Rubutawa: Aminu Salisu Husaini
Mafi yawan mutane da suke amfani da kayan wutar lantarki irin na kwamfuta da waya suna kara fahimta da jin dadin yadda ake yin mu’amala da su, ga sabo da kwarewa cikin amfani da su wanda ya kai a yanzu zaka samu mutum yana iya ajiyar muhimman bayanai da suka shafe shi ko suka shafi kasuwancinsa a cikin wadannan na’urori. Wannan ya kai ga mutum zai iya amfani da katin cire kudi ATM a cikin kwamfutarsa ya yi siyayya a intanet ba tare da yaje bankinsa ba. Haka mutum zai iya amfani da kananan manhajojin waya ya turawa wani kudi ba tare da ya je jikin ATM ba.
Kullum ana samun hanyoyi masu kawo sauki a cikin ayyukan mu na yau da kullum, a gefe guda kuma ana samun mutane mara tsoron Allah suna kokarin ganin sun saci muhimman bayanai da muke ajiyarsu a cikin na’urorinmu.
A wannan darasi da zamu yi zamu fada muku abubuwa guda goma na garkuwa da ya kamata duk wanda yake mu’amala da waya ko computer ya san su kuma ya iya amfani da su.
1 Social Engineering Attacks

Social Inginering Attacks wannan a turance ana magana da hayar da gwanayen fashi da makami da ‘yan dandatsa a kwamfuta suke amfani da shi wurin satar muhimman bayanai a cikin kayan na’ura. Suna amfani da dabaru sosai wurin wufintar da jama’a domin su cuce su, ta hanyar amfani da wasikun bogi ko su yi sojan gona na wani kamfani ko mutane domin a yarda da su.
Saboda haka mu yi takatsantsan da duk wani link da muka yi shakkarsa, ko sakon imel da bamu san waye ya aiko mana ba, ko kuma amsa wayar da za ace ana bukatar taimako ko kuma za a taimake ka. Kodayake yana da kayau ka sani mafi yawan irin wannan cuta ana yin amfani da bayanai na wanda ya sanka ne. Irin hanya da ake amfani da ita ta social engineering attacks ko gwanaye suna iya fadawa sai mu kiyaye.
2 Kulle Waya Da Sabbin Hanyoyi

Saka harufa guda hudu da ake yi a jikin wadansu wayoyi musamman wayoyin iPhones hanya ce mai kyau amma kuma mu sani ana iya amfani da sa a a hada irin wadannan lambobi bayan an sace maka waya a iya bude ta shi yasa yake da kyau mutum ya saka garkuwa ta musamman da amfani da wadansu harrufa da lambobi da alama wurin kulle wayarsa, yadda zai yi wahala wani ya koda dauke ta yayi ya iya bude wayar. Tsare waya ta hanyar sa mata makulli mai kyau na daga cikin kariya a wannan lokaci.
3 Ajiyar Muhimman Bayanai (Back Up)

Kamar yadda da yawa suka sani cewar kwamfuta bata da tabbas shi yasa ake baiwa duk mai amfani da ita shawara ya yi kokari a kalla yana da wani wurin da yake kwashe kayan da yake da su masu muhimmanci yana jiyesu a wani wuri na daban wanda zai iya kasancewa koda wani lokaci kwamfutar ta bace ba zai yi a sarar aikinsa ba.
Duk da cewar akwai manhajoji masu yawa wadanda ake daurasu a cikin kwamfuta ko waya domin su taimaka maka wurin yin wannan ajiyar, yana da kyau ka sani cewar zaka iya samun CD ko DVD ka rika tara irin wadannan muhimman ayyukan ka a ciki.
Kuma a wannan lokacin ai akwai irin su Google Drive da irinsu Microsoft One Drive da ake iya ajiyar irin wannan ayyukan koda wata rana, ranar ta bace.
4 Saka Ingantattun manhajojin kariya daga cutar kwamfuta

Virus da Malware kodawane lokaci abin tsoro ne, domin da su ake yin amfani wurin satar bayanai a kwamfuta ko kuma lalata manhajoji ko ayyuka ko ma a lalata ita kanta kwamfutar. Shi yasa yana da kyau mu rika yin amfani da antivirus mai kyau da inganci, domin wadansu antivirus software din su ma kansu virus ne, wadansu kuma su suke kiran virus wadansu kuma su aikin da suke yi shi ne yi wa mutum karyar cewa akwai virus a kwamfutar sa. Shi yasa yake da kyau mutum ya rika tambayar hakakin masana game da wani irin anti virus ya kamata in saka a cikin kwamfutata domin wani lokaci mutane sun fi yarda da maganar gamagarin mutane maimaikon masa a kan fanni.
5 Kulle Wireless Router ko Hotspot

Makami na farko da mutane za su iya amfani da shi domin su cutar da kai shine ta yin amfani da budadden hanyar intanet dinka, a da sai mai kudi sosai ya ke iya siyan services na intanet ya sake shi a cikin gidansa domin iyalansa su yi amfani da shi. Amma a wannan lokacin kusan duk wanda yake da wayar komai da ruwanki wato Smart Phone yasa akwai tsarin da ake amfani da shi domin a saki intanet duk mai wireless ya iyin yin browsing kyauta, wanda ake kira da Hotspot.
A nan abin da muke son jama’a su lura da shi shine su sani cewar idan ka sani wannan Hotspot ba tare da ka saka mishi mukulli ba wani zai iya zuwa ya yi amfani da shi ba tare da saninka ba, abin Allah Ya kiyaye da zai amfani da shi ya yi wani aikin da bai kamata ba, to hukuma idan ta yi binciken IP address waye aka yi amfani da shi za su san naka ne kuma ba yadda za kayi ka kare kanka, shi yasa ake sa password domin duk wanda zai yi amfani da shi sai ka sanshi.
6 Ba a aikawa da sako mai tsanin sirri a imel sai ta jagwalgwalliyar hanya

