32.4 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Matsalolin da Kwamfuta take haifarwa Ido: Hanyoyi Goma domin Magance Su

Karuwan mutane da ke amfani da kwamfuta yasa ana kokawa kan yawan samun zafi ko raɗaɗin da nauyin idanuwa. Bincike ya nuna cewa yawn samun ciwon idanu ko alamun hakan yakan faruwa a cikin kashi hamsin (50%) zuwa casa’in (90%) cikin ɗari na mutane masu amfani da kwamfuta musamman a wajen aiki.

Wannan matsalan kan auku ne saboda yawaita samun gajiyawar idanu a sanadiyar lura ga hasken kwanfuta.

Ga wasu hanyouyi guda goma (10) da ka iya rage ko sauƙaƙa wannan  matsalar

1 Samu dubawar idanun ka daga kwararru

Samun dubawar idanu akai-akai yana da matuakr muhimmanci domin kaucewa ko magance matsalolin gani a sanadiyar amfani da ita kwamfutar.

2 Takaita hasken kwamfutar ka

Zugin ido yana aukuwa idan hasken rana da ke shigowa ta tagan ka ko hasken lantarki mai tsanani yayi yawaita. Rage hasken ko ka daidai ta shi kamar  yadda yawancin hasken ofishi yake, yin hakan yana taimakawa sosai. Ka rage hasken ta saukar da labulen gogin ka sannan ka da kasa kwaya-kwayan lantarki da yawa ta yadda haske zai yawaita. Ka na iya amfani da marasa haske sosai. Sannan idan zai yiwu ya zamo cewan tibin kwamfutar ka (monitor) ya zama tagarka na ta gefe ne maimakon ta gaba ko bayan monitor.

Saboda  da yawa daga cikin masu amfani da kwamfuta sukan faɗi cewar sun samu sauƙin raɗaɗi ga idanuwan su idan suka bi wannan tsarin.

3 Takaita ƙura idanun ka

Kura idanu ga duk wani abu mai kyalli kai da ma hasken kwanfuta kanta na iy haifar da zafi ko raƙaƙin idanu. Ka kwatanta amfani da irin gilashi nan da ake amfani a wajen rage hasken kwamfuta (screen guard) ko kuma ya kasance fentin bangon ɗakin ka ko ofis ya zama mara kaske sosai. Hakan zai taimaka maka sosai.

4 Chanza talbijin ɗin kwanfutar ka (monitor)

Idan baka taɓa canza talabijin ɗin wamfutar ka ba (monitor) daga tsohon yayi  (CRT) wanda ke taimakawa wajen samun ciwon idanu to ka gaggauta yin hakan. Domin irin wanda ake amfani da shi yanzu ba shi da hasken da ka iya jawo maka ciwon ko zafin idanu.

Idan kuma babu hali ya zama dole ka yi amfani da irin wannan na farkon (CRT) to ka rage ƙarfin haskensa. Ka duba hasken ta cikin control panel idan karfin hasken na ƙasa da mizanin 70Hertz (Hz) to ka canza shi zuwa sama har ƙarshen sa.

5 Daidaita saitin hasken kwamfutan ka

daidaita hasken talbijin ɗin kwamfutan ka (monitor) zai taimaka maka sosai wajen rage nauyi  ko raɗaɗi da zugin idanu. Atakaice seta hasken yana da muhimmanci sosai kamar haka:

  1. Hasken kwalba (monitor);- rage shi zuwa hasken sa ya daidaita da hasken ɗakin ko ofishin da kake aiki.
  2. Girman harufa:- ka rage ko kara girman haruffan dai-dai da idanun ka yadda zaka samu sauƙin ganinsu (wato yadda ka ji ya yi ma)
  • Kaifin kala (colour):- fitowar kala (spectrum of visible light) yana da nashi illar ga idanun ka. Idan baka daidaita shi ba musamman shudi (blue) wanda ya ke da gajeren zango (short wavelenth) zai cutar da ganin ka.

TSAURIN RUBUTU KO KALAN NA’URAR KA

Domin kauce wa illar cutar da idanu haruffan rubutun ka ya kamata su zama girman su kamar linki uku mafi karancin ganin ka na haruffan da kake iya gani.

Misali danna “ Ctrl +” zai dinga ƙara girman fuskan monitor ne kawai. Sannan kuma ‘Ctrl+0’ zai daidaita shi sannan ‘Ctrl+ – “ rage girman.

Idan kuma rubutu kawai kake so ka rage ko ka ƙara sai kai amfani da “Alt+V’ sannan “Z” da “T”. sai kuma kayi amfani da “+” zaka ga rubut ne kwai ke canza wa.

6 Yawaita Kiftawar idanu

Kiftawar idanu na da muhimmanci wajen kiyaye fama da matsalar idanu a sanadiyar amfani da kwamfuta. Ido na samun danshi a yayin da ka kifta saboda bushe wa da ya ke yi idan ka kura ma abu ɗaya idanu.

Da yawa daga cikin mutane za kaga idan suna aiki da iwmfuta basa kiftawa kamar yadda bincikei ya nuna.

Danshin kwalla da ke samu wa idan ka rufe kwayar idanu ta hanayr kiftawa ya kan sa idanu su samu sauƙin raɗaɗi.

7 Ka rinƙa yi wa idanuwan ka atisayi

Babban abu da ke haifar da zugi a idanu shi ne gajiya. Domin rage gajiyan idanu saboda ƙuri na dogon lokaci da ka ke yi, ka rinƙa kautar da idanun ka duk bayan mintuna ashirin. Sannan ka yi atisayi kamar haka, kalli abun da ke nesa kamar akalla kafa ashirin (20 feet) na tsawon kamar daƙiƙa ashirin (20s). Likitocin ido na kiran  wannan tsarin da suna “20-20-20 rule” .

Wata atisayien kuma shi ne ka kalli nesa kamar na dakika goma ko sha biyar (10 – 15 seconds) sai kuma ka ɗaga idanun ka sama sai ƙasa kamar adadin shima (10 -15 seconds).

8 Rinƙa samun hutu

Domin samun sauƙi daga kamuwa da ciwon idanu, wuya da baya wanda yawan zama ke akan kwamfuta ke haifar wa, ka rinƙa samun hutu (break) akai-akai.

Mafi yawancin masu aiki da kwamfuta ba sa samun isasshen hutu da ya dace da su ta inda hakan ke haifar da cutarwa gare su. Kamar yadda bincike ya nuna. Wasu suna ganin cewa idan suka tsaya hutu kamar aiki zai wuce su. Idan ka hutu bawai a na nufin ka zauna dirshan bane, a na so ka tashi kaɗan yi ɗan tattaki, miƙa, da miƙar da hannuwan ka, ƙafa, wuya da kafaɗun ka domin ka rage gajiya.

9 Kyautata wajen aikin ka

yin irin zaman da bai dace ba kamar durƙushe da tanƙware wa na cutar da jikin ka da idanu wankan. Ka dai dai ta akwatin talabijin ɗinka (monitor) ta yadda ba sai ka durƙusa ba. Ka kuma zaunar da shi kamar inchi ashirin zuwa ashirin da huɗu nesa da kai (20-24 inches) a kan teburin ka.

10 Ka na iya amfani da tabaran idanu

Gaskiya ne idan ka yi amfani da tabaran ido zai taimaka maka sosai. Amma fa ka yi amfani da wanda malaman lafiyar ido su ka tantance ko zaɓa maka.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img