A cikin wayar hannu da computer akwai wani abu mai amfani ga mutane mai suna Reminder musammama Musulmi wajen tabbatar dakai a cikin sahun da addini yake bukata. Da kuma fitar dakai daga abinda Allah da Manzonsa suka suffanta a matsayin munafurci. Malam bature ya kirkiri reminder ne dan tunatar da ‘yan uwansa wasu abubuwa na rayuwa, amma kuma amfanin reminder ga Musulmi yafi masa amfani.
Duba da yadda Allah ya fada da kansa cewa “KU CIKA ALKAWARI. DOMIN LALLE SHI ALKAWARI ABIN TAMBAYAWANE” (Isra’ 17:34).
Cikin hikimar Allah, ya kawo mana wannan abu mai amfani dan tabbatar da alkawari da sauran Uzirori na rayuwa.
AMFANIN REMINDER A WAYA
- Yana taimakawa wajen cika alkawari tsakanin al’umma.
- Yana tabbatar da kamalar mutum ta cika alkwari.
- Yana hada kan al’umma ta wajen halattar taro.
- Yana tunatar da mutum kana nun aiyuka ds.
SIFFOFIN REMINDER
- Yana dauke da kwanan wata,
- Yana dauke da watanni goma sha biyu, da kwanakin cikin mako,
- Yana dauke da lokaci da kalanda dan tabbatar da lokaci
- Yana dauke da setin kararrawa wato (alarm)
- Yana dauke da wurin rubuta abinda yake ranka na daga abinda zaka yi.
YADDA AKE SETA REMINDER
Ana seta reminder ta hanyar zaban rana da lokaci da wata da kuma suna abinda zaka yi ko zaka je a wannan lokacin. Wanda da zarar lokacinsa yayi na bugawa da kansa zai aiwatar da abinda aka umarceshi, yayi. Â Yana dauke da alarm da sunan abinda zaka aiwatar akan waya ko computer. Yana tuni kafin lokacinsa ya cika ta hanyar alarm.
Alhamdulillahi da wannan da wannan tunatarwa dan dayawa suna dashi amma ba asan amfaninsa ba.
wannan taimako ne akaimana,ni ina amfani da reminder sobada in rika cika alkawari,domin duk mutumen da baya cika alkawari to ba shakka yana cikin munafukai,Allah ya tsaremu,amin.
Allah ya saka da alkhairi da wannan tunatarwa.
INNA FARIN CIKI GA WANNAN SHAFI NA GODE KUHU TA LAFIYA
Aslm. Agaskiya inna maimatukar nuna jin dana da godiya ta ga wannan katafare fili mai dauke da
1,Limantawa
2,Fada kadarwa
3,Karu wa tafannoni daban-daban
4,kai !!! Dai sauran abubuwan da bazan iya lissafa su ba asaboda haka naga yada ce indan turo sakon Godi ga wannan katafaren zaure. Mai albarka.
Allah ya taimaka amin
Asslmu alaikm) gaskia Alhamdu-lillah ba abin xance muku sai godiya Allah Yasa da alkhairi da irin taimakon da kuke yimana..
Allah Ya taimaka..
Godiya muke da wannan fadakarwa, amma ni inada computer ban san inda zan samu remainder ba a ina ne zan shiga in samu?
Wannan karatu ya shafi wayar hannu ce. Idan kana bukatar na computer to zaka yi amfani da Outlook ne
mungode da wannan kayataccen shafi da ke ilimantar da al’umma Allah ya saka muku da alkairi.inada samsung at&t a877 inaso inyi rajistar anti lost ya zanyi ga lambata 08060002270 ko gsombaba@yahoo.com?nagode