38.1 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

YADDA AKE DAWO DA LAFIYAR NOKIA E66 CIKIN RUWAN SANYI

Rubutawa: Adamu Abdullahi AAADAM36

Wannan ɗan bayani zai taimaka wajen waɗanda suke tambaya a kan yaya za su iya dawo da lafiyar wayar su ta Nokia a lokacin da ta samu matsala kamar yadda ɗaya daga cikin ɗaliban wannan dandalin mai albarka ya yi kamar haka: Webmaster, da fatan kana lafiya.

Dan Allah wayata ce na manta security code ɗinta, Nokia ce ƙirar E66 to ina buƙatar yi mata formating amma abin ya ki yiwuwa.

Shi nake so ko akwai wani taimako da zan samu daga gare ka, in na ɗauko applications ba sa installation kuma wasu apps ɗin ma basa remove kwata-kwata.

Ka huta lafiya. http://www.facebook.com/abdullah.nuhu

1. Gyara mai sauƙi (Soft Reset)

Wannan hanya ta share dukkan wani abu da aka saka wa ita wayar a cikin fallanta na .ini amma kuma baya goge abubuwan da ka saka a cikin ita wayar kamar su hotuna ko bidiyo ko rubuce-rubucenka ko kuma wani application da ka saka mata, zai yi ƙoƙarin ya dawo da ita zuga ga lafiyarta. Za ka rubuta *# 7780 # .

2. Kankare ta gaba ɗayanta (Hard Reset).

Shi kuwa nan kankare ita wayar ta ko ma babu komai a cikin ta, domin yana share dukkanin abubuwan da aka taɗa saka mata ta dawo kamar yadda aka sayota daga kamfani, amma yana da kyau wanda yake son ya gabatar da wannan tsari ya tabbatar da cewar batirin wayar a cike yake, ko kuma yana haɗe da wuta, sannan ya tabbatar da ya kwashe dukkan abubuwa masu amfani a cikin wayarshi kamar hotuna da makamantansu. Bayan ya gama sai ya rubuta wannan a wayar ta shi. *#37370#

Wannan shi ne a taƙaice bayani a kan yadda za ka yi resetting na wayar Nokia E66.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img