Muhimman bayanai kamar bayanai na bankinka, wata lambar ajiyar kudinka ko lambar biyan kudin harajinka ko kuma wani sirrin kasuwancin ka kada ka taba aikawa da shi ta imel sai ka tabbatar da imel dinka yana amfani da jagwalgwalalliyar hanya (Encrypted). Zaka iya yin amfani da manhaja ko tsarin aikawa da jagwalgwallen imel da irin su ProntoMail ko PGP da dai makamantansu.
Yin haka yana taimakawa wurin datse wata hanyar da idan wani ya samu damar shiga akwatin imel din wanda ka aikawa da sako ba zai iya sanin me aka aiko ba, haka wadanda suke fashin hanyar imel koda sun sami irin wannan sakon naka ba za su iya amfana da komai ba.
7. Kada ka yi amfani da Wi-fi don kowa da kowa sai tare da VPN

Amfani da intanet na kyauta irin filin jingin sama ko makaranta da dai makamantan wurin da ake bayar da kyatar intanet na Wi-Fi bai cika zama da hatsari ba ko da yake yana da kyan ka kare kanka daga irin gurbatattun mutane ba sai daga baya ba a zo a ce maka kayi hakuri. Amfani Virtual Private Network ko VPN yana sa ka zama mai amfani da intanet a matsayin wanda ba a sanshi ba, domin yin amfani da Public Wi-Fi wadansu bayanai naka ka iya zuwa hannun wani wanda baka sani shi ba. Misali kana amfani da irin wannan tsarin a wani wurin da kowa ya amninta da kowa inda ka ba sauran abokan huldar ka daman amfani da folder ta Domcument dinka da Music dinka to idan ka shigo irin wannan wuri suma irin wadannan za su sami irin wannan dama. Sai a kiyaye.
8 Amfanin da Manhajar Lura da Password (Password Manager)

Akwai hatsari sosai a wurin yin amfani da password irin daya ga dukkan gidaje ko shafuka da ka ke shiga a intanet. Misali facebook da gmail da yahoo da Instagram duk password iri daya ne. Idan kuwa ka yarda da cewar akwai hatsari domin idan aka gano shi wannan password dinka duk sauran dakunan ka za a iya shige su to kana bukatar ka yi amfani da mabanbantan password a kowane shafi.
To yin haka kuma kaima yana da matsala a wurinka saboda sha’anin mantuwa, shi yasa kake da bukatar manhaja da ake kiranta da Password Manager wanda yaka da alhakin lura da duk gidan da ka shiga kuma ka saka username da password shi zai haddace su, koda bayan ka fita daga cikinsu idan ka dawo daga baya zaka sake shiga cikin wannan shafin shi zai zuba maka username din da password din da kanshi.
Amma kuma a nan zamu sake baka wata shawara, ka sani wani littafi da kasan ba zai kai hannun kowa ba ka rika rubuta username da password din kowane website da kake mu’amala da su domin koda za a samu bacin rana.
9 Amfani da Two-Factor Authentication

Amfani da wannan tsari da ba username da password kadai mutum zai yi amfani da shi ya bude shafinsa ba, ko kuma yin wani cinikakkya online zai da karin amsa wata tambaya ko kuma saka wadansu bayanai na sirri.
A yanzu da yake kullum kara samun hanyoyin tsaro to yana da kyau mutum ya yi amfani da wannan tsarin musamman idan kana amfani da shafukan da suke baka da ma ka yi amfani da wannan tsarin na Two-Factor.
Wanda koda ace wayarka ce ta bace ko wani ya sata amma kuma yana tsammanin ya san password dinka idan kana amfani da tsarin 2FA to ba zai iya shiga cikin wayar ba. Irin wannan tsarin duk wanda yake amfani da online banking ko irin su remita zai baka labari.
10 Duba doka amfani da Manhajojin Waya da Security Settings kodawane lokaci

Yana da kyau duk mai amfani da na’uara ya sani kodawane lokaci kamfanin da suke kirkiran manhajoji suna sabunta dokokin amfani da su zuwa wanda zai yi musu dadi da kuma kara musu tsaro.
Shi yasa yake da kyau mu rika shiga cikin shafukan da suke tara bayanai na dokokin aiki da su domin mu sansu kuma mu san mene ne suka canza ko suka kara domin kada su rika daukar bayanan mu suna aikawa da shi hukumomin tsaro alhali sun ce zasu rika yin haka mu ba mu sani ba.
Haka wurin da ake seta manhajoji ko shafuka yana da kyau shima mu rika ziyartar shi domin shima akan samu sauye-sauye da kare-kare da ya kamata mu sani domi sake tsare na’urorinmu.
Misali irin su facebook, twitter da google kodawane lokaci suna kokarin kara kawo sababin matakan tsaro amma kuma suna ba mutum zabi ne, to kaga idan ba muna karantasu ba ne ko kuma ziyartar irin wannan shafuka ba babu yadda za ayi mu sani.
Da fatan wadannan abubuwa guda 10 da na lissafo zasu taimaka mana wurin kara tsare na’uronmu. Kada a manta da liking page dinmu na facebook da twitter da instagram da youtube domin ci gaba da kawo muku abubuwa masu muhimmanci.