Email cikakken abin da ya ke nufi shi ne Electronic Mail, wato a hausa muna iya kiransa da sako ta hanyar sadarwar intanet.
Email wata hanyace da ake iya bi domin musayar wasiku tsakanin kwamfutoci guda biyu ko fiye da haka. Wadannan sakwannin da mutun zai iya aikawa sun hada da rubutu, da hotuna da sauti, da kuma hoto mai motsi (video) a lokaci guda.
Email ya na da matukar amfani ga ayyukanmu na yau da kullum domin bukatuwarsa a wannan lokaci ya kai bukatar da muke da ita ta wayar tafi da gidanka. Kasancewar a dukkanin harkokinmu da hulda da muke yi da mutane za mu iya musayar rubutu ko magana ko hotuna.
Dalibai suna amfani da akwatin imel dinsu domin ajiyar takardunsu, da kuma bincike da suka yi domin sake amfani da shi, ko kuma aikawa da malamansu. Masu neman aiki suna amfani da akwatin imel wurin ajiyar takardunsu da na shaidar kammalawa domin aikawa zuwa da kamfanoni masu neman ma’aikata.
Kwamfutocin da ake amfani da su domin zama uwar garken sakwannin sune maiframes computers da minicomputers. Irin wadannan kwamfutoci guda biyu suna da tsarin da ya ke basu damar karba da kuma iya aikawa da sakon da mutane ke aikawa zuwa ga abokanan huldansu.
Bayan mutum ya gama rubuta wasikar da zai aika yana bukatar sani adireshin wanda zai aikawa, ta wannan hanya ce kadai wanda ake son ya sami wannan sako zai iya samu. Aikawa mutum guda sako ko kuma ka aikawa da mutane da yawa shi ake kira da “Broadcasting” a tsarin ilimi na email. Sannan sakwanni da zasu iya zuwa ta hanyar imel suna da alama ta ‘@‘.
Shi yasa yana da kyau a wannan lokaci mu yi bayanin yadda tsarin suna ko kuma akwatin aikawa da imel ya ke.
Cikakken yadda kowane tsarin sunan akwatin mutum shi ne kamar haka sunanka@misali.com wanda sunanka shi ne sunan da ka zaba ya wakilce ka a duk lokacin da za a aiko da sako zai duba wannan suna.
Alamar @ wacce itace ke biye da sunanka na nuna cewar wannan zai tafi dakin ajiya da kuma kai sako ne, duk wakon da ake son a aika matukar ba a saka wannan alama ba to ba zai taba tafiya ba.
Misali.com shi kuma ya na fadar uwar garken da zai aika da sakon, saboda haka duk sakon da ba a saka uwar garken da za shi ba to ba zai tafi ba. Saboda haka kana bukatar wadannan abubuwa guda uku kafin ka sakonka ya zo ko kuma ya tafi wurin mutane. Sannan kuma ya kasance babu sarari (space) tsakaninsu.
Ba zaka ya aikawa da wani sakon imel ba sai idan ya kasance kana da akwatin da zaka iya amfani da shi wajen aikawa da kuma karbar sako na email. Wannan akwati shi ne ake kira da “email account“.
TSARIN SHIGA DA AMFANI DA EMAIL
Web-based Mail (Webmail)
Akwai tsari guda hudu da ake da su na karbar sako wanda ya hada da karbar sako ta amfani da browser wanda kusan mafi yawan mutane shi suka sani wanda ake kira da “webmail” ko kuma web-based mail. Shi wannan tsarin yana bukatar dole sai mutum yana da internet tukun zai iya karbar sako ko kuma ya aika da shi. Kamfanoni irin su AOL Mail da Gmail da Outlook.com da Yahoo! Mail suna daga cikin mafi shahara a wurin bayar da wannan tsari.
Na farko dole sai kana da browser da kuma internet sannan za ka iya karba da kuma aikawa da sakon da aka aiko maka daga daya daga cikin wadannan dakuna ko kuma gidaje ta hanyar amfani da damar da suke baka a lokacin da ka mallaki dakin na suna (Username) da kuma kalaman sirri (password).
POP3 Email
Tsari na biyu shi ne tsarin da ake kira da POP3 wanda cikakken ma’anarsa ke nufin Post Office Protocol 3. Wannan tsarin ya yi kama da tsarin mallakar akwatin sako na zahiri irin wanda gidan karbar sako na Post Office su ke yi. Sai dai shima wannan tsari na Kwamfuta ne.
Tsarin POP3 shine tsarin da yake baka damar saukar da sakonka a cikin kwamfutarka ko kuma wayarka sannan daga baya ka iya budesu koda kuma a wannan lokacin baka da internet. Ana iya amfani da Microsoft Outlook wurin hada email dinka da POP3 Mail Server
IMAP Email Servers
IMAP ko kuma ka kira shi da cikakken ma’anarsa ta “Internet Message Protocol” wannan wani tsari ne da yake baka damar shiga uwar garken da ake tara su sakwannin ta hanyar baka damar shiga cikin “folder” da ta ke mallakinka. Samun wannan dama ya nuna kana da cikakken iko wajen shigarwa da kuma ajiyar sakwanni kai tsaye. Wannan tsari ya fi POP3 domin kuwa bayan daka damar shiga haka za ka yi amfani da kwamfutarka da wayoyinka wurin karba ko kuma aikawa da sako. Ana iya amfani da Microsoft Outlook wurin hada email dinka da IMAP Server
MAPI email Servers.
MAPI ko kuma Messagin Application Programming Interface wannan tsari ne da kwamfanin Microsoft ya ke da shi a uwar garke domin bada damar aikawa da kuma karbar sakwanni a internet ko kuma a kwamfutoci da wayoyin mutane.
Amma yana da kyau mai karatu ya sani cewar dukkan wadannan tsare tsare da ake da su dole sai mutum yana da internet zai iya karbar sakon. Shi webmail sai kana da internet zaka iya karba da kuma iya karanta sakonka, amma sauran ukun su suna bukatar internet wurin saukar da shi a na’urarka da kuma lokacin da kake son ka aika da amsa ko kuma wani sabon sako.
A darasi na gaba da yardar Allah za mu koyar da yadda ake bude imail ta hanyar amfani Gmail da Outlook.com da kuma Yahoo! Mail
Menene gmail
Mene ne INTERFACE