32.4 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

Yadda ake saukar da video daga YouTube (1)

Wannan darasin sabo da tsawon shi mun raba shi gida biyu

Matashiya

Kafin mu yi bayanin hanyoyi da ake bi domin a saukar da bidiyo daga dandalin zumunta na YouTube, ya na da kyau mu fahimci wadansu ka’idoji da dokokin saukar da abu daga shi wannan zaure na YouTube.

Su dai wannan kamfani na YouTube mallakar babban ma’aikatar nan na Google ne, a hanlin da muke ciki a yanzu babu wani daki ko shafi a duniyan nan da ya ajiye hotuna masu motsi kamar YouTube, haka kuma shi ne shafi wanda aka fi ziyarta domin kallon hotuna masu mosti, kuma shi ne shafi na uku a ziyarta a duk shafukan da suke intanet.

Domin an ƙiyasta sama da mutane biliyan daya (1 billion) suke amfani da wannan shafi na YouTube haka kuma a shekarar 2014 kamfanin ya sami ribar kudi zunzurutun dalar Amurka biliyon 4 (4 Billion USD), haka kuma kamar yadda kamfanin dubawa da yin hasashe na DMR (Digital Marketing Statistics) su ka fadi cewar a kullum ana kallon bidiyo biliyan 4 a kowace rana.

A wuraren Satumbar 2011, kamfanin yayi wani alkawari da har yau bai cika ba, na cewar za su saki wata manhaja wacce zata ba mutane masu amfani da wayar komai da ruwanka damar kallon bidiyo a YouTube ba tare da amfani da fasahar intanet ba, matuƙar ka bude shi bidiyon kafin ka kashe intanet din. Wannan yunƙuri na su, har yanzu bai tabbata ba.

Amma kuma idan ka dubi mafi yawancin bidiyon da yake cikin kwamfutocin mutane da wayoyinsu za ka samu cewar ana samun su ne daga YouTube. To, haka abin yake, domin kusan kafin a fara samun makarantu masu zaman kansu a intanet, mutane da dama suna daura karatukansu a shafin YouTube domin jama’a su kalle su. Shi yasa YouTube ya zama wani dausayin alheri da kuma tsibiri na sharri. Domin kusan dukkanin wani ilimi da mutum yake son ya koya zai yi wahala a shiga cikin shafin YouTube bai same shi ba. Wani lokaci ma shi wannan shafin manyan gidajen jaridu da gidajen yada labarai na talabijin suna amfani da shi wurin daura shirye-shirye domin jama’a su yi amfani da shi ko kuma su sake kallonsa.

Shi yasa kowane irin bidiyo ake samun shi a YouTube, kama tun daga na karatu, wasanni, nishadi, fadakarwa da dai makamantansu, kuma dukkaninsu ana samun masu tsawo da matsakaita. A wani lokaci zaka samu mutum daya ya daura bidiyo sama da dubu biyu a shafinsa, kuma ka samu yana da mabiya ko masu kallo sama da miliyoyin adadi.

Takaitaccen tarihin kafa YouTube

YouTube na daya daga cikin shafu a Intanet irin wadanda ake kiran su da video-sharing website, wato shafukan da ake saka bidiyo domin wadansu su kalla, ya na da Hedkwata a San Bruno da Jihar California ta kasar Amurka. Wadansu matasa su uku Steve Chen, Chad Hurley da kuma Jawed Karim su ne suka kiriro shafin a 14 ga watan Fabrairu 2005 bayan da suka bar aiki a wani kamfanin hada-hadar kudi a intanet mai suna PayPal. Tun daga shekarar 2005 zuwa 2006 su ne suke da alhakin mallakar komai a shafin YouTube har zuwa lokacin da kamfanin Google ya ga muhimmancin wannan shafi da yadda ya sami karbuwa a wurin mutane, ya siye shi da kudi wuri na gugar wuri har dalar Amurka Bilyan 1 da Miliyan 650 ($1.65 billion) a watan Satumba 2006.

 Chad Hurley, Steve Chen, sai Jawed Karim
Daga dama: Chad Hurley, Steve Chen, sai Jawed Karim

Shafin wanda yake ba mutane damar su daura bidiyo domin mutane su kalla ko domin su yada shi a shafukan intanet ko kuma lika shi a shafukan zumunta. Ana amfani da zarin abin kallo na kwamfuta da wayoyin domin iya kallon su, kamar tsarin WebM da H.264 da MPEG-4 da AVC da kuma Adobe Flash Player.

