38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Rayuwar Dalibai ‘yan Najeriya A Kasar Ghana

Mun samu tattaunawa da wasu daga cikin dalibai ‘yan kasar Najeriya dake karatu a kasar Ghana, a yayin da daliban suka labarta mana irin ci gaba da suke samu a tsawon zaman su a wannan kasa, duk da yake akwai ‘yan matsaloli da suke fuskanta ta fuskar zamantakewa da jama’a, musamman bambancin harshe da suke fuskanta da kuma wayewa irin ta kasashen turai, wanda ya jawo karancin kula da addini ga mafi yawancin al’ummar kasar. Hakanan ta bangaren ci gaban karatu, Ghana tana daya daga cikin kasashen da suke kan gaba a harkar ilimi a yammacin kasashen Afirka. Kasantuwarta daya daga cikin kasashen da kasar Ingila ta raina, wannan ya taimaka wa kasar wajen samun zama masu amfani da harshe guda wato turanci, tare da fitar masa da dukkanin hakkinsa lokacin da suke karatunshi ko kuma ake koyar da su shi. Wannan yana daya daga cikin dalilan da ya taimakawa wasu daga cikin dalibai ‘yan asalin kasar Najeriya da ke karatu a wannan kasa, domin sun sami karin gogewa da kuma kwarewa a harshen turanci.

Musamman idan aka yi la’akari da ci gaba da ake samu a bangaren ilimin Kimiyya da Fasaha, da kuma hanyoyin kasuwanci, wanda ya jawo hankalin jami’o’in kasashen turawa da wasu kasashen renon Igila, kamar kasar Indiya da makamantansu, wadanda a wannan zamani suna matukar tashe a bangaren kimiyya da fasaha, suka kafa jami’o’insu a wannan kasa, suka kuma samu matukar karbuwa a hannun gwamnati. Karbuwar da suka samu ya kawo dalilin da ya sanya irin wadannan jami’o’i da manyan kamfanunnuka suka saka hannuwansu a ciki domin ganin cewar sun taimakawa harkar ilimin da dalibai da suke kasarsu sun sami ingantaccen ilimi da kuma samun aiki a ko’ina a fadin kasar. Da yawa daga cikin dalibai da ke jami’o’i daban daban a wannan kasa ta Ghana, sun labarta mana cewa akwai bambanci mai nisa a harkar cigaban karatun boko, tsakanin kasarmu ta Najeriya da kuma kasar Ghana, idan aka yi la’akari da adadin jami’o’in kasashen ketare da suka kafa makarantu a nan, wanda idan kayi la’akari da yanayin yadda ake gabatar da karatu a jami’o’in da suke Najeriya da kuma yawan yajin aiki da malamai suke yi, da kuma irin rashin baiwa bangaren ilimi mahimmanci da gwamnati take yi sai kaga lallai a kwai canji matuka. Ga kuma sauki wajen karantar da dalibai, domin baya yiwuwa a kasar Ghana a ce kana karanta wani kwas kuma ace an shigo maka da wani karatu da baya cikin tsarin karatunka, sannan kuma malamai suna kokarin ganin dalibai lallai sai sun fahimci karatun da ake yi musu, sannan kuma su malaman suna ba da hankalinsu wuri guda ga dalibai musamman ace sun fahimci cewar wannan dalibi bai cika gane karatu ba. Ga kuma isasassun takardun karatu, wanda idan malami ya baka aiki ko da na zamanine ko sabon ilimine, zaka samu littafin a wannan dakin bincike. Idan kuwa aka yi rashin sa’a babu wannan littafin da kake nema, mai lura da wannan dakin binciken zai dauki sunan ka da kuma ajin da kake karatu sannan kuma ya rubuta sunan littafin da kake bukata, domin kai kadai sai hukumar makaranta ta sayo maka littafin kuma idan an kawo a ba ka ka ci gaba da bincikenka a ciki.

Ga kadan daga cikin ra’ayoyin wasu cikin daliban kasar Najeriya da suke karatu a jami’o’i daban-daban a kasar ta Ghana.

Alhamdulillahi, ina muna matukar godiya ga Allah da ya bamu ikon barin kasar da mu zuwa wata kasa mai bambancin al’adu, da kuma karancin kula kan al’amura na addini, ya kuma bamu ikon zama da wadannan al’umma cikin aminci, ba tare da tsangwama ba, ko kuma kabilanci ba, muka kuma kasance wakilai na gari ga kasarmu Najeriya a wannan kasa. Dangane da ci gaban karatu; tabbas na samu ci gaba a wannan kasa ta Ghana, kasantuwar na samu darussa masu amfanarwa a harkar karatuna na ilimin computer, da kuma sanin harkar kasuwanci a fasahance. Duk da yake akwai ‘yan matsaloli na zamantakewa da na fuskanta, amma hakan bai sanya ya shafi karatuna ko addini na ko kuma bambancin kasantuwata ba dan wannan kasa ba. Duk da yake akwai banbanci na ganin cewa duk dan Najeriya mutumin banza ne, kasantuwar bata sunan kasar tamu da wasu marasa kishin kasa da kuma kishin kansu suke nunawa. Musamman idan muka yi la’akari da masu harkar fasakwauri a internet (yahoo boyz), ko kuma harkar fashi da makami, ko damfara da yin zamba cikin aminci, da kuma harkar shigowa da muggan kwayoyi, za ka samu kusan mafi yawanci wadanda ake kamawa ‘yan kasarmu ne. Hakan ya jawo karancin kallon mutunci da ake yiwa ‘yan kasar ta Najeriya. Duk wani dan kasuwa ya na maka kallon ko kana da kudi ya cuce ka, ko kuma yana tsoron kar ka cuce shi. Amma duk da haka Alhamdulillahi, tun da duk rayuwarmu muna yinta ne tsakaninmu da dalibai ‘yan uwanmu da muke tare, kuma mutanen kirki, zamantakewarmu tsakanin junanmu ma har ya taimaka wurin canja rayuwar wasu da yawa da suka zo nan da tunanin aikata wasu ayyukan na assha. Sheriff Shuaibu Abubakar na jihar Kadunan Najeriya. dalibin shekarar karshe a bangaren ilimin kasuwanci a kimiyyance wato (business information technology) da ke jami’ar Greenwich ta Ingila da ke IPMC Labone/Accra Ghana.

