23.5 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a Kaduna in da muka tattauna game da hanyoyin da ake bi domin a cuci mutane a wannan kafa ta intanet.

A cikin shirin wanda Malam Zakariya Aliyu yake gabatarwa mai taken DUNIYAR MU A YAU shirin ya samu damar gayyato Salisu Hassan Webmaster (Shugaban Duniyar Computer) tare da Malam Bashir Aliyu wanda yake lura da bangaren ICT na gidan Rediyon Freedom Kaduna.

Shirin wanda ya kwashe kimanin mintuna 45 mun yi bayani ne game da hanyoyin da bata gari suke bi domin su damfari jama’a da kuma hanyoyin da mutane zasu bi domin ku kare kansu.

Wannan shiri za ku iya suke shi ku saurari ta wannan link dake kasa

http://duniyarcomputer.com/wp-content/uploads/2019/09/freedomradio_internet.mp3

8 COMMENTS

  1. Assalamu alaikum warahmatulllah wabara katuhu malam Allah yakara basira da ilmi, ina da tambaya akan bayanin da kukai na https da kuma https, shin duk website kinda babu “s” kinnan hakan yana nufin anyi shine dan kwashe bayanan mutane? Sannan ana iya samun shafi wanda batada wannan manufan amma bata amfani da https? Allah yakara ilmi Amiiiiiinnn

    • Tambaya mai Ma’ana..

      Ni ma zan so naji amsar da Malam Zai baki.

      Allah yasa idan yaga wannan sharhin (Comment) naki ya yi Reply akai.

    • Malam Maina ba abin da ake nufi ba ke nan! Idan ka shiga website din da zaka yi sayayya sai kaga a jikin website address din ya fara da https to ana fada maka cewar duk abinda ka rubuta na katin wayar ka ko kuma form din da ka cika, babu wani da zai iya tare wannan sakon a hanyar internet ya san me ka rubuta. Zai je a jagwalgwalo ne yadda koda masu website din suka shiga cikin database dinsu suma jagwalgwalo kawai zasu gani ba zasu ga zahirin abinda ka rubuta ba.

      Ana iya samun shafi a internet da basu da https kuma ba ‘yan dandatsa bane, hasali ma su suka fi yawa gaskiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img