Shin kana da kane ko aboki dake amfani da computar ka kuma yake batama abubuwan da ka ajiye ko kuma baka son yaga wasu surrukan da ka ajiye to idan ka biyomu zami maka maganin matsalarka.
Zaka iya maganin wan nan matsalar ta hanyar User Account, shi dai user account na bada damar ga mutane sama da ɗaya suyi amfani da computer daya inda ko ke da account da password nasa.
Shi dai User Account din ya kasu kashi uku.
- Administrator Account wan nan Account shi ke bada damar yin duk wani chanji tare da saka wani abu da kuma cire shi koda kuwa zai shafi tsaron computer ko sauran masu amfani da ita wato users.
- 2 Standard Account wan nan account ana amfani dashi wajen al’amuran yau da kullum amma bai da damar canjin da zai shafi tsaron computer ko kuma user account.
- Guest Accoun shi
kuma wan nan account ana amfani da shi domin wadan da ke amfani da computer na dan wani lokaci.
Zaka iya bude user account ta wan nan hanyar da farko zaka dora mouse dinka a kan star sai ka latsa daga abin da zata bude maka idan ka duba dama zaka ga control panel sai ka latsa kan cotrol panel daga abin da zai budema zaka ga User Account and Family Safety idan ka latsa zai budema wani waje da za ka ga user account a kasan sa zaka ga change your account picture da change your window password inda zaka iya canza password daga dama kuma zaka ga add or remove user account inda daga nan ne zaka iya bode ko kuma ka goge user account din, idan ka latsa kan add or remove user accounts zai bude maka user accounts din dake kan computer daga kasa kuma zaka ga create a new account, idan ka latsa zai kaika idan zaka saka suna user account din da zaka bude da kuma damar da zaka bashi misali kasa masa suna Gajida ka bashi damar Administrator ko
Standard san nan ka dubu kasa daga dama zaka ga create account sai ka danna shi ke nan ka bude account. Daga nan zai nuna maka user account din dake kan computer sai kan danna kan sunan account idan zai bude maka wani waje daga sama an saka make changes to Gajida account idan Gajida shine sunan account, daga kasa an saka change the account name inda zaka iya canza sunan account create password da dai sauransu, idan ka latsa create password inda zai bude maka inda zaka saka lambar sirri wato password zaka ga new password inda zaka saka lambar sirri da kuma confirm new password sai da kara saka password inda akalla ka saka baki shida ko baki da lamba guda shida kuma idan da babban baki ka saka idan kazo kunna computer to ka saka da babban baki. Zaka kuma iya goge user accout daga wajen da ka saka password idan ka duba kasa zaka ga Delete the account idan ka dan na zai kaika wajen da zaka ga an rubuta Do you want to keep Gajida file idan kaso ka ajiye sai ka duba kasa zaka ga keep files sai ka dan na idan kuma baka son ajiye file din sai ka dan na Delete files san nan ka dan na Delete Account shike nan ka goge account din. Idan hali yayi zamu ci gaba.
Daga Balarabe Yusif Babale Gajida 08036318846