28.4 C
Nigeria
Monday, April 28, 2025

YADDA AKE HADA 2GO DA FACEBOOK!

Sanin kowa ne, wannan tsarin yawancin mutane sun iyashi, amma kuma halin Dan Adam wato mantuwa shine muka ga ya dace mu ma Duniyar Computer muyi bayani akansa.

To da farko sai ka tabbata kana da account biyu wato 2go da facebook, sannan hakan zai yiwu,

 

1. Facebook account:

Yayin da ka bude facebook, bayan ya gama komai, sai ka bawa Facebook na ka Username wanda idan kasa a google dan ka nema zai baka sunan ka kai tsaye,

 

 FACEBOOK USERNAME:

  1. Username za ka rubuta shi ka dan.
  2. Ya kan kasance ma wata inkiyar kace wanda ake kiranka da ita,
  3. Ba’a bukatar space yayin kirkirarsa
  4. Yakan kasance suna zalla misali: AAADAM ko kuma da lamba Misali: AAADAM36, ko kuma da symbol wato .,?!@’-_(:;&) da sauransu misali aa.adam36, amma ba’a bukatar space.
  5. Baya bukatar zabi wato manyan baki ko kanana duk wanda kasa zai karba matukar wani bai riga ka sawaba.

To da wannan za ka yi amfani wajen hada 2go da facebook.

Idan ka bude facebook sai ka danna “profile” ko “Timeline” idan na ka yana da “profile” to sa ika danna “Info” wato kasa da sunanka suka da “photos” idan ya bude za ka ga wani rubuta a kasa da adadin friends naka cewar: “Profile name” to sunan da ke gabansa shine Username, idan kuma “Timeline” ne naka danna “edit profile” na gefen hotonka za ka ganshi a can kasa kadan, to shi zaka dauka.

 

 2go Account:

Ya yin da ka bude 2go na ka akwai wasu matakai guda 4 da zaka bi wajen seta Facebook da 2go.

 1. Setting

Da zarar ka bude 2go naka saika tafi karshe zaka ga setin saika danna shi.

 2. Gateways:

Bayan setin ya bude saika zabi gateways ka danna shi.

 3. Facebook Gateway:

Bayan Gateways ya bude saika zabi facebook gateway ka danna shi.

 4. Activate:

Bayan Facebook gateway ya bude saika zabi Activate ka danna shi yana bude zai ruboto maka wasu rubutu, saika danna “Continue” zasu umarce ka kasa facebook Username da facebook password, kana gama sawa saika danna “Summit” shikenan 2go da facebook naka sun hadu.

Misali: 2go<select select setting> sai <Gateways>select<facebook gateway>sai ka zabi<Activate> sannan ka latsa<Continue> sannan kasa facebook username da password.

2go & facebook password:

  • 2go password ya kansance lambobi mai dashi suna yana bada matsala.

Facebook password baya bukatar zabi suna ko lamba ko kuma duka biyun lamba da suna a hade.

11 COMMENTS

  1. Salam!

    Idan hada 2go da facebook yaki, to ku canza facebook password daga lamba zuwa suna

    misali idan facebook password naka 123456 ne to ka me dashi zuwa suna, misali.

  2. Salam,Ina da account da 2go kuma yanzu ina amfani da Nokia C5 amma duk sanda nayi kokarin budewa sai yaki ya bude sai ace wai untrusted supplier ne narasa ya zam bude 2go na

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img