Keylogger yana daga cikin shahararru kuma matsalar da kuwa yake jin tsoro game da harkar tsaro a kwamfuta. Domin keylogger ba kamar yadda muka sani cewar Virus yana yin ta’adi ba ne, mun san cewar daga cikin tsoron da ake ji da Virus zai iya yi maka a cikin kwamfutarka bai wuce ya lalata maka ayyukanka, ko kuma ya lalata maka hard disk din ka, ko kuma su hana ita kwamfutar ta tashi. Keylogger ya wuce da haka domin shi yana da matukar wuya a iya gano cewar yana ma cikin kwamfutarka ballantana ma a ce har an iya cire shi. Domin kadan daga cikin abin da keylogger yake yi shi ne yana shiga cikin kwamfutar mutum ne domin ya saci muhimman bayanan sirri da mutum yake ajiyewa a cikin kwamfuta. Wadannan bayanai sun hada da password da kuma bayanai na credit card din mutum.
Akwai hanyoyi da dama da mutum zai bi domin ya kare kansa daga fadawa cikin wannan matsalar ta keylogger. Domin wadannan hanyoyi za su taimaka maka ne kawai idan har baka riga ka fada hannunsu ba. Amma kuma hanyoyin da mutum zai fi kiyaye kansa na farko shine ya yi kokari kada ya rika amfani da kowane irin software sai wanda ya saya daga asalin kamfanin software. Duk mutumin da yake shiga internet ya shiga kasuwar bayan fage ya dauko software kamar a torrent da makamantansu, to ya sani zai yi wahala ya iya kare kansa daga keyloggers.
Ga dukkanin wanda yake son ya san wurin da ya kamata mutum ya shiga a internet da wurin da bai kamata ba sai ya karanta mukalarmu ta (Wurare 17 da suka fi ko’ina hatsarin shiga a internet – Mujalla ta farko shafi na 85)
Amfani da Firewall (Wutar Bango)

Sau da dama keylogger yana amfani da internet ne wajen aikawa da bayanan da ya kwaso daga kwamfutar mutum zuwa wurin mutanen da suke yi shi domin su sami damar yadda za su yi maka ta’adi. Wannan kuwa yana nuna maka cewar aikawa da sakon yana faruwa ne kawai ta hanyar internet wanda kenan idan mutum ba shi da internet ko kuma ba ya browsing, to ko da akwai keylogger a cikin kwamfutarsa, to ko da ya kwaso muhimman bayanai babu wata hanya da zai bi ya watsa su.
Amma ga wanda yake amfani da internet a kwamfutarsa abin da ya fi mahimmanci a gare shi shi ne ya yi amfani da firewall software domin lura da abin da yake shigowa da kuma abin da yake fita daga kwamfutarsa ta hanyar internet. Yin amfani da firewall a kwamfuta zai rage maka shiga cikin hatsari matuka saboda shi kamar yadda muka ce duk wani ‘application’ da mutum zai yi amfani da shi wanda shi wannan application yana da bukatar ya sami damar haduwa da internet, to shi wannan firewall software zai taso ya nemi bahasi a wurin ka, shin wannan application da ya taso kai ka ba shi izini ya fitar da sako daga wannan kwamfutar ko kuwa ba kai ba ne? Domin sanin cikakken bayani a kan yaya firewall yake aiki sai a karanta (Firewall Software – Mujalla ta farko shafi na 61).
Yin amfani da firewall ba zai baka cikkakken garanti ba ne, sai dai zai taimaka maka matuka wajen kare ka daga shige da ficen abubuwa daga kwamfutarka zuwa internet.
Daga cikin irin nasarar da ake samu a yaunzu shine yanda kamfanin Microsoft suka kara kaimi wajen lura da firewall da ke cikin OS na Windows 7 da Windows 8, domin kusan duk wani dan lokaci sai ka samu idan kana hade da internet sai ka ji sun aiko da sakon cewar kana bukatar da kayi updating na Windows Defender dinka wanda yin hakan ya nuna cewar kamfanin yanzu sun dau ragamar fada da duk wani abu da zai iya kawo matsala ga kwamfutocin mutum.
Amfani da Password Manager

