Kowanne irin mataki ka dauka, lallai ajiya (Backup) ita ce matakin farko.
Al-Amin J Hadison
Kamar yadda muka sani a wannan zamani, muna amfani da naurar Computer wajen wasu mahimman ayyukan mu na yau da kullum. Misali muna amfani da na’urar wajen rubuta wasikun mu, ajiye hotuna, sunayen ma’aikata, dadai makamantan su. Haka yake! amma matsalar na’ura a kowane lokaci ta iya lalacewa, ko a sanadiyyar wutan lantarki, ko matsaloli na karfe, sai ya zama anyi asarar komai da komai da yake cikin wannan na’ura.
Saboda haka, wajibine idan ba kana son ka rasa mahimman ayyukan ka, to kana bukatar ka ajiye ayyukan ka a wani wuri na daban, inda ba computer ka ba, kamar ka ajiye cikin babbar kwakwalwa na waje (External hard drive) ko CD/DVD da dai makamantan abubuwan da ake iya ajiyar abubuwa.
Iya yawan abubuwan daka tara a cikin na’urar iya girman abinda kake bukata domin ajiyar ka, sabo da haka, idan kana da USB Flash da girman shi yakai 128MB, to, kaga abinda zaka iya kwashewa a ciki, ko ka ajiye shine kawai documents da irin su hotuna, wasiku da makamantan abubuwan da basu da nauyi sosai. Amma idan kana da babbar kwakwalwa ta waje (external drive) kaga zaka iya ajiye dukkan abinda ke cikin na’urarka, tun daga irin su ginin na’urar (Operating System) da hotuna masu motsi (Video) dama wadansu abubuwan ke cikin na’urar. Domin akan sami external hard drive mai girman 200GB, wanda kudinshi bai wuce N13,500.00
A wajen wadansu mutane, suna iya ajiye ayyukansu a kowane sati, amma mafi kyau shine mutum ya ajiye dukkan abinda ke kan na’urarshi a karshe ko wane wata.
SOFTWARE DA SUKE IYA AJIYA (Backup Software)
Idan na’urarka a shirye take, zaka iya samun folders inda kake ajiye mahimman ayyukan da kayi da kanka – ka duba MY DOCUMENT, sai kayi coping din kayan zuwa cikin cd ko dvd, ko cikin USB Flash ko kuma External Hard Drive.
Amma ka tuna, ko wanne lokaci kana bukatar ka rinka yin haka duk da yake cewar wannan dama da kayi amfani da ita ba hanya bace da zaka tattara dukkanin abinda ke cikin abinda ke kan na’urarka, tun daga programs, systems file da settings. Saboda haka, kana bukatar wani software dake ajiyar abubuwan na’ura mai kwakwalwa (backup software).
Akan samu wasu daga cikin kundin rubutu (cd/dvd writer) sukan zo da software na ajiya. Haka zaka iya amfani da Backup Software irin su Norton Ghost (www.symantec.com) wanda yake daukan hoton dukkan abinda ake cikin na’ura wanda ake kiran shi (Snapshot) domin rubuta ko kwashe dukkan abinda ke cikin na’urarka, kuma wani sa’in ana kiranshi da (disk image). Windows shima yakan zo da nashi kayan aiki wajen taimaka maka wajen ajiyar abubuwan da suke cikin na’urarka, wanda ake kira da Backup. Ko da yake yana da saukin amfani da wannan software amma fa akwai wadansu abubuwan da masu amfani da ba’a samu a Windows. Misali kaga ba za ka iya ajiya kai tsaye cikin cd ko dvd bad a wannan software.
Sanya Windows Backup Software (Installation)
Idan kana amfani da Windows XP Home Edition, kana bukatar ka sanya Windows Backup Software daga CD.
Kunna naurarka, latsa Start > All Programs > Accessories > System Tools idan Backup ba’a sanya shi ajikin na’urarka ba, sai ka sanya Windows XP CD wanda ya zo da na’urarka. Idan wani shafin barka da zuwa ya fito bayan ka sanya CD, to ka manta da shi. Ka bude My Computer, sai ka latsa hannun mouse na hagu (Right-Click) akan CD Icon sannan ka zabi Explore a cikin list daya bayyana. Ka bude Valueadd > msft > ntbackup sannan ka latsa Ntbackup.msi da sauri sau biyu (double-click).
