Kowanne irin mataki ka dauka, lallai ajiya (Backup) ita ce matakin farko.
Kamar yadda muka sani a wannan zamani, muna amfani da na’urar Computer wajen wasu muhimman ayyukanmu na yau da kullum. Misali muna amfani da na’urar wajen rubuta wasikunmu, ajiye hotuna, sunayen ma’aikata, da dai makamantan su. Haka yake! amma matsalar na’ura a kowane lokaci ta iya lalacewa, ko a sanadiyyar wutar lantarki, ko matsaloli na karfe, sai ya zama an yi asarar komai da komai da yake cikin wannan na’ura.
Saboda haka, wajibi ne idan ba kana son ka rasa muhimman ayyukan ka, to kana bukatar ka ajiye ayyukan ka a wani wuri na daban, inda ba computer dinka ba, kamar ka ajiye cikin babbar kwakwalwa na waje (External hard drive) ko CD/DVD da dai makamantan abubuwan da ake iya ajiyar abubuwa.
Iya yawan abubuwan da ka tara a cikin na’urar iya girman abin da kake bukata domin ajiyar ka, saboda haka, idan kana da USB Flash da girman shi ya kai 128MB, to, ka ga abin da za ka iya kwashewa a ciki, ko ka ajiye shi ne kawai documents da irin su hotuna, wasiku da makamantan abubuwan da ba su da nauyi sosai. Amma idan kana da babbar kwakwalwa ta waje (external drive) ka ga za ka iya ajiye dukkan abin da ke cikin na’urarka, tun daga irin su ginin na’urar (Operating System) da hotuna masu motsi (Video) da ma wadansu abubuwan ke cikin na’urar. Domin a kan sami external hard drive mai girman 200GB, wanda kudin shi bai wuce N13,500.00
A wajen wadansu mutane, suna iya ajiye ayyukansu a kowane mako, amma mafi kyau shi ne mutum ya ajiye dukkan abin da ke kan na’urarshi a karshe kowane wata.
SOFTWARE DA SUKE IYA AJIYA (Backup Software)
Idan na’urarka a shirye take, za ka iya samun folders inda kake ajiye muhimman ayyukan da ka yi da kanka – ka duba MY DOCUMENT, sai ka yi coping din kayan zuwa cikin cd ko dvd, ko cikin USB Flash ko kuma External Hard Drive.
Amma ka tuna, ko wanne lokaci kana bukatar ka rinka yin haka duk da yake cewar wannan dama da ka yi amfani da ita ba hanya bace da za ka tattara dukkanin abin da ke cikin abin da ke kan na’urarka, tun daga programs, systems file da settings. Saboda haka, kana bukatar wani software da ke ajiyar abubuwan na’ura mai kwakwalwa (backup software).
A kan samu wasu daga cikin kundin rubutu (cd/dvd writer) sukan zo da software na ajiya. Haka za ka iya amfani da Backup Software irin su Norton Ghost (www.symantec.com) wanda yake daukar hoton dukkan abin da ake cikin na’ura wanda ake kiran shi (Snapshot) domin rubuta ko kwashe dukkan abin da ke cikin na’urarka, kuma wani lokaci ana kiran shi da (disk image). Windows shi ma yakan zo da nashi kayan aiki wajen taimaka maka wajen ajiyar abubuwan da suke cikin na’urarka, wanda ake kira da Backup. Kodayake yana da saukin amfani da wannan software amma fa akwai wadansu abubuwan da masu amfani da ba a samu a Windows. Misali ka ga ba za ka iya ajiya kai tsaye cikin cd ko dvd ba da wannan software.
Sanya Windows Backup Software (Installation)
Idan kana amfani da Windows XP Home Edition, kana bukatar ka sanya Windows Backup Software daga CD.
Kunna na’urarka, latsa Start > All Programs > Accessories > System Tools idan Backup ba a sanya shi a jikin na’urarka ba, sai ka sanya Windows XP CD wanda ya zo da na’urarka. Idan wani shafin barka da zuwa ya fito bayan ka sanya CD, to ka manta da shi. Ka bude My Computer, sai ka latsa hannun mouse na hagu (Right-Click) a kan CD Icon sannan ka zaBi Explore a cikin list daya bayyana. Ka bude Valueadd > msft > ntbackup sannan ka latsa Ntbackup.msi da sauri sau biyu (double-click).
