Ba mamaki mu yi bankwana da daukar hoto da manyan wayoyinmu, sakamakon sabuwar kamarar da kamfanin Toshiba ya fito da ita.
Sabuwar fasahar ta kamfanin na Japan, za ta bayar da damar daidaita fasalin hoto bayan an riga an dauke shi.
Madubin kamarar na hangen abubuwa daban daban ta bangarori da dama.
Za kuma a iya amfani da su wurin daidaita hoto bayan an dauka. Jami’ar Stanford ce ta fara kirkiro da fasahar amma bata kai labari ba saboda girmanta da kuma tsada.
Manhajar OS za ta maye gurbin Android
Za a samar da manhajar kwamfiyuta ta Ubuntu a wayoyin salula na komai da ruwanka, wanda zai ba da damar amfani da ita a kwamfiyutar tebur.
Sabuwar manhajar ta OS – za a fara samar da ita ne da farko ta hanyar sauko da ita daga shafin internet domin maye gurbin manhajar Android ta wayoyin Samsung Galaxy Nexus.
Sai dai ana fatan nan gaba a wannan shekarar za a fara sayar da wayoyi masu dauke da manhajar ta Ubuntu.
Allah Ya taimaka