29.8 C
Nigeria
Thursday, April 24, 2025

ZUWA GA GWAMNA MASARI Daga Prof Ibrahim Malumfashi

Na bi wannan mataki ne domin na bayyana abubuwan da ke makure a cikin zuciyata game da dan bar da aka dora na gudanar da mulki a Jihar Katsina. Na kuma soma kokawa ne tun kafin tafiyar ta yi nisa saboda a sa wa tayoyin motar tafiya iska a kuma tabbata an sa wa notocin motar giris, don jin dadin tafiya.

Mai girma Gwamna, wadannan batutuwa da zan zazzage a nan, su ne muka zazzagawa wa tsohon Gwamna Shema lokacin yana kan mulki, amma canjin da muke tsammani bai samu ba har ka hau karaga. Abin da kawai zan yi a nan shi ne cire duk inda sunan Gwamna Sheme ya fito in maye shi da naka, domin mu ga ko canjin da aka yi mana alkawari zai samu kamar yadda yawancin mu ke buƙata.

Ya mai girma Gwamna, ranar litinin, wato 28 ga watan Mayu 2012, na yi bikin cika shekara daya na samun ganawa da Gwamna Ibrahim Shehu Shema na jihar Katsina ta fuskar yin irin wannan rubutu, ganawa irin wadda ka yi da dattawa da kuma wasu daga cikin masu fada a ji a jihar Katsina ranar Asabar 12 ga watan Satumba, 2015. Ita wancan ganawa da Gwamna Shema, tamkar irin taka ganawar ce, ita ma Gwamna Shema ya nemi ganawa ne da duk wasu masana da suka samu kai koluluwar karatunsu na zamani, wato masu digirin digirgir da kuma Farfesoshi, ‘yan jihar Katsina. An yi wannan ganawa ce a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina bayan laccar da aka gabatar domin bikin hawan Gwamna Shema bisa karagar mulkin jihar a karo na biyu. Ita kan ta laccar da Mai Shari’a Umaru Abdullahi ya gabatar, abin tunawa ce, abin tinkaho ce, domin kuwa ta nuna cewa Gwamna Shema zai iya tattara mutane domin su ba shi shawara, ya kuma saurari mai dadi ko masar dadi. Wannan shi ne kila ya sa mani kwarin gwiwar da ta sa na amince in halarci taron ganawar da Gwamnan a kebance ba tare da hayaniyar sauran jama’a ko ‘yan jarida ba.

Amma duk wadannan abubuwa ba su ne makasudin yin wannan sharhi ba a yau. Niyyata a yau ita ce na ƙwance jakar da nake dauke da ita tun samun waccan damar ganawar da muka yi da Gwamna Shema, a shekarar 2011. Jaka ce da ke dauke da batutuwa da nake ganin za su yi mana jagora wajen kara fahimtar yadda gwamnati ke gudana da yadda sauran mutane da ke kusa da gwamnatin ke mu’amula da ita da ma kuma yadda wadanda ke nesa da ita ke mata kallon kitsen rogo da kuma uwa-uba yadda shi talakan ke faman kasancewa talaka duk da cewa wai shi ake wa mulki ko kuma in ce shi ake mulka.

Abin da ya burge ni a lokacin waccan ganawa da Gwamna Shema shi ne yadda Gwamna ya gayyaci masanan jihar Katsinar, aka kuma zauna, zama irin na gurguzun al’umma, ba Sarki balle Talaka domin a fahimci juna, a kuma ba juna shawara kan yaya za a ciyar da jihar Katsina gaba. Gwamna Shema ya gaya wa Daktoci da Farfesoshin jihar Katsina cewa, ya tara su ne domin a gaya masa inda ya yi kuskure a baya domin ya gyara, a kuma bayyana masa inda ake neman a mayar da hankali a gaba, domin a nazarta, a kuma kokarta jan akalar aiki zuwa can.

Shawarwarin da aka bayar ba za su kasaftu a nan ba, amma duk da haka Gwamna Shema ya saurari duk wanda ya ba da gudunmuwar yadda yake ko take son a tunkari lamurra.

Wasu gudunmuwar tasu ta gina kasa ce, wasu kuma domin gina kai da kai ne. Amsoshin da Gwamna Shema ya bayar da alkawurran da ya yi su ma abin dubawa ne, ba kuma inda ya fi birge ni irin shan alwashin da ya yi na tabbatar da zai yi aiki da shawarwarin da aka ba shi.