A matsayina na dalibi a wannan kasa ta Ghana, zan ba dalibai ‘yan ‘uwana da suke da ra’ayin zuwa karatu wannan kasa dama wadanda suke yin karatu a nan akan su dage kan abin da ya kawosu, domin samun nasara a harkar karatun su, da kuma yin kokari wajen yin abota da abokanan kirki wajen yin mu’amalarsu, su kuma kasance wakilai na gari na kasarsu Najeriya a wannan kasa. Bashir Bature, na jihar Kadunan Najeriya. dalibin shekarar karshe a bangaren ilimin kasuwanci a kimiyyance wato (business information technology) da ke jami’ar Greenwich ta Ingila da ke IPMC Labone/Accra Ghana.

To Alhamdulillahi da damar da muka samu na zuwa wannan karatu tun muna da lokacin yin hakan, zan kuma ba iyaye shawara akan bawa ‘ya’yansu tarbiyya ta gari domin su kasance mutanen kwarai a duk inda suke, su kuma yi hakuri da dukkan wahalar da za a fuskanta wajen bawa yaransu ilimi na gari, da kuma taimaka musu a harkar ilimi da kuma yi musu addu’a akan Allah ya taimaka musu. Ghana kasace ta karatu da kasuwanci kwarai da gaske! Nasir Abubakar na jihar Katsinan Najeriya. dalibin shekarar karshe a bangaren ilimin kasuwanci a kimiyyance wato (business information technology) da ke jami’ar Greenwich ta Ingila da ke IPMC Labone/Accra Ghana.

Darajar dalibi a nawa tunanin shine tsare mutuncinsa da kuma sanin abin da ya kawo shi kasar da ba tasa ba, da tuna alkawarin da ya daukarwa iyayensa a rayuwarsa a yayin da baya tare dasu, ina kuma ba dalibai ‘yan uwa na shawara a duk kasar da suka tsinci kansu, su tuna Allah na tare dasu. Hassan Muhammad Yusuf, Potiskum da ke Jihar Yoben Najeriya. dalibin shekarar farko a bangaren ilimin kasuwanci wato (Business Administration) a jami’ar Sikkim Manipal University India da ke Accra Ghana.

Ni kam ban fuskanci wata matsala ba a wannan kasa, saboda takaici na da kasata dama wutar lantarki, to an share min hawaye na a wannan kasar, saboda karatun kimiyya a kasar da babu wuta ba karamar nakasu ba ne kwarai, kuma ina fata kasata ta Najeriya za ta gyara wannan matsalar wata rana. Muhammad A Madu Potiskum da ke Jihar Yoben Najeriya, dalibin shekarar karshe a bangaren ilimin kasuwanci a kimiyyance wato (business information technology) da ke jami’ar Greenwich ta Ingila da ke IPMC Labone/Accra Ghana.

Nidai shawarata musamman ga ‘yan uwana mata da suke da ra’ayin fita kasashen waje karatu suji tsoron Allah da kuma kiyaye darajar su da tuna cewa su ba tijara bane na kasuwanci, kamar yadda wasu matan suke mayar da kawunansu, musamman a wannan kasa ta Ghana inda ya kasance mace ta zama tamkar ledar pure water, domin karancin addini, da kuma tsananin daukar rayuwar turawa da sukayi. Su kuma samari su kiyaye kawunansu daga neman matan banza, musamman idan suka yi la’akari da cutar kanjamau da ta yawaita a wannan kasa, kuma ina bayar da shawara ga sauran ‘yan uwa na mata masu ra’ayin zuwa Ghana karatu akan tuna cewa mu masu rauni ne, amma idan muka sanya Allah a gaba, to, shi mai tsari ne akan mutum. Ambashair Sumayin. dalibar shekarar karshe a bangaren ilimin kasuwanci a kimiyyance wato (business information technology) da ke jami’ar Greenwich ta Ingila da ke IPMC Labone/Accra Ghana.

2 COMMENTS

  1. hakane kam, dan a gaskiya nima ina daya dagacikin daliban dasuke karatu a kasar ghana, ban-bancin shine kuwa gurin yaren turanci dan har shewa suke ‘yan najeriya basu iya turanciba dan nima har kunya nakeji yadda naga yan najeriya sukeyin turancin. wannan yazama kalubale ga gwamnatin najeriya akan kula da karatun dalibai. allah yabada daman gyarawa…

  2. dalibin ajin farko na kwalejin ilimi ta jihar neja.ina baiwa dalibai yan’uwana shawara akan muji tsoron Allah a duk inda muke.saboda Allah s.w.t yana kallon mu duk inda muka shiga,kuma kowa zaiyi bayani a gaban Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img