Ka ɗauka ruwa za ka yi amfani da shi sai wayar ta faɗa cikin ruwan, ka yi maza-maza ka ɗauko ta, a daidai lokacin da ka ɗauko ta ta riga ta jiƙe sharkaf da ruwa. Mataki na farko da za ka ɗauka shi ne sai ka cire batir ɗin ta sannan ka tabbatar ba ka kunnata ba domin idan ka kunnata a wannan lokacin lallai za ka yi damejinta.
Ita kuwa matsala ta faɗawar waya cikin ruwa wannan kusan ruwan dare ne wanda ke game da duniya, kusan wannan matsalar tana damun mutane da dama, sannan kuma kowa da irin matakin da yake ɗauka, kusan rabin mutane da wannan matsalan take shafar su ƙoƙari suke yi su bi hanyan da za su bi su iya tsane ita wayar tasu. Saura kuma ta ke kawai ta ke mutuwa, saboda wasu ganganci da suke yi bayan sun fito da ita wayar ta su a cikin ruwa. Saboda haka duk wanda wayar shi ta faɗa cikin ruwa ya yi hanzari ya tsamo ta nan take ya cire murfin wayar ya kuma zare batir ɗin ta, zai iya saka batirin a fili ko kuma wayar da batir ɗin a fili yadda rana za ta gasa su. Sanan kuma yana da kyau a lokacin da ya duɗe wayar ya cire batir ya sake dubawa ya gani shin ruwan ya riga ya shiga har cikin injin wayar ko kuwa bai shiga ba? To, idan har ka lura cewar ai ruwan ya shiga ciki za ka iya ɗaukarta ka riƙe gefenta ka riƙa yarfeta kamar yadda kake yarfar da kaya idan an wanke su, za ka ci gaba da yin haka har sai ka tabbatar cewar wayar babu sauran ruwa a cikin ta sannan ka sake mayar da ita cikin rana, ka kuma kifa bayanta a ƙasa, wato fuskarta yana kallon ƙasa bayanta na kallon sama saboda kada rana ta ɓata screen ɓin wayar.
To idan kuwa ka fuskanci cewa lallai wayar ta jiƙe sharkaf to abu na biyu shi ne ka sakata a cikin ɗanyar shinkafa? Shinkafa? Na san da yawa za su ji abin banbaraƙwai me ya kawo kuma shinkafa a maganar tsane waya? Wannan haka yake, lallai shinkafa za ta iya tsane maka dukkanin ruwan da wayarka ta ɗebo a cikinta.
Yadda za ka yi shi ne, za ka samu wani kwano mai girma wanda zai iya ɗaukar wayar ka saka ta da batirin ta a gefe sai ka cika wannan kwanon da ɗanyar shinkafar, ka sami murfi ka rufeta ruf, sai ka barta har tsawon awowi shida, daga nan sai ka ɗaukota ka mayar da batirinta, idan ka kunna ta zata tashi da yardar Allah. (Wannan an jarabta kuma ya yi aiki)
Haka kuma mutum zai iya amfani da abin hura gashi wanda mata ke amfani da shi idan suka jiƙa gashin kansu (Dryer) domin ya bushe. Amma shi ma idan za a yi amfani da shi dole a lura da wani irin dryer za a yi amfani da shi, domin a lokacin da ka fuskanci cewar lallai wayar ka ta jiƙe sosai har kana ganin cewa idan ka yi anfani da ɗanyar shinkafa ba zai tsane ruwan ciki ba, ka ga a nan kana buƙatar amfani da dryer. Da farko dai za ka cire batirin wayar sannan ka riƙe wayar a hannunka sosai sannan ka fara yarfad da ita kamar yadda ake yarfar da kaya da suka jiƙe, bayan ka gama yarfarwa ka tabbatar da babu sauran ruwa a jikin ta sai ka ciro ko kuma ka je shagon da ake yi wa mata gyaran gashi su baka karamin dryer sannan kuma ka yi amfani da mai sanyi ba mai zafi ba, domin idan ka yi amfani da mai zafi to za ka ƙarawa wayarka wata matsala ta daban, haka za ka ci gaba da busa mata iskar har sai ka tabbatar da wayar ta bushe sosai, sannan ka mayar da batirin sannan ka saka ta a caji bayan wani tsawon lokaci sai ka kunnata .
Shi ya sa yana da matuƙar kyau idan ka na da waya kuma tana da tsada ko kuma halin gyara to yana da kyau ka riƙa saka mata irin rigunan ruwa da kuma abubuwan da za su hanata lalacewa.
Wannan shi ne a taƙaice hanyoyin da za mu iya bi domin mu ga mun dawo da hayyacin wayarmu a lokacin da ta faɗa a cikin ruwa. A ƙarshe nake cewar a yi hattara!
Salam, Allah ya saka da alkhairi da wannan jawabi me ilmantarwa.
Tambaya ta anan shine a yanzu mafi yawa wayoyin da akeyi ba’a iya cire batir dinsu sai an kwance a wajen mai gyara, a irin wannan woyoyin akwai wata dabara da mutum zai iya yi ne cikin gaggawa?
Nagode
Abin da zaka yi shine ka yi sauri ka kashe ta ka ciccire kamar SIM da Memory sannnan sai a gabatar da sauran abubuwan da ke cikin wannan mukalar.
Jazakallahu bi Khairan Malam