Ba zan iya kawo dukkan shawarwarin da aka ba shi ba, da kuma yadda ya yi alkawarin shawo kan matsalolin ba, amma zan mayar da hankali kan shawarwarin da ni da irina muka bayar da kuma irin alkawarin da Gwamna Shema ya yi game da su, domin a gane yadda ake tufka da warwara a fagen mulki, kila ta haka a tsinci dame a kala a lokacin gudanar da naka mulki yanzu.

Abu na farko shi ne alakar da ke tsakanin Shugabanni da Talakawa da kuma fafutikar zaman lafiya. Ni a nawa ganin kamar yadda na bayyana, ba yadda za a yi a samar da ingantaccen zaman lafiya sai in shugabanni da mabiya sun canza hali game da sha’anin mulki. Ba wani abu ya jawo matsalar da ake cin karo da ita a halin yanzu ba, sai lalacewa da tabarbarewar sha’anin mulki. Hanyar da nake ganin za a samar da zaman lafiya shi ne masu mulki su kusanci talakawa, su bar warewa can gefe suna kyamar wadanda suka zabe su. Idan suka yi haka, suka kuma inganta mulki da yin aikin kwarai, aka kuma samu wasu daga cikin al’umma da ke nuna wa shugabanni inda suka kauce, ba da son rai ko neman abin duniya ba, to za a samu zaman lafiya a tsakanin al’umma. Dole ne idan ana neman zaman lafiya da raya kasa a samu masu kururuwa game da cin hanci da almundahana da lalacewar lamurran mulki a kowane fanni na rayuwa.

Jihar Katsina, jiharmu ce mu duka, lalacewar ta da ci gaban ta, namu ne mu duka. Lokaci ya yi da za mu mayar da hankali kan warware mata matsalolinta da sake lalubo matakan da suka dace domin tayar da komadar ci gaban nata. Yanzu ba lokacin da shugabanni za su tsaya wasa da hankalin talakawa ba ne. Kan mage ya waye! Canji ya samu.

Kenan dole ne a nemar wa jihar Katsina hakkinta. Dole ne mutanen Jihar Katsina (kowa da kowa) su mike domin inganta da ciyar da jihar Katsina gaba. A dage domin yi wa al’umma aiki, a kuma tabbata an zauna don yin daunin da ya dace da kowane yanki na Jihar Katsina. A tabbata ana bin diddigin yadda ake sarrafa dukiyar mutane. A sami wasu daga cikin al’ummar jihar ta Katsina, kamar yadda na fada a baya da za su dinga nuni da inda ake barna domin a gyara.

Ya Mai Girma, abin da muke fada a kullum shi ne mu tsaya tsayin daka mu fahimci yadda mulki ya kamata ya gudana. Kowa na da irin gudunmuwar da zai iya bayar wa, tun daga Gwamna har zuwa talakawa. Mu zauna domin tsara yadda mulki zai gudana, domin taimakon kai da kai.

Saboda haka ya Gwamna, ina ya ga ya dace a samar da wani tsari a jihar tamu da za a yi amfani da shi domin a tabbata aiki na gudana yadda ake so. Halin da ake ciki na ruruta da bayyana rashin katabus da aka tafka a baya, musamman a zamanin Gwamnatin Shema ya isa haka nan. An dai yi kokawa, kuma ya Mai Girma, ai ka yi kaye, lokaci ya yi da za a motsa zuwa gaba. Matsalarmu a yau ba ta tsohon Gwamna Shema ba ce, ta inda za mu dosa ne daga inda ya tsaya. Me za mu yi? Yaya za mu yi? Muna da kudaden da za su taimaka mana wajen ganin mun yi abin da ya dace? Kudaden shiga sun ishe mu? Idan ba su isa ba, ina za mu kwakwulo wasu don raya jihar ta Katsina? Wadannan tambayoyi da wasu irin su, ina jin su ne ya kamata mu mayar da hankali kai. Ta tsohon Gwamna Shema ta kare, yanzu ta Gwamna Masari ake yi! Me aka shirya wa al’ummar jihar Katsina?

