A gaskiya Malam Abbas Babayo Gombi akwai banbanci mai yawa da ke tsakanin Windows Xp da kuma Windows 7, kadan daga cikin banbanci da ke tsakanin su shi ne
1) Bangaren tsaro:- Kamfanin Microsoft sun kara USER ACCOUNT CONTROL tun daga windows Vista har zuwa windows 7 wanda babu shi a cikin XP, shi kuma aikin da wannan UAC yake yi shi ne ya lura da hanyar da duk wani program da yake son ya yi installing kan shi a cikin computer ya zamanto ba zai yi ba sai ka bashi izini, idan kana amfani da windows Vista ko 7 idan kana son ka yi installing wani program sai ka ga wani dan karamin windows ya bude yana tambayar ka Allow ko Cancil, mene ne dalilin da yasa aka kirkiri wannan tsari, domin kowane irin Virus da zai shiga Kwamfutarka sai ya yi installing kan shi kafin ya shiga, shi yasa suka kara wannan bangaren tsaro tun da dai sai ya yi installation zai yi ta’adi dole sai ka bashi dama tukunnan ya zauna a computer ka, to ka ga babu wanna a Windows XP, shi yasa yawancin Virus da suke shiga XP ba sa iya shiga Win7.
2) Sannan ka ga akwai banbanci mai yawa a wajen karbar Hardware! dukkanin hardware da za ka yi installing idan a kan Win7 ne to za ta zo da shi amma a wani WinXP sai ka nemo, haka wajan yadda program suke za ka a cikin computer da kuma rage matsalar lalacewar su a sanadin Virus shi ma an cireshi a cikin Win7.
3) Idan muka dawo ta wajen yadda Win7 yake iya handling files da folder shi ma an sami ci gaba
4) Windows Defender da Windows Update su ma an kara masu karfi matuka wanda matukar kana da win7 sannan koda wani lokaci ka na Updating Windows din ka kuma kana Updating Windows Defender naka to ko da baka saka Anti-Virus ba kusan irin Virus da suke damun mu a Najeriya computer ka tafi karfin su.
5) Anytime Upgrade kusan idan kana amfani da Win XP home kana son ka mayar da shi Win XP Pro, dole sai dai ka yi upgrading ta hanyar amfani da CD na Win XP Pro kafin ka iya upgrading din shi, amma koda Compterka ta zo da Win 7 Home kana son ka mayar da ita Win 7 Ultimate baka bukatar CD ko DVD abin da kake bukata shi ne kawai Serial Key na Win 7 Ultimate idan ka samu sai ka yi typing Anytime Upgrade a jikin search box na windows take zai fito ka saka wadannan serial numba ba tare da ya hada ka da internet ba ya yi maka upgrading.
6) Ta wajen system ya yi crashing ko kuma nuna maka blue screen of death Microsoft sun cire wadannan matsalolin da ake yawan samunsu tare da windows Xp wanda zai yi matukar wahala OS din ka ya yi crashing ko kuma idan wani matsala ta faru ka kasa recorvery document din ka.
A takaice wannan shi ne kada daga cikin banbanci da ake iya samu tsakanin Win7 da XP. Amma maganar ka ta karshe na cewar ya za ka yi ka komar da Windows 7 zuwa Windows XP, a ka idan computer tazo da OS da yake babba ba bu wata hanya babba wacce aka bayar domin mutum ya iya downgrading OS dinshi, amma za ka iya upgrading daga XP zuwa Vista daga Vista zuwa Win 7, amma za ka iya share shi OS 7 da kake da shi ka mayar da shi XP amma wannan ba ana kiran shi da Upgrading ba ne ana kiran shi da FRESH INSTALLATIONS na gode da fatan za ka yi hakuri na rashin baka amsa da bamu yi a kan lokaci, wannan domin mu tabbatar da mun baku abin da yake ingantacce kuma sahihi. Na gode Allah yabar zumunci