38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

KUSAKURAI GOMA DA MASU KOYON KWAMFUTA

Ga jerin gwanon kusakurai goma da masu koyon kwamfuta sukeyi da kuma yadda za’a gujewa afkawa irin waɗannan kusakurai.

  1. RASHIN ADANA AYYUKA MASU MAHIMMANCI

Babban kuskuren da ake samu shine rashin adana ayyuka masu mahimmanci. Ayanzu, akwai hanyoyin daban-daban da za’a iya adana muhimman ayyuka da babu wani dalili da zai hanaka adana ayyukan ka kafin ka rasa su.

  • Yadda ake adana manhaja a kwamfuta
  1. DANNA CIGABA (Next) KO EH (Ok) BA TAREDA KARANTA ƘA’IDOJINTA BA

Sabo da amfanida yanargizo ke sa mutane rashin haƙuri wajen karanta ƙa’idoji kafin danna cigaba (next) ko eh (ok) amma, mafiyawancin masu koyo suna danna cigaba (next) ko eh (ok) ba tare da karanta ƙa’idojin yarda da kuma tabbatar da sun cike akwatin (check box). Ka tabbatar ka karanta ƙa’idojin  kafin ka yarda don gudu shigar da abubuwa marasa amfani.

  1. RASHIN AJIYE AIKI

A lokacin da kake aikinka a yanargizo ko kai tsaye, ka tabbatar kana ajiye aikin (saving) a duk bayan minti goma zuwa sha biyar saboda za’a iya rasa aikin sanadiyyar samun ɗauke war wuta ko yankewar yanargizo ko maƙalewar manhajar, duk abinda kayi ya zama babu.

  1. KASHE KWAMFUTA TA HANYAR DA BAI DACE BA

Ba kowa bane ya iya kashe kwamfuta ta hanyar da ta dace ba, saboda sabo da amfani da smart phones da tablets kafin fara amfani da kwamfuta, ita kwamfuta  Idan  zaka kashe ta, kana buƙatar ka ajiye ayyukanka (save), ka rufe manhajojin da suke abuɗe sa’annan ka kashe ta yadda ya dace.

  1. BUƊE SAƘONIN IMEL

Hattara da saƙon imel ɗin da kake kokwanto domin mafi yawancin mugayen mutane suna amfani da wannan hanyar ne dan cutar da kwamfutocin mu ta hanyar  saƙonnin da kake karɓa daga yan’uwa ko abokanai da kuma sauran mutane.

  1. KIYAYE FAƊAWA CIKIN WAƊANNAN MATSALOLIN: PHISING, SPAM DA KUMA CHAIN MAIL

PHISHING

Ka kassance masani akan yadda masu kai ma kwamfutar ka hari ta hanyar dabarar  binciko bayanai a yanargizo, don kada ka kasance daga cikin waɗanda hatsarin ya afkawa.

SPAM

Mafi yawancin spam na samuwa ne daga mugayen mutanae ko kwamfutoci masu illa, idan kaga irin waɗannan saƙon goge su sune mafita sabo da idan aka maida masu saƙon shi ke sa mugayen susan lalai akwai me wanna addreshin kuma su cigaba da turo da wasu saƙonnin ko su raba addreshin ma sauran mugayen.

CHAIN MAIL

Domin kiya ye kanka da kuma ‘yan uwan ka daga samun wata matsala a cikin saƙonsu, sai ka kiyaye haɗa kan ka da wasu chain mail. Idan kuma ka samu wata chian mail kuma ka na tsoro, to ka tabbatar da shi kafin ka turawa ɗan uwanka.

  1. SAUKARWA DA SHIGAR DA GURƁATATTUN MANHAJOJI A KWAMFUTA

A yanzu, mafi yawancin abunda ke ɓata kwamfutocin mu shi ne saukar mata da manhaja mara inganci. Muna saukar da manhaja ba tare da mun tabattar da ingancin ta ba ko kuma manhaja ta kyauta da ake bayarwa. Mu kula da wannan domin wasu suna zuwa da virus wato abin da zai lalata maka kwamfutar ka don haka mu kula wajen saukarwa da shigar da manhaja akan kwamfutan mu.

Domin saukar da manhaja kana buƙatar waɗannan ƙa’idojin :

WAJEN SAUKARWA

Mu kiyaye! Wajen saukar da manhaja domin mugayen mutane suna saukar da manhaja ingantatu su mai da shi gurbatacen manhaja su ajiyeshi da sunan shi domin su gurbata maka kwamfuta.

MANHAJAR SAUKARWA

A kiyaye wurin saukar da manhaja ta hanyar amfani da wata manhajar saukarwa da mafi yawancin kamfanoni ka bayarwa, domin mafi yawa yana zuwa tare da matsaloli da zai iya cutar da kwamfuta.

GUJEWA SAUKAR DA TALLACE TALLACEA A SHAFIKAN

A kula da yawanci  tallace tallace da ake sanyawa a shafinkan download wasu ana sawa ne don jawo hankalin  mutane domin su samu saukin samun manhaja. Su kuma suna amfanin da hanyar ne wurin samun kuɗi ko kuma goya virus don su illata kwamfutocin mutane.

GUJEWA SHAFUKAN DA SUKE SAUKA KAI TSAYE

Kada ka yarda da wasu abubuwa da suke sauka a kwamfutar ka kai tsaye ba tare da sanin kaba, wanda yawancin shafuka suke buƙata ka sabunta ko ka saukar, wanda idan babu waɗannan shafin ba zai buɗe ba.

  1. RASHIN SABUNTA (CANZA) MANHAJA DA OPERATING SYSTEM (OS) NA ZAMANI

A ko da yaushe ana samun sababbin manhajoji da operating system, sabunta su na hana samun matsalolin domin suna zuwa tare da tsaro, a duk lokacin da sabon manhaja ta fito ana samun masu duba kuskuren su. Sabuntawa zai sanya ayyuka su zama cikin tsaro.

  1. AJIYE KWAMFUTA CIKIN TSARO

A yayin da ka jona kwamfutar ka a jikin soket, laptop-smartphone da tablet kana buƙatar tsarin kare kwamfutar ka daga samun matsala ta hanyar amfani da surge, yana taimakawa wajen kare kwamfutar ka akan matsala ta wuta don kada ta samu matsala.

Awurin amfani da desktop ana amfani da UPS akan kwamfutar ka, shi wannan UPS ɗin yana hana ɗaukewar komfuta a yayin samun daukewar wuta na tsawon minti daya zuwa biyu.

  1. SIYAN KAYAYYAKIN KWAMFUTA WANDA BA NATA BA

Mafi yawancin kwanfutocin mu suna amfani da hardwares ko kuma pheripherals wanda zai ɗauki irin wannan device ɗin, misali kamar kwamfuter apple bata daukar kowace irin hard ware wanda ba nata ba ko kuma V.S PC kwamfuta da PC kwanfuta da take amfani da linux ko windows (os) wanda ko wannensu yana amfani da hardware ɗin shi ne.

A yayin siyan hardware ko haɓɓaka shi ka tabbatar komai ya zama na wannaan kwamfutar domin cika duk wani ƙaidojin da ake buƙata na operating system.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img