A wani sabon gwaji da aka gabatar a garin tallin an samu nasarar aikawa da saƙon data mai nauyin Gigabait 1 a cikin daƙiƙa guda. Wannan wata sabuwar hanya ce da ake ganin zata kawo gagarumin nasara a fagen aikawa da saƙwonni masu nauyi da girma nan ba da jimawa ba ta hanyar amfani da tsarin Wireless.
Wi-Fi wacce ita ce hanyar da ake amfani da ita a wannan lokaci wacce ake ganin tana da matuƙar sauri wurin aikawa da saƙon data, a sabuwar hanya da ake da ita wacce take tafiya ta 5GHz ana iya aikawa da data mai nauyi Megabait 600 a cikin daƙiƙa guda. Wannan sabon tsari na Li-Fi ana sa ran zai iya aikawa da data wacce takai nauyi Gigabait 224 a cikin daƙiƙa guda.
Yanayin yadda ake sa ran aiki da haske wurin aikawa da data ta fasahar Li-Fi
Li-Fi wanda za ka iya kira cewar ƙwan lantarki ne irin wanda muke amfani da shi a gidajenmu, ko kuma irin wanda ake samun ƙananan ƙwai na tocilar zamani mai ƙananan fararan ƙwayaye sai dai shi an ɗan ƙara mishi wani sinadari da kuma saka mishi wayoyi waɗanda za ayi amfani da su wurin aikawa da data. Haka shi wannan Li-Fi yana buƙatar wata na’ura ta musamman wacce zata riƙa fassara saƙon da wannan ƙwan zai riƙa aikowa kasancewar shi wannan ƙwai zai riƙa yin amfani da tsarin Binary ne kai tsaye shi kuma wannan na’urar ta na fassara shi zuwa data da mutum zai yi amfani da shi wurin buɗe intanet.

Wannan ba ƙaramin nasara ba ce idan aka yi la’akari da hasashe da ake da shi idan shekarar 2019 ta zo ana sa ran a kowane wata za a riƙa yin amfani da kimanin Gigabait Billion 37 na data, wanda hakan yana nuna buƙatar wannan fasahar kasancewar Wi-Fi ba zai iya bayar da wannan ba.
Wi-Fi wanda ya ke amfani da tsarin aikawa da saƙo ta hanyar Radio Frequency yana da iyaka da kuma wadansu matsaloli wanda ya dangance shi, da wannan dalili ne ya sanya ake tunanin cewar a watan wata rana za a wayi gari ba za a iya amfani da Wi-Fi ba.
Matsalar Wi-Fi ba a nan ta tsaya ba, domin idan mutum na tunanin aikawa da saƙo ta hanyar Wi-Fi ita wannan hanyar tana samun wahalar kafar da za ta bi domin ta kai saƙon da ake turawa. Wannan ba ana magana da irin saƙon da mutum zai amfani da wayarsa ko kwamfuta da kwamfuta ya aika ba. A nan ana maganar aikawa da saƙo na Wireless da ake amfani da shi domin samarwa da mutane Intanet a wurare mai faɗi.
Shi wannan saƙo da ake amfani da wireless a aika shi, yana fama da matsalolin na bango ko ƙofofi da suke iya kare mishi hanyar da zai yi amfani da ita wurin kaiwa zuwa ga na’urar da aka aike shi. Idan kuwa aka zo ga maganar aikawa da baban data to Wi-Fi sai a hankali.
Li-Fi wanda ake kiranshi da Light Fidelity shi kuwa yana ɓangaren fasahar Electromagnetic Spectrum wanda ake amfani da Radio Waves, sai dai shi Li-Fi yana amfani da fasahar tafiyar haske ne fiye da radio wave sau 10,000.

Wannan ya ke nuna cewar Li-Fi yana iya amfani da hanya mara iyaka wurin aikawa da sakonni. maimakon a ce zai yi amfani da hanya guda kamar Wi-Fi wurin aikawa da saƙo, wannan fasahar tana amfani da siririyar hanya wacce ta fi na Wi-Fi sirantaka, sannan kuma za ta kuma raba kanta har sama da gida dubunnai domin isar da wannan saƙo.
Haka ita wannan fasahar ta Li-Fi za ta yi amfani da tsari ne na LED Light wato ƙwan lantarki da muke amfani da shi domin haskaka ɗakunan mu. Domin ƙwan lantarki idan ka kunna shi kana ganin haske ne, amma a zahiri wutar ba ta tsayawa, tana kashe kanta ta kunna kanta cikin sauri ta yadda ido baya iya ganin mutuwar wannan wutar.
Wannan fasahar dai ta fara bayyana ne ta hannun wani Farfesa dan asalin ƙasar Jamus mai suna Harald Haas, Malami a Jami’ar Edinburgh da ke ƙasar Amura wanda ya bayyana yadda ita wannan sabuwar fasahar za ta riƙa yin aiki. Tun a cikin shekara 2011 ya gabatar da gwaji na farko a wani babban taro da aka yi domin nuna bunƙasar fasaha a kowane ɓangare a duniya TED.

Haas ya ce abin da ake buƙata ɗan kaɗan ne domin ganin samun sauƙin aikawa da data. Domin ya ce ya lura da amfani da Radio Mars da sama da miliyan 10 da ake da su a ƙasar Amurka da kuma amfani da ƙananan wayoyin hannu fiye da biliyan 8. Sannna kuma ya ga yadda ko da wane lokaci bunƙasar fasaha da kimiyar Ƙera-Ƙere kullum Ƙara gaba ta ke yi, ya sanya ya yi tunanin yadda zai mayar da hasken wutar lantarki zuwa wata hanya da za ayi amfani da ita wurin aikawa da saƙon data.
Ya ce mutane suna buƙatar wannan dan ƙwai wanda za a iya ƙara sinadaran sa a cikin ƙwan lantarki da muke amfani da shi yau da kullum sannan kai kuma ka sani yar karamar na’ura wacce take iya fahimtar saƙon da wannan haske ya ke aikawa domin kai kuma ka yi amfani da shi a matsayin data na shiga intanet.
Yanzu dai haka tuni an fara ƙera su irin waɗannan ƙwayaye domin ci gaba da gwajin da ake yi na ganin tabbatuwar wannan fasaha. Sai dai Farfesa Haas ya ce wannan fasahar ko kaɗan ba tana neman kashewa Wi-Fi ka suwa ba ne. In da masana suke ganin idan har wannan fasahar ta tabbata to babu wani abu da za a yi da Wi-Fi.