Kamfanin Sony ya samar da wayar salularsa wadda ruwa baya lalatawa.
Wayar samfurin Xperia Z na da wasu abubuwa da ba kowacce wayar salula ce ke da su ba.
An gabatar da wayar ne a wurin bikin baje kolin fasahar kere-kere na CES a birnin Las Vegas na Amurka wanda ake yi duk shekara.
Kamar kowacce shekara, abana ma manya da kananan kamfanonin kere-kere a duniya sun baje kayayyakin su.
Akwatunan talbijin da suka fi fito da hoto rangadadau su suka fi jan hankali a bikin baje kolin, inda wadanda suka kerasu ke baje sabon samfurin da suka samar.
Kamfanin Samsung dai ya fito da tasa talbijin din wadda ita ce ta fi sauran a duniya.
Sannan kamfanin samar da katunan wasa na nVidia ya kaddamar da wata na’urar wasa mara nauyi.
Na’urar na dauke da manhajar wayar salula mafi sauri a duniya.
Sai dai ana ganin kwamfiyutar hannu ta Razor Edge Pro, ce za ta yi gogayya da ita. Ita dai tana amfani ne da manhajar Windows 8, kuma wannan na’urar ta Joystick na bada damar yin wasa da ita.
Labari: Daga BBC Hausa