Amfani da Windows Backup Software
Da zarar ka sanya Backup Software, za ka iya amfani da wizard wajan shirya ko ajiye ayyukan ka.
Kunna na’urarka, latsa Start > All Programs > Accessories > System Tools sannan ka zaBi Backup. Backup Wizerd a cigaba da kan shi da wannan wuri. Latsa Next. Ka tabbata Backup Files and Setting ka zabe su sannan ka sake latsa Next. Daga nan sai ka zaBi folder ko files da kake son ka ajiye sannan ka sake latsa Next. Daga nan sai ka latsa Browse sai zaBi idan kake son ka ajiye wadannan abubuwan daka zaba. Bayan ka zaba sai ka latsa Save. Daga nan sai ka latsa Finish domin ya fara wannan ajiya.
Idan kana son ka dawo da abubuwan da ka ajiye (restore) za ka sake bin wancan hanya ta tayar da wizard amma wannan karon ba za ka latsa Backup ba, sai dai ka latsa Restore Files and Settings.
Dawo da Na’urarka zuwa wani lokaci da tayi aiki daidai
Windows yana zuwa da utility da ake kira System Restore. Idan wani tsautsayi ya auku wanda ya janyo har na’urarka ta ki yin aiki kamar yadda tayi dazun, ko jiya. To, System Restore zai dawo da ita baya kamar yadda tayi aiki a jiyan ko wani lokaci da aka yi amfani da ita.
To ga yadda za ka shiryawa na’urarka domin ta kula da lokacin da take cikin koshin lafiya:
Ka latsa yatsan dama na mouse din ka (right-click) a kan My Computer daga cikin list day a fito ka zaBi Properties za ka ga dan karamin window ya bude mai suna System Properties sai zaBi fallen (Tab) System Restore ka tabbatar ka zaBi Monitoring a kan kowa babban kwakwalwa (Hard Disk)
System Restore da kan shi yake shirya lokaci a ko wanne rana domin ajiyar tsari mafi kyau na yadda na’ura ko tafiyar da kanta. Ko da yake duk lokacin da mutum zai sa wani sabon program ko ya cire System Restore kan ajiye abin da na’urar ke da shi a wannan lokaci, saboda haka a lokacin da ka sake kunna na’urarka (restart) sai ka ga bata aiki kamar yadda ka yi amfani da ita dazu ko yanzu ko jiya to za ka iya cewa System Restore ya dawo da na’urar (Restore Point) zuwa shirin jiya ko dazu da dai sauransu. Ga yadda za ka yi domin ka dawo da na’urarka zuwa lokacin da ta yi aiki daidai.
Kunna na’urarka, latsa Start > All Programs > Accessories > System Tools sannan ka zaBi System Restore. Ka tabbata akwai digo (dot) kusa da Restore my computer to an earlier time, sannan ka latsa Next. ZaBi sa’adda kake tunanin ya yi daidai da lokacin da kake bukatar na’urarka ta dako (alamar da za ka gani shi calendar da za ta nuna maka lokutan da na’urarka tayi ajiya), sannan ka latsa Next. Daga nan sai ka cigaba dabin dokoki da na’urar za ka baka, iri su kada ka kashe ta har sai ta kashe kanta da dai makamantan su. Daga karshe na’urar da kanta za ta kashe kanta ta kunna kanta (Restart) idan komai ya yi daidai za ta gaya cewa na’urarka ta dawo daidai zuwa lokacin da ka zada.
SHAWARA:
Idan ka shirya hotunan ka, da wakokin ka, da sauran abubuwan da ke ajiyewa ana’ura to yana da kyau ka ajiye su a My Document Folder, domin yana da wadansu Karin folder da za ka iya rarraba ayyukan ka , kamar My Music Folder domin ajiyar wakoki ko sauti, Video Folder domin ajiyar hoto mai motsi (Video), haka My Picture Folder domin ajiyar hotuna da dai makamantan irin wadannan folder, dukkan su suna karkashin My Document Folder.
Muna godiya mal Allah yakara daukaka