar kirkiran, rabawa da kuma ajiye muhimman abubuwan takardun kwamfuta, har da wadansu manhajojin aikin yau da kullum da ake amfani da su da ake kira da productivity apps. Kadan daga abubuwan da zaka samu Google Drive sune kamar haka :-

Documents: shi yana baka dama ne ka rubuta labari, wasika da dai sauransu, kamar dai yadda ka san ana amfani da Microsoft Word, kuma kyauta ba tare da siya ko biyan kudi ba.

Spreadsheet: ya na baka dama ne kayi aikin lissafi da fitar da kididdiga da yin bayanai a taswira irin na Chat kamar yadda aka san ana yi a shahararren manhajar nan ta Microsoft Excel. Wani lokaci me abubuwan da ake yi a Spreadsheet na Google ya fi na Microsoft dadi da kuma saukin warware matsaloli.

Presentation: kamar dai yanda kasani (Microsoft powerpoint) shima haka yake aiki. shima yana baka damar shirya takardu domin gabatarwa a dakunan taro, ko takaita kasida da za a gabatar a wurin bita, ko fitar da karamin bayanan darasi da malami zai gabata. Sannan yana taimakwa wurin bayar da shafuka masu launi da rubutu cikin gwaninta kamar Microsoft Powerpoint.

Form: Yana baka damar ka kirkiri takarda da za aturawa mutane su rika cikewa (form), musamman idan ana son a tattara bayanan wani abu, misali kamar za a shirya wani taro da ake bukatar ayi rijista daga ko’ina to mutum zai iya amfani da Google Form ya kirkiri wannan takarda ya tura dmin mutane su iya cikewa.

Drawing: domin kirkiran zanen kwamfuta masu sauki da makamantansu.

YANDA AKE KIRKIRAN ASUSUN GOOGLE (GOOGLE ACCOUNT)

Idan kana son amfani da Google Drive farko kana bukatar Google Account. Google account kirkiranshi kyauta ne sannan dole ana bukatar wasu daga cikin bayanan ka domin baka damar kirkiran asusunka (google account). Bayanan sune Sunanka, shekarar haihuwa da kuma wajan zama.

Da zarar ka bude (google account) to nan take za su baka Gmail wato (Gmail address) wanda shine makullin google drive dinka.

Ga zaka yi amfani da wannan link domin  shiga shafin kamfanin Google  WWW.GOOGLE.COM. Zai bude maka shafi kamar haka  Sai ka danna wannan Alamar (Sign Up) din.

Zai sake bude maka wani Shafin kamar haka

Sai ka danna inda aka sa maka (create account) domin yin register.

Wannan Shafin shine in da zaka saka bayanan ka da lambar sirrinka da kuma yadda Email dinka kake so ya

sai ka danna next domin ya kai ka inda zaka saka lambar wayarka

Zasu tura maka (code) wato wasu lambobi ne ake turawa dan tabbatar da ka saka lambar wayarka dai dai, sannan kuma ba robot bane yake cike musu wannan form din. Sai ka sake yin next.

Bayan ka saka lambar code din da aka tura maka sai ka danna (verify) wato tabbatarwa cewar ka sami sako ta wayarka.

Zai kawo ka Shafin da za ka saka shekarun haihuwarka da kuma zabar jinsinka, shima sai kayi next.

Akwai abunda muke cewa privacy and terms


Wannan wani shafine da yake fitowa mai register, wasu ka’idojin su ne suke gindaya maka wanda dole sai ka yarda dasu ko da kuwa baka karanta baya zame maka wajibi ka nuna amincewar ka da su

Amincewa da sharrudan su shine mataki na karshe wajan kirkiran asusun naka. Wannan shine yadda zaka ga Google Drive naka a kowanne Shafin Google idan ka shiga

Shiga Google Drive dinka

Da zarar ka gama kirkirar asusun google to za ka iya shiga Google Drive ta hanyar rubuta https://drive.google.com ta browser dinka.

Haka kuma zaka iya shiga wannan ma’ajiya idan kana amfani da kowane irin service na google, kamar ka bude gmail dinka ko ka bude sabon shafi a google chrom zaka ga wani hoto daga gefe mai kamar gidan suga kusa da karshe daga sama sai ka taba shi.


Da Zarar ka danna kan hoto na Google Drive din naka zai bude maka kaman haka

Fuskar Google Drive

Google drive dinka zai zama babu komai tunda yanzu ka kirkire shi, amma da zarar ka fara dauara mishi kaya, ko kana kirkirar takardun kwamfuta (files), kana da bukatar sanin yadda za aka rika ganin abu, sarrafa shi, da shirya shi ta hanyar fuskar da kake amfani da ita

Fuskar Google Drive a wayar hannu

Ana samun wannan manhajar a wayoyin iOS da Android idan mutum ya ziyarci shafukan ajiyar manhajojinsu sai ya rubuta Google Drive wanda da zarar ka sauke kuma ka saka email dinka na gmail, zai baka damar ka rika ganin kayanka kuma da iya daura wani kayan ta amfani da wayarka

Google drive mobile interface.

Google naya da manhaja ta musamman wacce da ita ake iya kirkirar takardun google da kuma gyara a cikinsu, kamar documents, da spreadsheets dan presentation.

Fuskar Google Drive a Manhajar Kwamfuta

Idan ka fi son yin amfani da kwamfuta a maimakon manhajar wayar hanu, zaka iya saukar da manhajar kwamfuta ta google drive. Ita ma wannan manhajar ana samun ta manhajar Windows da OS X. Wannan manhajar tana da dan sauki sosai wurin daura kayayyaki da suke cikin na’urarka da internet ko babu internet (offline). Da zarar ka sauke manhajar ka girke ta (install) ka bude ta zaka ka sabuwar folder ta Google Drive a kwamfutarka. Kowane irin file ka tura a cikin wannan folder din shi kuma da zarar yaji internet a jikin kwamfutar take zai daura a cikin Google Drive dinka

wannan shine a takaice bayani game da Google Drive da amfaninsa da kuma yadda mutum zai mallake shi. A fitowa ta gaba In Sha Allah zan yi magana akan yadda ake kirkirar sabon file a google drive, yaya ake amfani da templates, yadda ake daura kaya a google drive da samunsu a sauran na’urorin ka, canza kayayyakin ka su koma tsarin kayan takardun Google.

Jamilu Haladu dalibine a Jami’ar National Open University of Nigeria dake karatun Information Technology, sannan kuma dalibi ne a Makarantar Duniyar Computer zaku iya samunsa a email dinsa kamar haka

2 COMMENTS

  1. Masha Allah gaskiya Mun Karo Da illimin Google drive sosai, Allah ya Saka Da Alkhairi ya Kara Illimi Da basira

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Blockchain a Gwari-Gwari

Wannan wani kirkirarriyar fasaha ce mai wuyar sha’ani da...

Fasahar AI: Kafin Musulmi yayi amfani da ita dole yasan wadannan abubuwa guda 7

Rubutawa: Salisu Hassan Webmaster GabatarwaA zamanin da na’urori ke iyan...

Mene ne Artificial Intelligence (AI) tare misalan rayuwarmu na yau da kullum

Artificial Intelligence ko ka kira shi da AI (fasahar...

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img
Previous article