Assalamu Alaikum, ina wa salisu webmaster barka da shan ruwa, da saura mutanen wannan dandali mai Albarka, ya mai girma duniyar computer ina tambaya akan yanda ake bude PAYPAL Account? da kuma yanda ake amfani da shi.
Duniyar Computer Da fatan kun sha ruwa lafiya, kuma zaku yi hakurin jinkirin rashin amsawa da ba ayi da wuri ba. Wato shi PAYPAL Account a takaice kamar mutum ne yaje banki yace yana son ya bude account to haka bude account a paypal yake. Wasu mutane ne a kasar Amurka suka kirkiri wannan hanya da zaka iya ajiyar kudi domin siye da siyarwa a Internet. Wato shi paypal banki ne amma wanda yake iya baka dama ka ajiye kudi koda nawa ne domin idan kaga wani abu a wani website da ake siyarwa ka shiya. Kuma saboda yadda sata tayi yawa a internet suna da kwararrun ma’aikata wanda zasu tsare maka dukiyar ka ba tare da wani ya taba maka ba, domin ana danganta Paypal accout da shine mafi tsaro a bankunan internet. Sai kash!!!! wani hanzari ba gudu ba basa yarda ‘yan Najeriya su bude account da su a sanadiyyar munanan dabi’u da abokanan zaman mu suke yi na cuta da cutarwa irin wadanda suke kiran kansu yahoo boys da kuma hackers da fatan kun gamsu
Comment: wanted