32.4 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

HANYOYIN DAMFARA 13 MASU WAHALAR GANEWA

Hakika a wannan lokaci da muke ciki yana da matukar wahala mutum yace bai san abin da ake cewar damfara da dabarun da ‘yan damfara ke amfani da shi fa domin karbar kudi ko jefa mutum cikin tarko ba.

Babu kuma shakka shigowar wayoyin hannu da wadatuwarsu a hannayen jama’a da imani da mutane ke yi da kowane irin sako da kuma son mallakar abin duniya cikin ruwan sanyi ya sanya mutane da dama fadawa hunnun ‘yan damfara wanda a Turance ake kira da yan 419, wasu kuma rashin sani da tsautsayi ke jefa su.

Wannnan rubutu ne da ya kunshi hanyoyin da ake amfani da su domin ayi wa mutane damfara kuma duk daya daga cikin da zaka gani idan kaji ya samu wani naka ko kai karankanka to ka sani cewar damfara ce.

1.   Bayar da bayanai na Bankin ka

Mutane da dama sun sami kansu cikin rigima da bankunan su bayan da wani zai kira su a waya yace musu daga bankinsu yake yana son su bayar da BVN dinsu domin akwai matsala a da accout. Ko kuma suce ya bayar labokin ATM dinsa ko PIN domin yi masa wani gyara.

Hakika babu wani banki a Najeriya ko a duniya da yake bukatar wani bayani da zai karbe shi kai tsaye daga wayarka, kowane lokaci bankuna suna bayar da sanarwar cewar ba sa neman bayanai masu muhimmanci ga abokanan huldarsu ta wayoyin salularsu, ko sakon karta kwana SMS ko ta akwatunan Email.

Saboda haka duk lokacin da wani ya kiraka yayi ikirarin cewar daga bankinka yake kuma ya tambaye ka bayani game da lambar sirrinka, ko wasu lambobi da suke jikin katin ATM dinka ko BVN dinka to ka sani ‘yan damfara ne.

2.   Mutuwa da Taimako

Wannan itama wata hanya ce da ake bi domin ayiwa mutum damfara da sunan aiko maka da sakon Email ko kuma kiranka kai tsaye daga wata kasa ana fada maka cewar wani bawan Allah ya rasu bashi da magaji kuma yana da dukiya mai yawa amma kai ake son a dankawa wannan dukiyar ta hanyar amfani da bayanan ka cewar wannan mutumin yabar wasiyar cewar a kai dukiyar Afirka.

Saboda haka za a iya yin amfani da muryar mace ko kuma wani namiji da sunan shi ma’aikacin banki ne, kuma shine managan wannan mamaci, saboda haka daga karshe zasu yaudare ka ne, kuma amshi yan kudadenka ta hanyar cewa ka aiko musu da ‘yan kudade domin kokarin gyara hanyoyin da wannan kudi zasu taho. Suma ‘yan damfara ne.

3.   Supply na kayan NEPA

Haka nan kawai zaka ji mutum ya kiraka a waya ya fadi sunan ka wani lokaci ma kawai ka ji yana lissafo abokanka ko danginka a karshe yace maka ai shine wane da yake aiki a NEPA, akwai wani supply da aka bashi yayi na wadansu kayan wuta, ana bukatar kamar waya mota biyu ko trailer daya shine yake son ka taimake shi ka kawo.

Ba wannan bane matsalar zai iya fada maka sunan wani abu da yake da wahalar nema, yace a gari kaza kawai ake iya samu, kamar idan yasan kai a Kaduna kake yace abin ana samunsa a Lagos ne, idan kana son zai hada ka da wani, zai turo kama lambar wani yace ka neme shi.

A karshe dai, wannan mutumin na biyu shi kuma zai fada maka cewar suna da shaguna dankare da wannan kaya, sai su fada maka farashi mai sauki wanda idan ka buga lissafi zaka ga zaka samu miliyoyin kudi a matsayin riba, daga nan kai kuma sai ka kira wanda ya fara kiranka kace an samu, sai yace tsaya yayi magana da oganshi yace an samu.

