Zaka ji da zarar mutum ya san computer ko kuma ya iya sarrafata sosai sai kaji a na kiran shi da kalmar harcker. A gaskiya kalmar “hacker” tana da ma’anoni da dama da kuma fassara iri-iri, amma idan aka dawo akan harkar da ta shafi computer kuma kana son ka yi maganar hackers da computer to bai wuce ta basu ma’ana guda biyu ba wadanda su wadannan ma’anoni biyun duk kana bukatar saninsu. Kamar yadda aka fasara kalmar hacker a wani dictionary mai suna “Merriam-Webster” “Hacker kwararren masanin ilimin sarrafa computer (programmer). Shi kuwa wannan ma’ana da suka ba da ta kunshi kusan mutane da dama masu amfani da computer amma kuma wadanda ba a tunanin zasu iya cutar da wani.
Amma ma’ana ta biyu tafi ta da hankali matuka, domin Hacker shine mutumin da ya shiga cikin Kwamfutar mutum ta barauniyar hanya domin ya saci wasu mahimman bayanan shi ko kuma ya yi maka ta’adi”. Idan muka fuskanci wannan ma’ana ta biyu yana nuna mana cewar dukkanin wani abu da hacker yake kokarin yi shine ta’addanci tare da Kwamfutar mutane ta hanyar da kuma barna, domin hakan na faruwa ba tare da sanin mai amfani da Kwamfutar ba.