Kasan cewar 2go ya kasance mai sauki wajen iyawa ga kowa, da saukin diban kudi wajen amfani, sannan kuma ya tanadi wasu abubuwa wanda kana kan 2go zaka iya magana da abokinka wanda yake twitter ko facebook, ta hanyar ganin alama cewa yana ‘Online’, zamu dauki yadda ake hada twitter da 2go.
Ka ziyarci www.gtalklife.com/signup.php. Dan yin rijista akan Gtalk,
Saika tabbata kana da Gmail account sannan 2go da twitter zai hadu, bi wannan matakan.
1. Ka ziyarci www.twitter.com, ka shiga account naka wato kasa Username naka da password ko email naka na twitter akan wurin da suka baka.
Bayan ka bude ka je kasan shafin twitter naka ko ka danna www.tweet.im, zai bude idan ka danna shi.
2. Yayin da ya bude saika danna “Authorise App” abinda zaka yi anan shine sai ka zabi Gmail sakamakon 2go yana dauke ne da Gtalk. Idan ka zabi Gmail to saika sa Email naka na gmail wurin sannan ka danna rijista “register”. Shi kenan saika fita daga twitter.
3. Saika bude 2go naka ka shiga “Setting bayan ya bude ka danna “Gateway” sai sake danna “Gtalk Gateway” saika danna “Activate” zasu nuna maka wasu rubutu saika danna “Continoue” sannan kasa Gtalk Username da Gtalk password, saika danna “Summit”
4. Jeka bangaren abokanka na 2go zaka ga “request” daga twitter da saika danna “Accept” ka kara aboki daga twitter.
Shi kenan kayi nasarar hada 2go da twitter yanzu zaka iya tura sako daga 2go zuwa twitter naka kai tsaye ga wanda kake so matukar yana jerin abokanka. Twitter IM service naka yana tsakanin Jabber ko Google@Gtalk.