Bayan wani lokaci zai sake kiranka a waya yace maka oga yace a kawo samfiri kamar guda biyar, amma shi (abokin naka) bashi da kudi a tare da shi, sai ya fada maka ka nemi kudi ka biya wancan gayen ya aiko maka da guda biyar. Idan har Allah ya rubuta maka asara sai kawai mutum ya aika da kudin da zimmar cewa wannan mutum zai aiko dashi.

To a zahiri, dukkansu bakinsu daya, kuma babu wani aiki ko kwamgila da aka basu, wannan kudin samfuri shine kudin da suke cutar mutane da shi.

4.   Aljanu masu taimako

Wannan wata hanya ce da ‘yan damfara suke amfani da ita a wannan lokaci domin cutar mutane da sunan taimako. Yadda suke yin abun wani gardi ne zai kiraka da sunan cewar yana son ka yiwa Annabi Muhammad SAW Salati, ka karanta Fatiha da wata ayoyi sai yace kadan matsa gefe guda.

Idan ka fada wannan tarkon zai fada maka shi ba mutum bane, shi Aljani ne, zai ya beka ya nuna maka ka taba taimakonsa, ko mahaifiyarsa ko babansa shine suke son su saka maka da dukiya mai yawa.

Saboda haka zai fara fada maka kayi kaza, ka sayi kaza, a karshe yace wasu irin kudi kake bukata a taimaka maka da su, misali idan kace Dalar Amurka kake so sai suce to kaje ka same su ka zuba su a cikin abu irin kaza ka kai wuri kaza, dai dai lokaci zasu mayar maka da wannan kudi miliyoyi. Wani lokaci kuma zaka ji sun ce su Aljanune daga Makka, suna son taimakonka, ka fara siyan kati ka tura musu.

Koma dai mene, Aljanu basa magana da mutane ta waya, kuma basa bukatar layin sadarwa domin su yi magana da mutum, hasalima ba dai ba a ganin Aljanu kuma ba yin magana da su. Duk wanda kaji yace maka shi Aljani ne, ko wani mutum yace maka yana magana da Aljanu koda da sunan Rukya ne to dan damfara ne, ku kiyaye su.

5.   Lambar Waya ta Shan Jini

Wannan kuma ba damfara ba ce hanya ce da ake bi domin a tsoratar da al’umma a sa musu shakku da yin hulda da mutane, musamman mata da kana nan yara. Shi yadda abin yake zaka ga wani akwo ne a Facebook ko WhatsApp cewar ga wata lambar waya kada ka kira ko amfani da ita domin duk wanda ya kira ko aka kirashi da ita ya dauka to zai mutu.

Wannan karya ce tsagwaronta, ku sani Allah bai mallakawa dan Adam wani abu na sarrafata ba, babu kuma wani da zai iya amfani da na’ura don tsabagen iya sihiri don ya cutar da mutum sai dai yayi amfani da wani kara ko sauti domin razana ka.

6.   Kwangilar Customes

Wannan kuma yafi yafuwa a sahar Facebook, zaka wani yace cewar shine shugaban masu dillancin kayan da kwastam suka kwace da aka shigo da su ta hanyar da bata dace ba, saboda haka gwamnati tana yin gwanjonsu, sai su lissafo kayayyaki kuma su saka adireshin intanet da zaka bi.

To suma irin wadannan mutane nen ‘yan damfara ne sosai, kuma sun dade suna cutan mutane kuma hukumar kwastum ta dade da fitar da sanarwa cewar bata da alaka da irin wadannan mutanen saboda haka ayi hattara.

7.   Bude account da sunan mace

Akwai akwatunan Facebook da Whatsapp a ake budewa da suna da hotun mace kuma a saka wannan hotun mai kyau da daukar hankali da kuma aiko maka da cewar ana son yin abota da kai. Daga bayan zaku fara yin masayar magana ta hanyar yin Chating har ku fara amincewa da juna, ta aiko maka da hotunanta tana kara jan ra’ayinka daga nan ta fara neman wasu kudade da niyar cewar zata kawo maka ziyar har gida.

To mafi yawancin irin wannan accout wani sangamin katon namiji kake hulda da shi, wani lokaci idan ka matsa cewar sai kaji murya sai a nemi wata matar a bata wayar ku yi magana, to itama wannan hanyar ta ‘yan damfara ne.