Password manager wani dan karamin software ne wanda a ke saka shi a cikin kwamfuta domin shi (software) ya haddace dukkan wadansu makullan sirri da kake yin amfani da su kana yin hada-hada a internet. Yin amfani da irin wannan software kan dakushe kaifin barnar da keylogger yake yi tunda shi keylogger bai cika damu da nauyin abun da zai aika ba abinda yake so shine idan yaji an taba matsalli ajikin keyboard shi yake tattarawa ya aika zuwa ga su wadanda suka yi shi.
Shi yasa wanda yake amfani da irin wannan application an password manager yake samun sauki domin dai shi kanshi software din lokacin da ka zo zaka cike wani muhimmin form da ke bukatar ka rubuta sunanka da password dinka, zai ta so da kansa ba tare da kai ka taso shi ba, a lokacin da zai taso ya danganta da wane irin password manager kake amfani da shi, idan mai karfi ne, to zai taso tare da wani mayafin batar da sawu wanda duk wani maballi da aka saka a cikin wancan ramin shima yana sane da shi kuma tunda ya lullube wannan rami zai kasance koda akwai keylogger a cikin kwamfutar sai ya kasa sanin me ke faruwa. Haka wannan software zai kwashe dukkanin wadannan bayanai ya boye su a cikinsa, sannan kuma yayi masu wani kulli irin na goro ta yadda babu wanda zai san abinda ke ciki.
Duk lokacin da ka dawo zaka sake cike wani form mai makon ka rubuta bayananka sai wannan software ya bijiro ya tambaye ka shin wane cikin bayanan sirrin kake son ya zuba maka da ka zabi wanda ake so shi da kansa zai cike maka wannan form din ba tare da ka taba keyboard ko guda ba.
Wani abun jin dadi kusan dukkain browser na zamani akwai wannan software a jikinsu, na san mutane ba su cika lura da wani abu da yake fitowa a lokacin da suka cike form a internet ba. Domin duk lokacin da ka zo za ka yi login ko signin a wani gida daga cikin gidajen internet kamar su facebook, yahoo da dai makamantan gidajen bayan ka gama saka sunan ka da password dinka sai wani dan karamin abu ya fito a saman browser kafin wurin da ake saka adireshi yana tambayarka ya ajiye wannan suna? To idan ka ce mashi e zai dauki wadannan bayanai da ka rubuta ya zuba su a cikin mazubinsa wanda yake da kariya yadda idan nan gaba ka zaka sake shiga gidan ko kuma wani gida sai ya ji ka fara rubuta suna sai kawai ya karasa maka. To, yin haka da kuma samun wannan application a jikin kowace irin browser ta zamani ya kara sa an samu saukin irin wadannan ta’adin na keylogger.
Haka kuma wadansu kwamfutoci su kan zo da shi tare da su wanda yake lura da dukkan wani rubutu ko wani form da mutum ya ke cikewa a internet. Haka manyan kamfanonin anti-virus kamar kamfanin Symantec wanda su suke yin Norton Anti-Virus da kuma kamfanin Kerspasky wanda su suke yin Kerspasky Anti-Virus suna bayar da kariya ta musamman ga wadannan program wanda suke da wani tsari da cakudawa da kuma lalatawa da kuma dabaibayi ga dukkan wani form da mutum zai cika wanda ko da wani ya iya daukar wadannan bayanai babu yadda zai yi masa amfani tunda an cukurkuda shi.
Kodawane lokaci Software dinka su kasance ana updating dinsu.

Wata hanya da miyagun masu kirkiran keylogger su ke bi shine ta hanyar amfani da rubabbun software ko kuma ta hanyar gani cewar software kaza masu shi (wanda suka yi shi) sun bar wata kafa da za a iya shiga. To a lokacin da suka gano haka zasu yi iya kokarinsu su yi amfani da wannan kafa ta hanyar shigar da wannan dan karamin software da kuma su yi amfani da wannan rami wajen aiko musu da sako.
Daya daga cikin software da suke yin amfani da shi kusan kowane lokaci shine Flash Player. Flash Player shima dan karamin application wanda ake daurashi a kan browser wanda yake baka damar sauraron sauti ko kuma kallan video a internet, shi yasa kake ganin kowane lokaci ake gaya maka cewar akwai update na shi wannan application. To, duk lokacin da mutum ya ga wannan bayani na cewar akwai update to yana da kyau mutum ya tsaya yayi domin yin wannan updating kan taimaka wajen rufe dukkanin wani rami da aka manta da shi a lokacin da ake tsara shi wannan software.
Haka ita kanta Kwamfutarka ta na bukatar kodawane lokacin ka rika yi mata updating domin su kansu wadanda suka yi Operating System suna kokarin kodawane lokaci su kulle kafofin da suka manta lokacin kirkiran manhajojin. Kuma zamu iya cewar ana ta samun Karin kariya. Domin a lokacin da kamfanin Microsoft ya fara lura sosai da sashin kula da virus an sami ci gaba sosai saboda a halin da ake ciki duk mutumun da yake da Windows 7 ko Windows 8 kuma yana updating dinshi kodawane lokaci to akwai tabbacin cewar babu virus din da zai kamashi.
To bama Operating System ba, hatta sauran software da suke cikin kwamfutarka kamar su coreldraw da sauran application wadanda kake yin amfani su, domin haka zai taimakawa ita kwamfutar wajen yin sauri da kuma kariya daga shiga hannun masu keylogger.
Chanza Password dinka kowane lokaci

Sama da duk wadancan abubuwan da muka lissafa shi ne, lura da password kodawane lokaci, domin duk yadda ka kai da yin kokarin ka wajen kiyayewa wadancan abubuwa guda uku da muka lissafa a baya, to zaka samu wani abun yakan fi karfin mutum saboda sai ka samu an saci muhimman bayanai da ke cikin kwamfutarsa.
Saboda haka, yana daga cikin hanya mafi inganci shine kodawane lokacin mutum ya rika kokarin canza password din kwamfutarshi da kuma na email dinshi. Domin yin haka zai baka damar rage karfin keyloggers.
Daga karshe muna son mutane su sani cewar idan kai a kan hanya kake to wani a kan hanyar ya kwana, ba munce mutum idan yabi wannan hanyoyin zai tsare kansa dari bisa dari bane amma muna son mutane su fahimci cewar idan mutum ya kiyaye wadannan hanyoyi zai magance irin wannan matsala.