Nan ne zan fara da jefo tawa gudunmuwar. Ya Mai Girma, daga bayanan da kake ta kururutawa game da abin da aka yi a baya a wancan Gwamnati ta Shema sai mutum ya dauka cewa ba aikin ci gaba ko daya da Gwamnatin Shema ta yi a jihar Katsina, sai facaka da almundahana, wanda na san ba haka kake nufi ba, tun da lokacin kamfen ya wuce, an kuma zabe ka.

Wani abu da na gani shi ne tamkar kwasan karar mahaukaciya ake neman yi wa matsalolin jihar Katsina, alhali ina ga dauki daidai zai fi alfanu. Ya Mai Girma, a maimakon a ce sai an taba kowane fanni na rayuwar al’umma da ya dagule, me zai hana a dubi matsala guda a hau kanta a dinga dirza har sai ta yi laushi, sa’annan a koma kan wata. Me ya sa gwamnati za ta fi mayar da hankali wajen shan kandamau, inda abin da ake buƙata shi ne sha ludayi-ludayi? Al’amurran ilimi na cikin tasku! Hanyoyinmu sun bulbulguce! Ingantaccen ruwan sha ya fara gagarar mu! Talauci ya yi wa yawancin mu katutu! Sata da almundahana a kowane fanni na rayuwa sun kusa zama ruwan dare! Ayyukan noma sai kokawa suke yi! Kiwon lafiya shi kan sa ba shi da lafiyar! Siyasa da mulki da zamantakewa na kewar masu kulawa! Duk ga su nan birjik!Bisa irin wannan fasali, shin ana ga kandamau zai biya? Ko alama!

Dangane da haka nake ganin ya dace a ce cikin wata uku da dori da aka yi an san inda aka nufa. Jama’ar jihar Katsina su san cewa aƙwai gwamnatin Aminu Bello Masari, ba gwamnati mai yekuwar gwamnatin Ibrahim Shehu Shema ta gaza ba. Ba wai nufina ba ne na ce ba wani abu sabo da gwamnatinka ta yi wa al’ummar jihar Katsina tun hawanta karaga ba ko alama, amma dabashirin ciyar da jihar Katsina gaba ne ban gani ko na ji ba a cikin tsawon lokacin da aka hau karagar mulki.

Ba wani abu ya sa na fadi haka ba sai ganin cewa tsari da tabbatuwar tsari da kuma hangen nesa da ingantaccen dabashiri wajen aiwatarwa su ne ke jan ragamar cigaba. Ke nan abin da ake buƙata a jihar Katsina a halin yanzu shi ne a san inda aka sa gaba domin yin aiki gadan-gadan, a kuma lura da bin tafarkin da yake shi ne zai fitar da A’i daga rogo. Me ya kamata a yi a wannan fasali?

Dole ne a bayyana wa mutane halin da ake ciki da kuma abin da aka shirya za a yi. Abin jin dadi shi ne ya Mai Girma, an somo da haka. An bayyana halin da jiya ta kasance, saura yau da kuma gobe. Wato dai ga cuta, saura magani.

Abin da ka bayyana a wajen taron da ka yi da masana da dattawan jihar Katsina bayan ƙwana 100 da hawanka mulki abin da aka saba ji ne kullum daga kowace irin gwamnati da aka yi a baya. Kowace shekara ai batun ke nan, za a inganta harkokin ilmi. Za a biya wa dalibai kudaden makaranta. Za a gina azuzuwan makarantu. Za a samar da takin zamani. Za a gina hanyoyi a birane da karkara. Za a kawar da talauci. Za a samar da ruwan sha. Za a samar da motocin shiga don inganta sufuri. Za a samar da aikin yi, za a….! Ba iyaka.

Amma kullum tambayar da al’umma ke yi shekara bayan shekara ita ce shin an samar da wadannan abubuwa ko dai kawai ana babarodo ne? Shi ya sa yake da kyau a fahimci lamurra da kyau kafin a dora dan ba. Dole ne idan ana son aikin gaskiya, a bayyana wa mutane abin da za a yi da yadda za a yi, da inda za a samar da kudaden yin abubuwan, a lokaci guda, a kuma gani a kasa a lokacin gudanarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Zafafan Sati

Makaloli

Masu alaka

Shahararrun Rukunai

spot_img