Tambaya
=================
Daga Bashir Abubakar Gada
Assalamu alaikum… Ina yiwa jagoran wannan shafin na “DUNIYAR COMPUTER” wato, Salisu Webmaster Allah ya ƙara basira ameen.
Ina da wata tambaya ce, Ina da yahoo imel amma sun yi blocking nasa nayi ƙoƙari insake dawowa da shi sai suce sai na sa security question tun lokacin da na buɗe imel for past five years.
A gaskiya duk ansar da nake tunanin ita ce na bada amma still sun ce ba dai dai bane.
Shi ne nake son in sani shin aƙwai hanyar da zan iya amfani da ita domin su yi retreaving ɗin aina nahin my security question and answer domin inbuɗe yahoo na.
Ko ko aƙwai wata hanya da zan iya bi in buɗe yahoo mail ɗina ba tare da na sa security ansar ba.
Nagode.
Daga
Bashir Abubakar Gada
Sokoto.
=======================
AMSA
=======================
Malam Bashir gaskiya waɗancan tambayoyin su ne kawai abin da zai iya tabbatar wa da Yahoo cewar wannan account ɗin naka ne, amma tun da ka manta dole haka zaka yi haƙuri da shi.
A yan zu aƙwai hanyoyi da dama da ake amfani da su wurin buɗe imel, ana yin amfani da recovery password wato zaka saka wani imel domin idan ka manta da password na imel ɗinka a tura shi zuwa wancan.
Misali abokinka na ƙud-da-ƙuk zai iya ba ka na shi imel din, sai ka saka a wurin recovery imel ɗinka.
Haka ma yanzu ana amfani da lambobin wayar hannu domin ita lambar da mutum yake da ita shi kaɗai ke amfani da irinta a duniya baki ɗaya, saboda haka idan ka zo buɗe sabon imel suna tambayar ka ka saka lambar wayarka hakan zai sa duk lokacin da ka manta da password zasu tambayeka hanyoyi guda uku.
Ko dai ka yi amfani da tambayoyin da ka amsa wurin buɗe imel, ko su aika maka da password cikin imel ɗin da ka ce a yi amfani da shi wurin password recorvery ko kuma su yi amfani da lambar wayar da ka buɗe imel da ita.
Da fatan wannan amsoshin da na baka sun gamsar.
Domin sanin yadda zaka buɗe imel da yahoo sai ka shiga ta wannan hanya
Domin sanin yadda zaka buɗe imel da gmail sai ka shiga wannan hanya http://duniyarcomputer.com/2018/05/09/yadda-ake-bude-gmail-account/