Shin kana da kani ko aboki da ke amfani da kwamfutarka ka kuma yake bata ma abubuwan da ka ajiye ko kuma ba ka son ya ga wasu surrukan da ka ajiye? to idan ka biyo mu za muyi maka maganin matsalarka.
Za ka iya maganin wannan matsalar ta hanyar User Account, shi dai user account na bada dama ga mutane sama da ɗaya su yi amfani da Kwamfuta ɗaya inda da account da password nasa.
Shi dai User Account ɗin ya kasu kashi uku.
1 Administrator Account: wannan Account shi ke bada damar yin duk wani canji tare da saka wani abu da kuma cire shi ko da kuwa zai shafi tsaron Kwamfuta ko sauran masu amfani da ita wato users.
2 Standard Account: Wannan account ana amfani da shi wajen al’amuran yau da kullum amma bai da damar canjin da zai shafi tsaron Kwamfuta ko kuma user account.
3 Guest Account: Shi kuma wannan account ana amfani da shi domin waɗanda ke amfani da Kwamfuta na ɗan wani lokaci.
Za ka iya buɗe user account ta wannan hanyar
- Da farko za ka ɗora mouse ɗinka a kan ‘start’ sai ka latsa
- Duba dama za ka ga ‘control panel’ sai ka latsa kan cotrol panel
Zai budema za ka ga User Account and Family Safety
- idan ka latsa zai buɗe ma wani waje da za ka ga user account a ka sansa za ka ga
‘change your account picture’ da ‘change your window password’
- inda za ka iya canza password daga dama kuma za ka ga ‘add’ or remove ‘user account’
- inda daga nan ne za ka iya bode ko kuma ka goge user account ɗin,
- idan ka latsa kan add or remove user accounts zai buɗe maka user accounts ɗin da ke kan Kwamfuta daga ka sa kuma za ka ga create a new account,
- idan ka latsa zai kaika idan za ka saka suna user account ɗin da za ka buɗe da kuma damar da za ka ba shi misali ka sa masa suna Gajida ka ba shi damar Administrator ko Standard san nan ka duba ka sa daga dama za ka ga create account,
- sai ka danna shi ke nan ka buɗe account.
Daga nan zai nuna maka user account ɗin da ke kan Kwamfuta sai kan danna kan sunan account idan zai buɗe maka wani waje daga sama an saka make changes to Gajida account idan Gajida shine sunan account, daga kasa an saka ‘change the account name’ inda za ka iya canza sunan account create password da dai sauransu.
idan ka latsa create password inda zai buɗe maka inda za ka saka lambar sirri wato password za ka ga new password inda za ka saka lambar sirri da kuma ‘confirm new password sai da kara saka password
inda aƙalla ka saka baki shida ko baki da lamba guda shida kuma idan da babban baki ka saka
- idan ka zo kunna Kwamfuta, to ka saka da babban baki.
- Za ka kuma iya goge user accout daga wajen da ka saka password idan ka duba ka sa za ka ga Delete the account idan ka danna zai kaika wajen da za ka ga an rubuta ‘Do you want to keep Gajida file’,
- idan kaso ka ajiye sai ka duba ka sa za ka ga ‘keep files’ sai ka danna idan kuma baka son ajiye file ɗin sai ka danna Delete files sannan ka danna Delete Account shi ke nan ka goge account ɗin. Idan hali ya yi za mu ci gaba.
Daga Balarabe Yusif Babale Gajida 08036318846