Amfani da Windows Backup Software
Da zarar ka sanya Backup Software, zaka iya amfani da wizard wajan shirya ko ajiye ayyukan ka.
Kunna naurarka, latsa Start > All Programs > Accessories > System Tools sannan ka zabi Backup. Backup Wizerd a cigaba da kanshi da wannan wuri. Latsa Next. Ka tabbata Backup Files and Setting ka zabe su sannan ka sake latsa Next. Daga nan sai ka zabi folder ko files da kake son ka ajiye sannan ka sake latsa Next. Daga nan sai ka latsa Browse sai zabi idan kake son ka ajiye wadannan abubuwan daka zaba. Bayan ka zaba sai ka latsa Save. Daga nan sai ka latsa Finish domin ya fara wannan ajiya.
Idan kana son ka dawo da abubuwan daka ajiye (restore) zaka sake bin wancan hanya ta tayar da wizard amma wannan karon ba zaka latsa Backup ba, sai dai ka latsa Restore Files and Settings.
Dawo da Na’urarka zuwa wani lokaci da tayi aiki daidai
Windows yana zuwa da utility da ake kira System Restore. Idan wani tsautsayi ya auku wanda ya janyo har na’urarka ta ki yin aiki kamar yadda tayi dazun, ko jiya. To, System Restore zai dawo da ita baya kamar yadda tayi aiki a jiyan ko wani lokaci da akayi amfani da ita.
To ga yadda zaka shiryawa na’urarka domin ta kula da lokacin da take cikin koshin lafiya:
Ka latsa yatsan dama na mouse din ka (right-click) akan My Computer daga cikin list day a fito ka zabi Properties zaka ga dan karamin window ya bude mai suna System Properties sai zabi fallen (Tab) System Restore ka tabbatar ka zabi Monitoring akan kowa babban kwakwalwa (Hard Disk)
System Restore dakanshi yake shirya lokaci a ko wanne rana domin ajiyar tsari mafi kyau na yadda na’ura ko tafiyar da kanta. Ko da yake duk lokacin da mutum zai sa wani sabon program ko ya cire System Restore kan ajiye abinda na’urar ke da shi a wannan lokaci, saboda haka alokaci da ka sake kunna na’urarka (restart) sai kaga bata aiki kamar yadda ka yi amfani da ita dazu ko yanzu ko jiya to zaka iya cewa System Restore ya dawo da na’urar (Restore Point) zuwa shirin jiya ko dazu da dai sauransu. Ga yadda zaka yi domin ka dawo da na’urarka zuwa lokacin da ta yi aiki daidai.
Kunna naurarka, latsa Start > All Programs > Accessories > System Tools sannan ka zabi System Restore. Ka tabbata akwai digo (dot) kusa da Restore my computer to an earlier time, sannan ka latsa Next. Zabi sanda kake tunanin yayi daidai da lokacin da kake bukatar na’urarka ta dako (alamar da zaka gani shi calendar da zata nuna maka lokutan da na’urarka tayi ajiya), sannan ka latsa Next. Daga nan sai ka cigaba dabin dokoki da na’urar zaka baka, iri su kada ka kashe ta har sai ta kashe kanta da dai makamantan su. Daga karshe na’urar dakan ta zata kashe kanta ta kunna kanta (Restart) idan komai yayi daidai zata gaya cewa naurarka ta dawo daidai zuwa lokacin da ka zaba.
SHAWARA:
Idan ka shirya hotunan ka, da wakokin ka, da sauran abubuwan da ke ajiyewa a na’ura to yana da kyau ka ajiye su a My Document Folder, domin yanada wadansu Karin folder da zaka iya rarraba ayyukan ka , kamar My Music Folder domin ajiyar wakoki ko sauti, Video Folder domin ajiyar hoto mai motsi (Video), haka My Picture Folder domin ajiyar hotuna da dai makamantan irin wadannan folder, dukkan su suna karkashin My Document Folder.