RECYCLER VIRUS
Recycler Virus wani daya daga cikin virus ne da ake dasu a cikin kusan Virus sama da miliyan bakwai da ake da su a duniya, na san wani zai yi mamaki akan haka, shi dai makasudin yin wannan virus domin ya rinka hayayyafan kanshi a cikin computer ne, ta yadda zai rinka kirkiran folder da take cikin computer ka. Misali idan wannan virus ya shiga cikin computerka kuma babu antivirus a cikin ta zai rinka kirkiran sunan folder yana karawa a cikin folder da ka bude. misali idan ka shiga cikin My Music folder sai kaga wata irinta da suna My Music ammakarshen zai kare da .exe. Wani yanki na cutarwa da wannan Virus yake yi shine zai iya share maka file ko kuma document da ke cikin computer ka su koma da .exe idan haka kuwa ta faru idan antivirus ya gansu zai sharesu. Bayan da aka gano yadda wannan cutarwar take sai suka canza salo ta yadda idan wannan virus ya kama computer ka ba zai cinye files dinka ba sai ya cinye maka folders da suke cikin computer su koma shortcut.
YA ZANYI IN DAWO DA FILES DA FOLDERS DA SUKA BACE?
Idan har ka fuskanci irin wannan matsala wacce take a daidai wannan lokaci da muke tattara wannan bayanai, kamfanin Microsoft wanda su suke yin Windows OS, kamar XP da VISTA da Windows 7 suna riga sun toshe waccan kafa da ake amfani da ita har RECYCLER VIRUS ta iya yin ta’adi a cikin computerka sai dai tayi a jikin MEMORY, ko FLASH ko kuma EXTERNAL HARD DISK DRIVE, idan har kaga computerka irin wannan virus ya kamata abu na farko da zaka yi shine ka yi Windows Update, idan ka yi wannan updating to ita computer da kanta zata magance maka wannan matsa. Mataki na biyu shine ya kasance kana amfani da Licence Anti-Virus sannan kuma kayi updating na shi shima. Duk wata computer da akayi updating din windows dinta kuma aka yi updating antivirus dinta ta irin wannan virus na RECYCLER da wadanda ma baka sansu ba idan ya shigo computer ka zai zama kamar file irin su video ko music ko kuma word document bashi da wani tasiri ko kadan. To amma fa ka sani idan har kai baka da damar da zaka yi updating, misali, kana amfani da ita computer a Business Center ne kuma babu Internet Connection a wurin to akwai matsala, hanya mai kyau da zaka iya magance irin wannan matsala shine ka je ka yi downloading KASPERSKY RESCURE DISK a website na kaspersky dake htt://www.kaspersky.com zaka same shi kyauta.
ME KASPERSKY RESCURE DISK KE YI?
Kaspersky Rescure disk yana taimaka maka wajen cire Virus a cikin computerka ba tare da ka saka anti-virus ba, wato shi wani mukulline da zaka iya amfani da shi idan kafin computer ka ta loda windows sai shi wannan program na rescure disk ya fara aiki, zai yi installing kanshi na wucin gadi, wato a maimakon idan ka kunna computer ka ka ga windows ya tashi sai kaga RESCURE DISK ya dauka. Ko da yake idan kayi downloading dinshi zai zo a dunkulellen file wanda ake kira da (iso) kana bukatar wani program na musamman da ake burning cd kamar Nero ko Ashampoo Burning Studio da dai makamantansu, sune zaka iya amfani da su wajen burning wannan file da kayi downloading ya zama mai amfani. Wato bayan kayi downloading dole ka mayar da shi ya zama CD ko DVD ta yadda computerka zata iya tashi da shi.
BABU VIRUS A COMPUTER TA AMMA FOLDERS BASU DAWO BA, YA ZAN YI?
Bayan ka kammala wadancan hanyoyi guda biyu, to daga cikin abinda shi wannan Virus yake yi shine ya mayar da Folder ya koma Shortcut. Asalin folders da suke cikin Flash Memory ko External Hard Disk suna nan, abinda shi wannan virus yake yi shine ya boye su, su zama baka iya ganinsu ko da ka bude Hidden File da folders, amma dai lallai suna nan a ciki, wanda hakan ta faru da shi yayi formatting to ya sani ya yi ta’adin da shi virus din baiyi ba.
YA ZA AYI IN FITO DA BOYAYYUN FOLDER NA?
1. Zaka shiga Control Panel
2. Ka shiga Folder Option
3. Ka click akan View
4. Kanemi inda aka rubuta Hidden File and Folder
5. Ka latsa inda aka rubuta Show Hidden File, Folders and Drives
6. Zaka cire abubuwa guda uku da suke karkashi abu na biyar (wato zaka ga an saka alamar good a gefensu sai ka cire su)
7. Hide empty Drives in the computer folders
8. Hide extensions for known file type
9. Hide protected Operating System files (Recommended)
10. idan ka cire na karshe zai nuna maka wani dan window sai ka clicking akan OK
11. bayan ka gama sai kayi clicking akan Apply sannan ka saka OK
To bayan ka gama wannan matakai kamar yadda muka lissafa sai ka koma MyComputer ka bude Flash Memory ko kuma External Hard Drive zaka kaga asalin folders dake ke ciki, amma kuma sunyi dishi-dishi, wannan alama ce dake nuna cewar wadannan file suna boye ne, wadancan matakai da kabi su suka fito maka da su a halin yanzu, sai mataki na karshe shine ka mayar da su folders su zama ba a boye ba.
1. Zaka yi right clicking akan folder da kake son ka fito da ita
2. sai ka yi clicking akan properties
3. sai zabi Customize
4. sai ka latsa Change Icon
5. wani karamin Window zai bude sai ka yi clicking akan Restore Default
6. sai kayi clicking akan OK
7. sai ka dawo latsa General
8. A karkashin shi zaka ga Hidden sai ka cire good na aka saka
9. sai kayi clicking Apply sannan OK
wannan shine hanyar da zaka bi ka fito da wannan su wadannan Hidden folder da RECYCLER VIRUS ta boye, amma kuma kana bukatar bayan ka gama fito da duka folders dinka, cire wancan matakai daka bi ka fito da hidden folder ka, domin barinsu a bayyane zai iya kawo matsalar lalacewar computer ka domin ka fito da dukkan sirrin files da suke cikin computer. zaka bi mataki na 1 zuwa 3 na farko, sai ka nemi Restore Default ka latsa, sannan ka clicking Apply sannan OK.
kai dama muna da matsala da RECYCLER amma yanzu kan na samu solution. THANKS
Inna godiya da wannan sashi @ isa mg kn thank you