32.4 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Matsalar Password na Waya

Assalamu alaikum duniyar computer naji dadin bayanin viros din waya da kuka yi, domin na karu kwarai da gaske domin ina da wani viros a waya ta wanda ina tsammanin shi ya hana memory na karbar kome juma wani lokaci yana shafe min ajiyayyun shafuka a opera, amma gaskiya abin da yake wahalar da ni idan na shiga shafi sai ace na shigar da password , kuma ba mamaki tsarin da kai bayani wato kanfanin waya ta shima idan na shiga hakane, to idan hakane wace lanba ko wani password ne kuma guda nawa zan shigar idan waya ta nokia 6300 cd da fatan kun gane tanbaya ta. Ku huta lafiya

Ina son ka sani cewa kamar yadda baka iya shigowa Facebook sai kayi login, kuma baka samu damar yin login sai da kayi registration da su Facebook,sai ka saka email din ka da password suka yi comferming dinka, to duk wani shafi da zaka shiga a internet idan har zasu baka wata kulawa ta musamman kana bukatar kayi register dasu, idan suka amince da rigistar da kayi, sai ka rinka sa username da password, kada ka manta kowane allazi da nashi amanu, ko wane gida ka shiga suna da tsarin rigistarsu da kuma tsarin yadda suke karbar mutane da fatan ka gamsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img