23.5 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

PROGRAMING LANGUAGE WANE NE YA KAMATA NA FARA KOYA?

Mene ne Programing Language ?

WANI TSARARREN RUBUTU NE DA AKE YI DOMIN KURMAN MASHIN, AMMA KUMA YA SANYA SHI YA KASANCE MAI JI KAMAR MAI KUNNE.

Daga ina ya kamata ka fara?

Mene ne dalilin da ya sa kake son ka fara yin Programing Language? Wannan ita tambayar da ya kamata ka fara yi wa kanka da kanka, kasancewar kowane Programing Language akwai abin da yake yi, da kuma abin da ake iya yi da shi, da kuma irin mashin ɗin da yake iya sarrafawa, da kuma alaƙar da take tsakanin sa da sauran Programing Language da ake da su.

Programing Language nawa ne a duniya?

Programing Language suna da matuƙar yawa, tun daga wanda ake amfani da shi a cikin ƙananan na’urori da kuma manya, da waɗanda ake amfani da su a cikin gida da kuma ma’aikatu da kuma waɗanda ake amfani da su a harkokinmu na yau da kullum. Sai dai a cikin waɗannan Programing Language  ɗin akwai waɗanda suka sami karɓuwa akwai waɗanda ko sunan su ma  mutane da yawa ba su taɓaji ba.

A wannan muƙalar za mu ɗauki yaren Kwamfuta waɗanda suka fi shahara guda tara (9) a wannan zamani, waɗanda kuma da su ne duniya ke taƙama kuma kusan duk wani abu da za ka gani a wannan lokaci idan dai na’ura ce, tun daga kayan wasan yara (games) da na’urorin da manya suke amfani da su kamar wayoyin tafi-da-gidanka, da ma manya da ƙananan manhajoji dukkaninsu ba sa wuce ɗaya daga cikin waɗannan Programing Language  ɗin.

Waɗannan programming guda tara ne, waɗanda suka hada da

  • Python
  • JAVA
  • C
  • PHP
  • C++
  • JavaScript
  • C#
  • Ruby
  • Objective-C

Mene ne dalilin da zai sa na koyi Programing Language ?

Akwai ra’ayi mabambanta ga masu koyon yaran kwamfuta. Waɗannan dalilai sun sha bambam, sai dai daga baya ra’ayin yana komawa ga mataki na ƙarshe amma kuma dukkansu babu matsala ga wanda mutum ya ɗauka.

An tattara ra’ayoyin jama’a masu koyon Computer Programming har gida shida (6), ta hanyar la’akari da ta ina mutum ya ɓullo da kuma ina yake son ya ɓulla a wannan harkar.

  • Ba su san dalilin da ya sa suke koyonprogramming
  • Domin amfanin yara.
  • Domin jin daɗi da nishaɗantarwa
  • Yana da ra’ayin yinprogramming
  • Yana son ƙara wa kanshi sani a cikinPrograming Language
  • Domin ya sami kuɗ

A darasinmu na gaba za mu ɗauki kowane ɗaya daga cikin waɗannan ra’ayoyi mu bada shawara ingantacciya ga duk mutumin da yake son ya koyi programmig language cikin waɗannan ra’ayoyi shida.

Fashin baƙi ga kowane ra’ayi guda cikin shidan nan

1                Ba su san dalilin da ya sa suke koyon programming ba.

Ga waɗanda suka tsinci kansu a cikin karatun kwamfuta kuma suka dace da shiga ɓangaren Programing Language, to shawarar da za mu ba su ita ce su koyi Python.

2                Domin amfani yara.

Duk wanda yake son ya koyi yaren kwamfuta domin ya ƙirƙiri wata manhaja domin ƙananan yara ko kuma ya koyi yaren da yake son ya koyawa yaransa su ma a fara damawa da su a kan abin da ya shafi Programing Language, to ya koyi Python.

3                Domin jin daɗi da nishaɗantarwa

Wanda yake da ra’ayin yin Programing Language  amma kuma yana yin shi domin jin daɗi da ɗebe kewa, da nishaɗantarwa, to akwai tambayoyi da za a yi masa, irin amsar da ya bada ita ce sakamakon inda ya kamata ya kai kanshi wurin abin da ya cancanta ya koya.

Kana da wani yare da kake da sha’awar amfani da shi a cikin guda shidan nan? Idan ba shi da shi, kawai shi dai yana son a koya mishi wanda zai fara to yana da zaɓi guda huɗu.

  1. Yana son ya koyi programmin language cikin ruwan sanyi, to ka koyi Python.
  2. Idan kuma kana son ka koyiPrograming Language da ya fi cancanta da kyau wurin koya, to ka koyi Python
  • Idan kuma kana son ka koyiPrograming Language amma ta yare mai ɗan wahala, to a nan za mu ba ka zaɓi ka koyi yaren da ake amfani da shi wurin sarrafa moto ta hawa waɗanda suke da tsarin manu’al da idan kana son za ka koyi yaren da za ka riƙa yin manhajoji dasu za su riƙa yin aiki a motoci na manu’al sai mu ce ka koyi yaren C Programming. Idan kuma kana son ka koyi yaren da za ka riƙa yin manhajojin da za su riƙa yin aiki a cikin motoci auto sai mu ce ka koyi JAVA Programming.
  1. Idan kuwa yana son ya koyiPrograming Language ta hanyar da ta fi kowace wahala, wacce zai samu sauƙi idan yana son nan gaba ya koyi wani yare, sai mu ce ya koyi C++ Programming.