8.   Hacking Accunt a Nemi temako

Wannan kuma account din mutum ake shiga sai a bude wurin sakonsa, a fara magana da abokansa a mastsayin shi ke yi, a fada maka cewar ya samu matsala ne a wurin kaza kuma yana bukatar taimakon katin waya ko a aiko da N1000 da zimmar yana shigowa gari zai mayar maka da shi.

To suma wannan hanyar damfara ce, abu na farko da zaka fara magance wannan matsalar shine kace ya kiraka a wayarka da kuma saba magana zaka ga daga wannan lokacin bai sake neman ka ba. Kai kuma taimakon da zaka yi sai ka fadawa wannan abokin naka cewa ana neman kudi da account dinshi.

9.   Sakon Facebook na albishir

Akwai sakon da ke shigowa ta Facebook da sunan cewar ka ci wata kyauta, amma ka bayar da wadansu kudade domin a aiko maka da wannan kyauta, ita damfara ce.

10.  Sakon WhasApp na ‘yan ISIS ko shan jini

Wannan ita ce hanyar tsoratar da jama’a ce da za aiko da wata tamba ta sahar WhatsApp da sunan cewar duk mutumin da ya shiga wannan group din to ya sani na kungiyar ISIS ne ko na yan shan jini, to shima wannan hanya ce ta tsoratar da mutane, kuma mafi yawa ‘yan damfara ne ke shirya wannan makircin.

11.  Kawo Kudi na ninka maka

Wannan hanyar damfara ce da ta shahara a intanet da zahiri, wannan wankiya ce tsagwaronta da ake amfani da dabarar bude wani kamfani da zai fada maka cewar yana yin harkar Danyan Mai da Gwal saboda haka idan ka saka dubu daya sati mai zawa zasu ninka maka ya koma dubu biyu ko fiye da haka.

Ko kuma idan a intanet ne sai ace maka akwai wani tsarin neman kudi da ake kira da suna forex trading wanda a zahiri da gaske a kwaishi, amma kuma cutarka za ayi da kuma yaudarar ka.

Duk wanda ka ji ya ce maka kawo kudi in maka kudi ko in kara maka bayan sati daya, ba kuma banki bane, ko gwamnati ta fitar da irin wannan tsarin ba, to yaudara ce da cin kudin mutane da zalunci.

12.  Zaka mutu idan ka fadawa wani

Wannan ita yaudarar da damfarar anfi yin ta ne a zahiri kuma tafi shafar mata, zasu shiga mota su hadu da wani sai akai mutum wani unguwa ace za a kashe shi idan ya bayar da labarin abin ke faruwa, sai a saka shi ya rika kawo kudi kodawane lokaci, idan bashi da kudi kuma a saka shi a rika ciwo bashi.

Ana iya fahimtar haka idan kuka yar ku bata da aiki yi sai kuka kodawane lokaci ko yawan yin shiru, da amsa waya ba a cikin mutane ba, da yawan neman cikin bashi. Idan har kun ga haka, to ku taimaka ta hadu da yan damfara na zahiri.

13.  Bayar da aron waya ga wanda baka sani ba.

Wannan kuma ba yaudara bace amma mun saka ta a ciki ne domin hatsarinta. Kada ka hadu da mutum a kan hanya kaga yana cikin wani yanayi na neman taimakon waya zai kira ka bashi ya kira.

Domin yin haka zai iya jefaka cikin musiba da bala’i. Wannan matsalar ta faru ne a gari a Najeriya idan wani yana tsaye a gefen hanya wani mutum yace ya bashi aron wayarsa ya kira, bayan da ya kira sai ga Tasi ta zo ta dauke shi, ashe barayin mota ne, suka je suka kashe direban suka kuma tafi da mutar.

Sai aka duba waye ya kira motar aka ga wannan lambar wannan mutumin, haka aka zo aka kama wannan mutumin aka yanke masa hukuncin kisa.  

Wadannan sune kadan daga cikin hanyoyin da ake bi ake yiwa mutane damfara a wannan zamani. Da fatan wannan bayani ya fa’idantar da ku. Allah kuma ya kara tsare mu daga dukkan sharri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img