Ana samu bidiyo daban-daban kamar na wasanni, shirye-shiryen gidajen yada labarai, bidiyon wakoki, fina-finai, karatuka, bidiyo domin ilmantar da dai makamantansu.

Mafi yawancin bidiyon da suke YouTube gama garin mutane ne suka daura shi, amma kuma ana samun gidanjen yada labarai manya sanannu suna amfani da shi, kamar irin su CBS, BBC da VOA da dai makamantansu.

Wanda bai yi rigista da YouTube ba zai iya kallo ne kawai, amma wanda yayi rijista zai iya kallo, zai iya daura shima na shi bidiyon domin wadansu su kalla, zai iya kulla alaka da wani mai daki a YouTube duk lokacin da ya daura wani sabon bidiyo a sanar da shi kai tsaye (Subcribe), sannan zai iya yin tsokaci (comment) ga bidiyon da aka bayar da damar yin tsokaci a kai.

Dukkan bidiyon da yake YouTube babu matsala wurin kallonsa matukar bai dauki hotuna na tsaraici ko na wanda yake dauke da hotuna masu hatsari, kamar kisa ko kuma abin da bai kamata masu karamin kwakwalsu kalla ba. To irin wadannan bidiyo dole sai ka fadawa YouTube cewar kai ka wuce shekaru 18 kafin ka ga irin wadannan bidiyoyin.

Shafin na YouTube yana samun kudaden shigar shi ta hanyar saka talla da yake yi a kan bidiyo da mutane su kallo, kuma sun ba masu bidiyon damar mallakar kashi 55% na kudin da ake biyansu. Misali a shekarar 2013 kamfanonin da suke ba YouTube talla su na biyan su dalar Amurka $6.60, idan aka kalli bidiyo ko kuma tallansu har sau 1000, wanda yake nuna cewar duk wanda ya amince da YouTube su saka talla a kan bidiyon da ya daura a shafinsu zai iya samun 0.5x$7.60×55%=N2.09 wannan tsarin an yi amfani da shi a shekarar 2013.

Shafin na YouTube yana iya kokarin ya ga ya hana mutane daura bidiyon da baka da hakkin mallaka, wato irin na satan safage wanda kusan da yawa daga cikin bidiyoyin da suke YouTube wadanda suka daura shi ba su suke da hakkin mallakar shi ba.

Shin daidai ne mutum ya saukar da Video a YouTube?

Babu laifi idan mutum ya saukar da bidiyo daga YouTube domin yayi amfani don karan-kansa ba tare da juyashi ba ko kuma ya canza shi zuwa wata hanya. Amma laifi shi mutum ya saukar da kowane irin bidiyo a YouTube sannan ya yi amfani da shi a wani gidan talabijin ko kuma ya gurza shi ko kuma domin sayarwa.

Kamar yadda kamfanin na google ya fadi a shafin shi na sharadin amfani da bidiyon YouTube sun rubuta kamar haka, “Ba a yarda kayi amfani da Video nan ba sai domin amfanin kanka, ba na neman kudi bane, ba za a diba ba (copy), ba sake gurzashi, ba rabashi, ba nuna shi a gidajen talabijin, ba yin kasuwanci da shi, kada ayi amfani da wani bangare nashi sai da izini rubutacce zuwa ga YouTube”. Daga jin irin wannan sharadi yake nuna mana cewar idan mutum zai saukar da bidiyo daga YouTube kuma yana son yayi amfani domin nishadantar da kansa ko kuma ilmantan da kansa, to babu laifi.

Haka idan muka dubi zuwa ga amfani da shi ta wadansu kafafe, sai muga hatta yadda mutanen mu suke saukar da bidiyo daga wannan gida kuma suyi ta gurzashi, wannan kai tsaye laifi ne. Shi ya sanya daga cikin dokokin amfani da shi, sun fadi cewar idan mutum ba zai yi amfani da intanet ba ne, ya kalla kai tsaye, to shima ba su yarda ya saukar da shi ba domin kallo.

Saukar da bidiyo daga YouTube yana kawo wa wannan kamfani cikas ga harkokin kasuwancin su. Mutane da dama su na yawan tambayar mu shin, irin waɗannan shafuka kamar google, ko facebook, ko YouTube mene ne ribarsu? Sai mu fada musu cewar shigar da muke yi suna amfani da shafukan su, shi ne ribar su, domin manyan kamfanoni na duniya suna yin la’akari da yawan mutanen da suke shiga dakuna a intanet, kuma wannan dalilin yake sanyawa a basu talla.