4.      Yana da ra’ayin yin programming

Shi ma wanda yake da ra’ayin yin Programing Language , shi ma za a tambaye shi, ƙana da wani yare da kake da sha’awar amfani da shi a cikin guda shidan nan? Idan ya amsa cewar yana da shi, sai a sake tambayar sa wane yare ne kuma ɓangaren me? A wannan wurin yana da zaɓi guda huɗu (4).

a)    Ina son in riƙa yin webdesign.

Kana son web site da zai riƙa yin aiki irin su facebook ko twitter da makamantansu? Idan amsar ta za ma e, sai mu ce maza ka koyi JavaScript. Idan kuwa ya ce bai sani ba, za mu tambaye shi kana son ka gwada wani abu sabo a rayuwarka ta ɓangaren web design? Idan ya ce e, sai mu tambaye shi shin a cikin kayan wasa na yara wanne ne kake ra’ayi ko kuma ya fi ba ka sha’awa. Idan ya ce lego sai mu ce ya koyi yaren Python. Idan kuma ya ce Play-Doh shi ne kayan wasan da ya ke ra’ayi sai mu ce ya koyi Ruby Programming. Idan kuwa ya ce shi bai san wani kayan wasa ba, ko kuma ya ce yana son ya yi amfani da kayan wasanni tsofaffi na da sai mu ce ya koyi PHP.

b)   Ina son aiki a manyan kamfanoni

Idan ka ce kai bayan ka iya yin programmin language kana son ka sami aiki ne a manyan kamfanoni na kimiya da fasaha, za mu tambaye ka ko kana da ra’ayin aiki a kamfanin Microsoft? Idan ka ce e, to sai mu ce ka je ka koyi C# Programme. Idan kuwa domin jin daɗi da nishadi ne, sai mu ce ya koyi JAVA Programming.

c)    Aiki da wayoyin komai da ruwanka

Idan kuma ya ce ina son idan na gama koyon Programing Language  in riƙa yin manhajojin da za su riƙa aiki da wayoyin komai da ruwanka (Smart Phones) sai mu tambaye ka wayoyin guda biyu ake da su. Akwai waya ƙirar Apple masu tsarin babbar manhajar iOS, da kuma wayoyi ƙirar Android. Idan ya ce yana son ya yi aiki da wayoyi ƙirar Apple sai mu ce ya koyi C Programming.  Idan kuwa ya ce yana son ya yi aiki da wayoyi ƙirar Android sai mu ce ya koyi yaren JAVA.

d)   Domin haɗa kayan Games

Idan kuwa ya ce yana son bayan ya iya programming ɗinsa ya riƙa yin manhajojin da ake amfani da su a cikin na’urorin games kamar playstation da irin su Nitando da dai makamantansu sai mu ce ya koyi C++  amma sai dai yanada ɗan wahalar koyo.

5.      Yana son Ƙara wa kanshi sani a cikin Programing Language

Ga wanda daman yana dan son programming kuma yana son kawai ya ƙara wa kanshi sani ne ko kuma sanin madogara, shi ma za a tambaye shi kana da wani yare da kake da sha’awar amfani da shi a cikin guda shidan nan? Idan ya amsa cewar yana da shi. Sai a sake tambayar sa wane yare ne kuma ɓangaren me? A wannan wurin yana da zaɓi guda huɗu (4).

a)    Ina son in rika yin webdesign.

Kana son web site da zai riƙa yin aiki irin su facebook ko twitter da makamantansu? Idan amsar ta zama e, sai mu ce maza ka koyi JavaScript. Idan kuwa ya ce bai sani ba, za mu tambaye shi kana son ka gwada wani abu sabo a rayuwarka ta ɓangaren web design? Idan ya ce e, sai mu tambaye shi shin a cikin kayan wasa na yara wanne ne kake ra’ayi ko kuma ya fi baka sha’awa. Idan yace lego sai muce ya koyi yaren Python. Idan kuma ya ce Play-Doh shi ne kayan wasan da ya ke ra’ayi sai muce ya koyi Ruby Programming. Idan kuwa yace shi bai san wani kayan wasa ba, ko kuma yace yana son ya yi amfani da kayan wasanni tsofaffi na dai sai muce ya koyi PHP.

b)   Ina son aiki a manyan kamfanoni

Idan ka ce kai bayan ka iya yin programmin language kana son ka sami aiki ne a manyan kamfanoni na kimiyya da fasaha, zamu tambaye ka ko kana da ra’ayin aiki a kamfanin Microsoft? Idan ka ce e to sai muce ka je ka koyi C# Programme. Idan kuwa domin jin dadi da nishadi ne sai muce ya koyi JAVA Programming.

c)    Aiki da wayoyin komai da ruwanka

Idan kuma ya ce ina son idan na gama koyon Programing Language  in riƙa yin manhajojin da za su riƙa aiki da wayoyin komai da ruwanka (Smart Phones) sai mu tambaye ka wayoyin guda biyu ake da su. Akwai waya ƙirar Apple masu tsarin babbar manhajar iOS, da kuma wayoyi ƙirar Android. Idan ya ce yana son ya yi aiki da wayoyi ƙirar Apple sai mu ce ya koyi C Programming.  Idan kuwa ya ce yana son ya yi aiki da wayoyi ƙirar Android sai mu ce ya koyi yaren JAVA.

d)   Domin hada kayan Games

Idan kuwa yace yana son bayan ya iya programming ɗin sa ya rika yin manhajojin da ake amfani da su a cikin na’urorin game kamar playstation da irinsu Nitando da dai makamantansu sai muce ya koyi C++  amma sai dai yana dan wahalar koya.

A darasinmu na gaba da yardar Allah za mu yi cikakken bayani a kan mataki na ƙarshe, wato IDAN MUTUM NA SON YA SAMI KUƊI A ƁANGAREN PROGRAMMING LANGUAGE ME ZAI KARANTA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img