38.2 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Tag: google

Yadda ake yin Bincike (search) da Google Search Engine (1)

A wannan rubutu da zan yi, zan raba shi kashi uku, kashi na farko bincike mai sauki, wanda ya ku san kowa shi yafi amfani da shi, sai dai kuma ana amfani da shi cikin kuskure, shine zamu yi dan gyara akai. Kashi na biyu kuwa zamu zurfafa binciken ne, ta wajen amfani da zurfafan hanyoyin yin bincike a shi google search engine, ta yadda yin amfani da wannan hanyar zai saukaka matuka da kuma fitar da sakamako mai inganci. Kashi na uku wanda kuma shine na karshe shi kuma zamu yi bayanin hanyoyin da ake bi a binciken hotuna, video da kuma wurare a dduniya baki daya. kamar yadda mafi yawa daga cikin mu suka sani, duk wanda yake da waya ko kuma yake da computer da yake son yayi bincike shine ya shiga google. wanda kuma bai san yadda zai yi ba to, zai rubuta www.google.com a wurin da ake rubuta adireshi shafukan internet wanda aka fi sani da Address Bar, da zarar ya rubuta zai bude mishi shafin farko.

Android – Tambayoyi 7 da mai amfani da Wayar Android ya kamata ya san amsarsu

Android wacce ake furta ta da hausa anduroyid manhaja (OS) ce da kamfanin Google Media Inc da ke kasar Amurka ya...