Mene ne dalilin da yasa ba maballin saukar da bidiyo kai tsaye a shafin YouTube?

Kamar yadda muka fadi cewar a shekarar 2014 kamfanin google ya sami ribar dalar Amurka biliyan 4 wanda yake daidai da Naira Biliyan Dari Tara (900,000,000,000) ta su bidiyoyin da ake kallo a shafin YouTube. Wannan ribar ta samu ne saboda talla da yake bayyana a jikin bidiyo lokacin da mutum yake kallo.

Wannan shi ne ma dalilin da ya sanya wani lokaci idan mutum yana son kallo a YouTube sai ya jira na ‘yan dakikoki biya domin kallon talla kafin ya baka zaɓin ko ka ci gaba da kallo ko kuma ka wuce zuwa ga shi bidiyon da ka nemi ka kalle shi. Matsalar nan ita ce, idan mutane suka sauke shi bidiyon kun ga babu yadda za ayi kamfanin su sami kudi, dalilin haka ya sanya su kamfanin basa so mutum ya ce zai saukar da shi.

Ko ba mu yi dogon bayani ba, kasan cewar da dukkanin bidiyoyin da suke cikin wayoyinmu za a barsu a shafukan da suke sai dai kawai mukalla a sama da kudaden da za su samu sai ya ninka wanda suka samu a shekarar 2014. Amma dai duk da haka mutane da yawa suna ta ƙoƙarin su ga yadda za ayi su saukar da wadannan bidiyoyi a kwamfutocinsu da wayoyin domin su iya amfana da su a wani lokaci.

Mene ne ya sa bidiyo yake da cin MB?

Dalili kuwa shi ne domin bidiyo hotuna ne aka tara su a wuri guda. Yadda abin ya ke shi ne, duk wani bidiyo da mutum ya gani tun daga dakika daya zuwa awanni daga hoto daya ne zuwa hotuna 25 zuwa hotuna 60. Idan ka duba na’urar daukan hoto misali Camera ta wayarka, zaka ga daga bayan an rubuta lamba a gaban lambar an rubata Pixel, misali 2 Mega Pixel. Wannan megapixel sinadari ne da ake auna kyau da girman da Kamara zata iya daukar hoto da shi.

Idan aka ce kamarar wayar ka ta na da 5-megapixel to ana son ka sani cewar wayar ka zata iya daukan hoto guda wanda sai an sami digo miliyan biyar a jikinshi. Shi daman Pixel a ilimin daukan hoto na nufin digo duga ko kuma rami guda da kala zai iya zama na hoto a cikinsa. Saboda haka, idan aka ce wayar mutum ko kuma kamarar shi tana daukar hoto mara motsi guda daya wanda ya kai nauyin 2Mb, to idan zata dauki bidiyon dakika guda sai ka hada 2mb x 25 = 120mb.

A takaice duk mafi yawan bidiyon da muke kallo suna da zubu iri biyu ne, PAL da NTSC, bidiyon da aka daukeshi da fasahar PAL a kwane dakika ana samun hotuna 25 ne, wanda kuma aka yi amfani da fasahar NTSC ana samun hotuna 29 zuwa 30 a kowane dakika guda. Ba a maganar cewar lokacin da kamarar take daukan hotunan tana kuna hadawa tare da sauti wanda shima yana da nasa nauyi.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya bidiyo ya ke nauyi kasancewar tarin hotuna ne da sauti a hade a wuri guda.

KARANTA DARASI NA GABA

17 COMMENTS

  1. Hakika wannan bayani abin farin ciki ne kuma kun karamana ilimo sosai Allah yasaka da alhairi. Sai dai munaso asamo wata hanya ta yadda zaasamu sauqin cin kudi ko Data domin saukakema masu karamin karfi. Thanks Sunusi Hashim Alameen

  2. Gaskiya na samu fa’idantuwa mai yawa akan shafin youtube amma ina da tambaya akansa me yasa you yake playing da MB data amma ba yayi da Subscribing kamar na Blackberry?

  3. Allah ya saka da alkhairi gaskiya nima na fa’idantu sosai

    amma don Allah ina da waya nokia E5 baya budan youtube ta application dinsa dole sai dai ta browser ko opera ko kuma ucweb a takaice dai dole sai ta stream video don Allah ya za’a na gyara wannan matsalan ?

  4. Kuna rubutawa muna karantawa kuma muna karuwa ✔
    Allah ya biyaku da mafificiyar Alkhairi kai harma da
    Mu baki daya,,✔
    Muna godiya domin muna karuwa sosai★100%

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img