38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Mene ne Software?

Software waɗansu rubutu na umarni ne da ake yi domin su iya sarrafa Hardware ko kuma su umurci kwamfuta yin wani abu ko kuma barin wani abu, wanda a Ingilishi ake cewa “Software is a set of instruction that control hardware or tells computer what to do”. Idan babu software, hardware ko kuma kwamfuta ba ta da wani amfani. Misali idan babu Browser a jikin kwamfuta babu yadda za ka yi ka buɗe wani shafi a intanet, haka idan babu babbar manhajar kwamfuta Operating System babu yadda za a yi ita birauzar ta iya hawa kan wannan kwamfutar sannan har kai ka iya ɗaukarta ka yi aiki da ita.

Keyboard da mouse da suke aiki da kwamfutarka ba su sami damar yin aikin ba sai bayan da aka saka musu manhajar su wacce take sarrafa su, haka hatta wayoyinmu da muke iya amfani da su wajen yin kira, rubuta wasiƙu, ɗaukar hoto duk da babu software da ba za su yi aiki ba.

Shi ya sa muka kira software da Manhajar Kwamfuta domin kasancewar ita ke sarrafa dukkan wani abu da ke ciki,  da kuma wajen kwamfutar.

Karkasuwar Software

Ga al’ada a na kasa Software kashi biyu, akwai System Software da kuma Application Software.

Mene ne System Software?

System Software shi ne muke kira da babbar manhaja wadda ita ce kwamfuta ke buƙata da farko domin ta sarrafa dukkan wani kayan lantarki da ake saka mata da kuma waɗansu kananan manhajoji da mutum yake buƙata ya yi amfani da su a cikin ita kwamfutar.

Shi ya sa system software suke kiranshi a Turance da “Set of Instruction that control Hardware” kenan System Software shi ke sarrafa dukkan wani Harware da ke jikin kwamfuta, waɗanda suka haɗa  da Operating System, da Drivers da su suke sarrafa hardware da kuma irin su Linkers da Debuggers. Haka System Software yana sarrafa dukkan wani Software da kwamfuta take buƙatar shi da kuma wanda ɗan adam ya ke buƙata domin yin amfani da su. Shi ya sa shi kanshi System Software ya kasu gida biyu.

Karkasuwar System Software

System Software ana iya kasa shi gida uku

  1. Operaating System
  2. Utility Software
  3. Device Driver

 

2 COMMENTS

  1. Comment:Gaskiya ina matukar karuwa da wannan shafin, domin kuwa ni mutum ne me matukar san naga na kware a bangaren ilimin na,ura me kwakwalwa.
    saboda ina matukar jin dadin wannan shafin naku, nagode ALLAH YA KARO BASIRA DA ILIMI ME AMFANI.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img