Kwarai da gaske malam Mustapha Adamu ai daman NOTEBOOK Computers an yi su ne domin yin karamin aiki da kuma ayyukan dalibai na makaranta wanda ya shafi rubutu da jotting, to amma babban abin da kowa yake korafi akanshi shi ne CD/DVD Room, wanda daman ita computer ba a yi mata muhallinshi ba. To amma wani hanzari ba guduba, dukkan wata computer da bata da dvd ko cd a jikin ta, ko kuma ya lalace, masu kere-keran kayan computer sun yi abin da ake kira da EXTERNAL PERIPERAL wato duk abin da ka gan shi tare da computer ana aiki da shi akwai irin shi wanda ake amfani da PORT ake jona shi, MISALI ita wannan NOTEBOOK irin ta da bata zuwa da EXTERNAL CD/DVD amma ta yanzu idan sabuwace ka siya tana zuwa da shi, haka kuma ko da wacce ka gani ba ta zo da shi ba to za ka iya shiga kasuwa inda ake sayar da kayan computer ka ce kana bukatar EXTERNAL CD/DVD, amma fa yana da dan tsada domin shi ma tafi da gidan ka ne. za ka iya amfani da shi a kowace computer. Da fatan ka gamsu.